141

703 43 0
                                    

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online WRITERS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH DAUKAKAKI YASA KI GAMA DA DUNIYA LAFIYA.*

*REALLY LOVE U ANTY NA*

*THANKS FOR UR LOVE ND SUPPORTING*

*PAGE*
*141*

*Kai ni kam Alhamdulilah. Masoya nagode muku. Allah kara zumunci. Allah barmu tare, sakon nin ku dayawa ya sameni dan haka ba abinda zance sai godiya da fatan alheri gaba dayan mu.*

*Nima ina son ku gaba dayan ku*


"Najib mijin ki, kinsan yayan ta ne ai."

Wata uwar ashar ta lailayo ta.
"Mama ta ce,
"Sumaiyya wai ke baza kiyi hankali bane, mene abin zagin ai sai ki godewa Allah da ya baki kishiya kamar Najwa ma."

"Mama kinsan me kike fada kuwa?  Najwa fa kika ce, yarinyar da nafi tsana duk duniyar nan."

"Ni kike fadawa haka. Ni kike fadawa  bakya son yar uwata."
"Haba Mama ai wata kusan tafi wata kusan."

"Allah ya shirya ki,"
Kashe wayar tayi. A ranta tana mamakin anya kuwa Mama mahaifiyar ta ce.

Kanwar Abban ta, ta kira, Kaltum.
Kaltum itama cikakiyar yar duniya ce, shiyasa tasu taxo daya da Sumaiyya.

Kaltum na daga wayar Summy ta fashe mata da kuka.
"Lafiya 'yata.?"

"Anty, ina shegiyar yarinyar nan Najwa?"

"Eh naji na gane ta."
"Anty wai ita zata auri mijina. Anty ya zanyi dan Allah Anty ki taimake ni. Wallahi Najwa ta shigo gidan nan nasan mutuwa xanyi, wallahi na tsane ta dan Allah Anty ki taimaka min."

"Ya isa ya isa, yanzu akan wannan kike kuka. To ki kwantar da hankalin ki. ki bar min komai a hannuna. Me ita Maman taki ta ce."

"Kinsan Mama ai, wai murna ma take yi."
"Murna? Wannan wacce irin uwa ce. Daba dan a gabana Maman ki ta haifeki ba da nace, ba yar ta bace ke. Ki dai na kuka zanji da komai."

"Yauwah Anty na nagode kar ki damu."
Sukai sallama.

Antyn ta, Kaltum mikewa tayi gidan Su Kakanin Najwa, daga nan tayi gidan su Najwa.

Duk inda taje masifa da rashin mutunci take akan su janye auren nan ko, kuma suga abinda zai biyo baya.

ko Kunyar idon su Baba da Mama bata gani ba. Haka a gidan su Najwa ma.

Mami bata ce mata kala ba. Basma dake daki tajiyo hayaniyar ta, lekowa tayi ta barandar benen su.

Kaltum na ganin ta, ta zata Najwa ce, ta hau zagi  ta uwa ta uba da ce musu matsafa dan sunga tana jin dadin mijin ta shine suke son su aura mata shi.

Mami dai ko kala bata ce ba. Fitar ta daga gidan kenan Dady ya shigo.

Mami ya sama tana kuka.
Lafiya Mamin Najwa?"

"Ina fa lafiya Dady, akan hada auren Najwa da Najib ne, yanzu Kaltum taje ta gama zage su Mama fitar ta kenan nan ma tazo ta gama mana kwasar Allah tsine."

Saukowa Mami tayi daga kan kujera, ta durkusa a gaban sa, ta ce,
"Dady ni da iyaye na munfi kowa son hadin nan. Amman tinda abin na neman rabewar zumunci dan Allah ku taimaka ku sa a janye batun nan dan Allah."

Kamo ta Dady yayi, ya ce,
"Mamin Najwa, nasan kina son na, kuma kina son zuri'a ta, to dan Allah kuyi hakuri, wannan abun ya faru dan shige burin su Baffah ba tin yau ba. Dan Allah kuyi hakuri."

NAJWA Complete ✔जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें