128

590 49 0
                                    

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE
*128*

"Wayoo ido na!"
Ya fada yana kallon ta.

Ai kuwa da sauri ta dago kanta tana kallon idon nasa.

Kallon juna suke, duk sun kasa kawar da idanun su.

A ran Najwa ta ce,
"Tabbas nasan wannan fuskar da idon,"

Ita ganin kamar su ma takeyi ta wani fannin  haske kadai zata nuna masa.

Allah me iko, Gaskiya Najib kyakyawa ne, dan dai shi baki ne kawai. Amman bakin nasa me kyau ne.

Ga ido da hanci, ga bakin sa dan karami dashi, haka gashin kansa ma me kyau dashi a kwance.

Ba abinda take gani a cikin idon ta face so da kaunar ta da suka mamaye shi.

Shima kallon sanin yake mata, amman yana daukar wannan sanin da ganin da yayi mata sune suke sawa yake kallon ya santa.

Idonun ta ba karamin burgeshi suke ba. Manya ne, masu kyau da su. Gasu farare tas dasu.

In ta saka kwalli wani kyau suke karawa da girma.

Yana son mace mai ido sai gashi Allah ya bashi Najwa me idanu abin shawa'a.

Haka nan bakin ta ba karamin son su yake ba. Dan dan karami ne abin sha'awa gasu pink da su  daga ido ma kasan masu laushi ne.

Haka hancin ta dogo ne gashi siriri. Gaban goshin ta kuwa gashi ne kwance luf luf dashi.

Haka jirar ta me kyau da ita a gyare kamar wacce aka yanke ta.

Suna jima suna kallon sunan su. Kuwa na aikawa da dan uwan sa sakon su ta idanun sa.

Najwa ce tayi karfin halin dauke idanu  ta tare da rufe fuskar ta da hannun masu kyau tsirara dasu.

Dariya yayi, ya ce,
"Muje mu zauna in fada miki abinda nace sai mun hadu."

Gaba tayi a ranta tana son tuno da me zai fada mata.

Akan wasu kujeru suka zauna, kallon ta yayi, ya ce,
"Najwa yau baki tambayen Antyn ki ba."

Murmushi tayi, ta ce,
"Ai haduwar mukenan shiyasa. Ya take, ka baro ta da kewar ka. Allah in nice kafata kafar ka."

Wani dadi yaji a ransa. Murmushi yayi ya ce,
"To Allah kaimu lokacin! Abinda nake son fada miki kenan. Ina da mata. Zaki iya aure na haka."

Kai ta girgiza masa ta ce,
"A'ah!"

Ido yayo waje dasu, ya ce,
"Dan Allah Najwa ki taimaka ki soni a haka muyi aure dan  Allah."

Ganin yana neman ya sauka ya durkusa yasa ta ce,
"Da wasa nake maka fa."

Kallon ta yayi dan ya gano da gaske take.
Kai ta daga masa ta ce,
"To mene dan kana da mata. In ban auri me mata ba. Watakila ni a kawo min ita.
Ba yabon kai ba. Allah bana kin kishiya in har zamu zauna lafiya.
Bana ganin aibun ta sam."

kallon ta ya tsaya yi dan ba karamin burge shi tayi ba.

Kuma ya gano gaskiyar abinda take fada ta cikin idon ta.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now