36-40

888 76 0
                                    

*NAJWA*



By *Maryam S Indabawa*
*MANS*



🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

PAGE *36-40*



Dedicated to *Rashida A kardam*
*Aunty Rash*


Lawalli, ya ce,
"Toh Hajiya."

"Me dame aka kawo?"
Ummah ta tambaye shi.

"Buhun dankali biyu da kwaryar doya biyu."

"Masha Allah a dauki daya a rabawa masu aiki. Doyar ma haka. Sannan ka raba dayan dankalin gida biyu a aikawa makwabta."

"To Hajiya Allah kara budi da arxiki."
"Ameen"

Ya juya ya fita.  Surutu Najib ya cigaba da isar Ummah dashi tin Mami na harara sa har ta kawar da kai.

"Aisha kuci abincin mana. Kai Najib tashi kuje kuci."

"Ummah lokacin sallah yayi bari muje muyi tukkuna."

"To shikenan. Aisha shiga daga ciki ko?"
"Toh!"

Mami ta fada. tana mikewa ta nufi dakin Ummah.

Daki ne me kyau dashi sai kace dakin budurwa ko na amarya.

Komai a gyare tsab dashi sai tashin kamshi yake, gwanin sha'awa.

Ban dakin dake cikin dakin ta nufa shima a gyare dashi sai kace ba'a amfani dashi.

A ran Mami tana kara jinjinawa sirikar ta wajen tsab ta da son kamshi. Duk da ta tsufa amman komai nata kamar na amare.

Ko fentin gidan duk shekara sai an sake haka nan gidan be rabuwa da kwas kwarima.

Alwalar tayo ta fito ta shimfidda sallaya ta tada sallah.

Lokacin Ummah ta shigo itama Alwalar tayo, tazo ta tada sallah.

Suna idar wa suka koma falo. Lokacin Najib ya dawo. Abincin ya sauka ya zuba musu shida Mami.

Burabusko ne da miyar taushe da taji gyada da naman kaji.

Sai kamshi ne ke tashi. Sai zubo da aka hadashi da cocumber.

Yana fara ci ya fara gyada kai dan a rayuwar Najib yana son abincin gargajiya bama waina shinkafa masa, ko dambu, tuwo, biski, dan wake, da gurasa kika hada masa wadan nan kin gama masa komai.

Haka nan lemo, yana son zubo, ginger, kunun aya, ko lemon tsamiya da irin wadan da ake sarrafa kayan marmari.

Sai da suka ci me yawa sannan ya fara zuba wa Ummah santi.

"Ummah wai dame ake biskin nan ne dadin sa yayi yawa gawani gardi kin qi, ki koya min."

"Ah lallai santi nan naka yayi yawa bana koya maka bane."
"Wallahi na manta"

"Toh! Gero da mai sune abin amfanin mu,
"Da farko, zaka samu gero sai a surfa, a bushe a wanke, a kuma regeshi, sai ka tankade shi. Ka sami madanbaci.
(Madanbaci shine abinda ake yin dambu dashi tin lokacin kaka da kakan ni."

"Na gane shi."
"Yauwah, sai ka zuba ruwa a kasan shi madanbacin.
(Amman yanzu zaka iya yi da tukunya, da abin tacar taliya, na karfe amman.
Zaka daura shi akan tukunya, sai ka zuba ruwa a kasa.)
A kan abin tace taliya zaka xuba wannan geron naka da ka gyara shi. Zaka daura akan wuta, yai ta turara har sai kaji yana tayar da kamshi, in ka taba kuma zakaji yayi laushi."

"Oh shikenan ma."
"Eh bashi da wahala. Ai ka iya miyar taushe ko?"

"Na iya amman taki naji tayi wani dan dano da wata kala ta daban."
"Oh saboda na hada da markadadiyar gyada da kuma dakakiya ne."

"Oh Ummah daman ana sa markadadiyar gyada a cikin miya."
"Ai yanzu mafi akasari ma an fisa ta dan tana bada wani dan dano na musamman."

"Gaskiya kam ai naji yanzu."
"Yaushe zan zo kimin dambun gargajiya me zogale."

"Ko yanzu kake so zan maka."
"A'ah ina ni, ina sa matata aiki yanzu, in zanzo zan fada miki."

"Allah kaimu."
"Ameen."

Sun jima suna hira har dare yayi, suka mike suka yi sallah.

Najib kuwa massalaci ya tafi. Inda acan suka hadu da Baffah tare ma suka dawo gida bayan sun yi sallah isha'i.

Baffah ya ce,
"Najib ka kara girma fa."
"Wallahi Baffah."

"Ya kamata kaima kayi aure kana ganin duk sa'anin ka sunyi aure."

Murmushi Najib yayi, ya ce,
"Baffah ana taya mu da addu'ar samun mace ta gari. Kamar Ummah."

"Toh Ameen!  Zance, amman samun mace kamar Ummah a wannan zamanin da kamr wuya, sai dai zan na maka addu'a kame yadda ka nema."

"Yauwah Baffah nima nasan da wuya samun irin ta amman kuma za a samu riba me kyau aka samu me irin halin ta. Dan dacen da kayi da ita shi yasa kai ma duk zuri'ar ka sai dai farin ciki."

"Haka ne, Najibullah, kayi wayo da dabara da hagen nesa da har ka gano haka. Allah baka mace ta gari me ilimi tarbiyya kamar Ummah ko ma fiye da ita."

"Ameen Baffah na."

Baffah tsohun mutum me ilimin addini da na zamani dan tsohon likita ne, duk da ya tsufa ka kalle shi sai kayi tsamanin befi shekara hamsin ko sitin ba.

Fari ne dogo dashi ba fulatanin asalii ne.

A babban Falo suka tadda su Ummah da Mami.

Mami ta zube akasa, tana gaishe shi,
"Barka da dawo wa Baffah."

Baffah ya amsa da,
"Yauwah Aisha."

"Ina yini Baffah?"

Baffah ya amsa da,
"Lafiya lou Alhamdulilah ya kuke ya gida da ma'aika tan ku."

Kan Mami a kasa. Ta ce,
"Duk lafiya Alhamdulilah."

Baffah ya ce,
"Masha Allah kunzo lafiya."

Najib ya ce,
"Lafiya lou."

"Madallah."
Jamila me aikin su Ummah ce ta kawo musu abinci.

Ummah ta dubi Mami cikin kulawa da kaunar sirikar tata.

Ta ce,
"Aisha ku sakko kuci abinci."

Ta fada tana mikewa. Baffah ma bayan ta yabi.

Najib kuwa ya mike, ya bude abincin ya fara hadiyar yawu.

Tuwon farar shinkafa ne, ya tuko lukwi dshi yayi fari tas dashi, sai miyar Kuka da taji naman kasuwa. Gefe kuma yajin daddawa ne, da kakile.

Sosai yaci abincin. Sai da suka gama suka shiga sukayiwa su Baffa Sallama.

Shadda Najib ya bawa Baffah kala uku, da kudi dubi hamsin akai.

Sannan ya bawa Ummah turmin atamfa uku da dubu hamsin ita ma.

Godiya suka dinga masa. Har bakin motar su, suka rako su sanna. Suka juya.



*INDABAWA**

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now