106

581 55 0
                                    

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

*By Maryam S Indabawa*
*MANS*

Page 106

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Aunty Rash*




Khaleel ne yake tsokanar Najib! Cewa yau fa sai ya samo masa budurwa

Dariya Najib yayi kawai dan yasan Khaleel tinda ya daura niyyar samo masa dan fitar dashi daga damuwar da yake se ya samo masa.

"Kayi shiru?"

Najib ya kalle shi. Ya ce,
"Me kake son nace,"

Khaleel ya kalle shi, ya ce,
"Kana son kace ka aminci "

"To ya zanyi ai dole na amince dan nasan halin ka."
Hannun sa ya dauke daga kan motar ya tafa su.

Ya ce,
"Ina son ka dan uwana."

Murmushi Najib yayi, ya ce,
"Wannan a jinin mu yake "

Khaleel ya dage gira ta ce,
"Tabbas."

Dai dai lokacin suka isa wajen. Ya fito sun tafiyi a tare, suka nufi hall din.

Hall din ya cika da hadaddun yan mata da samari. Amman shigar su Najib sai kallo ya koma sama. Dan daga mazan har matan duk sai da suka yaba da Najib.

Duk da shi ba fari bane, amman kyakywa ne, kasancewar sa bafulatanu. Haka maka Khaleel kyakyawa ne, amman shi fari ne.

Tafiya yake cikin iska da takama, har suka isa inda aka tanadar musu.

Yan mata da yawa ya dauke hankalin su, a ciki harda Summy wacce tsabar girman kanta duk yadda taji ana maganar gayen bata dago ta kalle shi, sai danna watar ta da ta cigaba dayi.

Suna Zama, Khaleel ya fara zuba ido dan ganin, ta inda ze samowa abokin nasa matar aure.

Cikin kalle kallen sa, idon sa ya fada kan Summy dake can gefe, tana ta basarwa, ga maza se zuwa suke amman ko kallo basu ishe ta ba.

Wanna yasa yaji yarinyar ta kwanta masa. MC ne ya fara jawabi cewa manyan abokan ango sun zo, dan haka ana musu barka da zuwa

Sannan yana son ganin ango da amarya a fili. Kai Najib ya dago yana kallon abokin sa Bashir.

Yayi kyau murmushi ya aika masa dashi. Sanna suka fito tsakiyar fili.

Anan ne MC yace, wannan fili na Manyan Aboka nan ango ne, Khaleel da dan uwan sa Najib.

Murmushi Khaleel tayi, ya ce,
"Tashi muje,"

Hararar sa Najib yayi, ya ce,
"Wannan filin zanje, ai ta kallon na sai kace TV."

Dariya Khaleel yayi, ya ce,
"Wai meyasa kwanan nan duk ka canja. Yau ka fara shiga cikin mutane ne. Dan Allah ka tashi kar mu bashi kunya."

Ba yadda Najib ya iya haka ya mike, suka shiga fili hoto aka farayi musu, sanna suka fara wa Bashir da amaryar sa likin yan dubu dubu.

Suna gamawa suka koma wajen su, akai serving nasum lemo kadai Najib Ya sha.

Kawayen Amarya akayi kira, dan nuna mata kara suma, Summy da wata Aisha aka kira, inda suma sukai musu nasu likin.

Kan Najib a kasa, dan ji yake duk ba a sake ba, dan gani yake da ya ga yan matan nan zata iya masa gizo yazo yana jin kunya.

"Bro kaga wata yarinya da nayi maka kamu."

Kai ka dai Najib ya jinjina.
"Bro Wallahi da gani zatayi maka. Dan baka ga yadda maza ke neman ta kula su ba amman taki."
Dago kai Najib yayi ya kalle shi. Ya ce
"Ni dai na baka wuka da nama."

Dariya suma yi.
Khaleel ya ce,
"Nagode!"

"Dame?"
Najib ya tambaya

"Da ka bani dama."
"Kaji ka. nike da godiya ai."

Suna zaune, har karfe goma tayi, agogon hannun sa Najib ya duba, ya kalli Khaleel ya ce,
"Dare fa!"

"Nagani, yarinyar nake son ta tashi ta fita "
"Yanzu har sai ta tashi zamu tafi."

"Haba man Najib."
"Naji. Amman bari naje mota in ka ga fitar ta ka taho, dan hayaniyar  tayi min yawa "

Ya fada yana mikewa. Wajen Ango yaje, ya duka gefen sa. Dai dai lokacin da Summy ta dago kan ta kenan.

Ya Salam!
Ta anbata a zuciyar ta dan gani tayi ya wuce inda taji ana yabar sa. Kasa dauke idon ta tayi daga kansa.

Tana kissimawa dama wanna mijin tane, da ta huta dan daga gani hutu da jin dadi. Hadi da ilimi sun zauna.

Magana yake masa
"Friend kayi hakuri zan dan fita hayaniyar nan ta fara sa min ciwon ka."

Bashir yace,
"Ba komai. Allah sauwake."

"Ameen! Ya fada, ya kalli Hauwa, amarya yace,
"amarya sai gobe in munzo."

Kasa tayi smda kanta. Tace,
"To nagode!"

Ya sauka ya cigaba da tafiya sa cikin takun kasaitar sa.

Summy kusa sandarewa tayi, dan yadda yake magana ma avin kallo ne ga takun sa na jan hankali da birgewa.

Take taji duk yadda ta dauki kanta ta raina, dan ta gefen ta ya wuce amman be san ma da wata hallita Ita a wajen ba."

Yana fita ya shiga mota ya kwantar da kujerar ya kanta akai. Tunanin yarinyar ya tafi.

Tin bayan fitar sa daga wajen taji duk wajen ya isheta, mikewa tayi, ta fice, ganin haka yasa Khaleel zuwa yayi wa Bashir Sallama.

Yana fita kuwa ya hange ta zata shiga motar ta, da sauri ya karasa wajen ta.

"Sannu yan Mata!'
Khaleel ya fada yana murmushi

Murmushi ita mata, ta amsa masa da yauwah.

"Dan Allah in baza ki damu ba number ki nake so."

Kallon sa tayi, ta ce,
"Number kuma!"

Murmushi yayi, ya ce,
"Eh ita kar ki Damu ba wani abu bane."

Kamar bazata bayar ba kuma sai ta bayar. Sukai sallama ta shiga motar ta, shima ya tafi wajen Najib suka tafi gida.

Tin a hanya ya fara tsara mata kalaman da zata amince da abokin sa, tare da tura mata hoton sa.

lokacin Summy bata Online, dan haka ya bar mata sakkon in ta hau ta gani.

Ranar a gidan su Najib ya kwana.

Summy na zuwa gida bayan ta gama komai ta hau Online, message din Khaleel ne suka shigo ta bude tafara karantawa.

Da farko abin dariya ya bata, ganin wai bashi ne ke son ta ba yake ta tsara ta, haka, bata kara gigicewa ba sai da taga hoton Najib sannan ta mike zaune.

Da farko ta zata idon take mata gizo sai da ta mutsika su sannan taga dai da gaske ne,

Wani uban tsalle ta dukka tana dariyar samun nassara.

Kin maida masada reply tayi dan tana son ta dan ja ajin ta.

Shikuwa Khaleel ya kagu safiya tayi ya hau Online, yaga reply din da zata turo

Wanna yasa tin asuba ya hau, sai dai me ta hau taga komai amman ba reply.

Rasa yadda ze yi yayi, kamar ya kira yaga kuma asuba ce. Dan haka ya ringa Allah Allah safiyya tayi ya kira ta.

Shidai Najib sai kallon Khaleel yake ganin bin-bini ya duba waya ko zega tayo reply.

Shi Najib ma abin har dariya ya fara bashi.


*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now