146

602 30 0
                                    

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*145*

Wannan shafin naka ne, *UMAR DALHA* Allah bar zumunci.
*Ameen*



*Shafi daya zan na kawo muku, saboda ina busy kwana biyu.*

*Nagode*



Sai la'asar sakali suka bar gidan umma, bayan ta gama wayar wa da jikar tata kanta. Najwa duk sai wani nauyin ta ta dada ji.

Haka nan Najib shima kamar yasan abinda akai amman wai kunyar sa take ji.

"Ummah me kuka tattauna ne ni babu ni"
Najib ya tambayi Ummah da suka rako su shiga mota.

"Kaji ka kai muka san me kuka tattauna da zaka tambaye mu."
Ummah ta bashi amsa.

"A'ah mu ba abinda muka tattauna."
Abbah ya fada.

"Ashe dai daya muke da kai."
Ummah ta fada

Dariya sukai suka shige mota. Suna dagawa kakan nin nasu hannu.

Sai da suke tafiyar muntina ba wanda yayi wa dan uwan sa magana. Kallon ta yayi, ya ce,
"Me Ummah ta fada miki ne naga duk kin canja."

Baki ta murguda mashi ta ce,
"Bakaji me Ummahn ta fada ba kenan."

Kallon ta yayi ya ce,
"Eyye ni kike murgudawa baki, lallai yarinya, wato rashin kunya Ummah ta koya miki ko?"

Bakin ta ta rufe da sauri dan ita bata san ma ta murguda masa bakin ba.

"Zaki sani ne."
Yayi dariya ciki ciki.

Ita dai shiru tayi tana nazarin magan ganun Ummah, "gaskiya abin da nauyi wallahi. Amman ya zanyi zan gwada naga yadda abin zai kaya."

Ajiyar zuciya ta sauke, da dauri Najib ya kalle ta, ya ce, "Lafiya?"

Murmushin son kare kai tayi, ta ce, "lafiya lou."

Kallon ta ya tsaya yi, ya ce, "Gaskiya Najwa keda Ummah baku da gaskiya ban yadda da wannan ajiyar zuciyar ba. Dan fada min kinji."

Ya miko mata kunnen sa, matsowa tayi kamar wacce zata fada miki. Murmushin mugunta tayi, tana kai bakin ta bakin kunnen ta sakar masa kara a kunnen.

Da sauri ya janye kunnen sa yana kallon ta, dariya ta saki, tana masa gwalo.

Girgiza kai yayi, ya ce, "zan rama ne."

"Haba Hammanah kayi hakiri." Kafada ya makale, ya ce, "Naki wayon."

"Please man." Kallon ta yayi yana mamakin canjawar ta, rabon da ta sake tai masa magana tib kafin kawo kayan lefen ta.

"Kallon fa!" Gira ya daga ua ce, "ke duk kin gama tafiya dani."

Baki ta tabe, ta ce,
"Kai dai."

"Baki yadda ba ko, bari sai kin shigo gidana zan nuna miki irin son da nake miki."
Shiru tayi, motar ya tayar suka dauki hanya.

Suna isa yayi locking motar, ta yunkura zata bude ta kasa, kallon sa tayi, ta ce,
"Bude mana."

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now