132

587 52 0
                                    

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE
*132*

*Ummu Ayda na gode sa kaunar ki gareni da littafi na. Nagode Allah bar kauna. Ameen*



Baffah da kansa yaje ya dauko Najwa dan ya ce, acan zasu je ta sauki bakon nata.

Duk abinda zatayi amfani dashi sai da ta diba sannan ta tafi.

Ranar da zai sauka tare da Ummah suka shiga kitchen suka tare shi da abinci kala kala na gargajiya da na zamani. Hakan nan lemo ma.

Ba wanda yakai su Ummah murnar hadin nan.

A gidan su ya sauka, da yamma ya kira ta, ta bashi address din inda take.

Murmushi yayi da yaji tana gidan su Ummah.

Kayan da ya kawo musu ya diba ya fito.

Cikin wata light brown din shadda an mata aiki da dark brown din zare dark brown din hula ya saka da takalmi.

Idon sa kuma sanye da farin tabarau ba karamin kyau yayi ba.

Sai tashin kamshi yake.

Ummah da kanta tasa aka kawo mata me yin kwalliya wai sai an wa Najwa kwalliya duk hakurin da ta bawa Ummah kin yadda tayi.

Me kwalliya ba karamin kwalliya tayiwa Najwa ba.

Dan tayi kyau ke kyace amarya ce.
wata atamfa ta dauka jikin ta siiblue, da orange a jiki.

An mata dinkin riga da siket, dinkin ya zauna a jikin ta sosai.

Dauri akai mata shima me kyau wanda ya kara fito da kyan ta.

Turare Ummah ta bata ta feshe jikin ta dasu.

A falon Ummah aka jere masa duk abinda zai bukata.

Biyar da rabi ya kirata yace, ya karaso.

Ummah ta fadawa ta fita shigo dashi. Yana tsaye a jikin motar sa ya harde hannun sa a kirji.

Kofar da zata fito ya zubawa ido. Duk gaisar dashin da suke hankalin sa na kan Najwa da ta fito.

Baki ya saki da hanci yana kallon ta. Har ta karaso be san ta karaso ba. Sai da ta tafa hannun ta sannan ya dawo cikin hankalin sa.

"Hamma wannan kallon haka."
ta fada kan ta a kasa.

Murmushi yayi, ya ce,
"Ai ke din ce."

Dan hararar sa tayi, ya ce,
"Ni shige muje."

"Haba sarauniyar mata, ina nasan gidan da zanyi gaba."
Gira ta daga, ta ce,

"Haka ne fa."
Tayi gaba ya biyo bayan ta.

Har babban falo ta dire shi, sannan ta zame kasa ta gaisar dashi.

Kasa amsawa yayi, sai kallo da ya bita dashi.

"Hamma!"
Ta fada a shagwabe.

"Menene?"
"Ina gaishe da kai kayi shiru."

"Ayyah yi hakuri wallahi duk na rasa control di nane."
Ido ta zaro, ta ce,

"Hamma gidan mutane fa."
"Gidan mu dai. Ba gidan kakan nn ki bane."

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now