123

554 53 0
                                    

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *123*

"Allah yasa su zo, dan basa kula samari."

Ta fada tana yin cikin dakin nasu.

Kallo ya bita dashi, har ta kure masa.

Tana shiga dakin suka gaisa, sannan ta ce,
"Anty Najwa da Anty Zahra wani ne a waje yace dan Allah kuje wai."

Kai Najwa ta dauke ta hau kan gadon ta, dinkin da suka amso ta dauka tana karawa da mayafin da suka siyo.

Zahra kuwa kallo  ta, ta tsaya yi.
Je kice gamu nan."

Ta juya ta fita. Fada masa tayi, kudi ya debo ya bata kin amsa tayi sai da kyar.

Yarinyar na fita Zahra ta matsa gun Najwa tace,
"Wai ke mene haka kinji dai abinda aka ce ko? Kinsan waye?"

"Ban sani ba dan haka bazani ba."
Mikewa Zahra tayi ta Dauki Hijab din ta. Tayi waje.

Tin daga nesa take kallon sa tana son tina a ina ta sanshi.  A ranta ta ce, ko me kama dashi ta sani ne.

Karasawa tayi wajen sa da sallama.
gaisawa sukai cikin girmama shi.

Fuskar sa dauke da murmushi ya ce,
"Dan Allah kiyi hakuri nasan baki sanni ba, amman dan Allah yar uwar ki da kuka shigo yanzu nake son gani."

Kallon sa tayi, gayen yayi beda makusa kuma kowa zai yi kwadayin samun sa.

A fuskar nagarta kuwa daga kallo kasa mutunin kirki ne.

"Kinyi shiru?"
Ya katse mata tunani.

Murmushi tayi, ta ce,
"Najwa yanzu bazata iya fitowa ba kanta ke ciwo magani ta sha har ta kwanta ma."

"Ayyah to ki mata sannu amman dan Allah gobe zan dawo ko zuwa anjima."

Amsa masa tayi da
"Ba komai."

Godiya yayi mata ya shiga mota ya tayar.
Zuciyar sa kamar kankara dan murna da farin ciki.

Daga nan gari ya shiga zagayawa cikin nishadi abinda be taba yi ba a garin katsina ba kenan.

Tana shiga daki ta kara sa gefen gadon da Najwa ke zaune.

Kallon ta tayi, ta ce,
"Sis gunki yazo, amman nace baki da lafiya. Ya ce anjima ko gobe zai dawo."

Kai ta dauke kamar bata ji ba.
"Wai kuwa lafiyar ki kalou kuwa? Allah ina jin sai na hada ki da Mami."

Harara ta tayi, mikewa tayi ta koma kan kujerar dake dakin. Tana magana

"Amman fa gayen ya gama haduwa da badan ina da Mustapha na ba da ba abimda zai hana in so shi."

Tsaki Najwa tayi ta dauki littafin ta tana dubawa.

Dariya Zahra tayi itama ta dauki littafin ta tana dubawa.

Besamu komawa a daren jiya ba dan haka yau tin karfe goma ya dira a makarantar.

A lokacin ma suna jarabawa yafi awa daya sannan aka fara fito daga jarabawar.

Yarinyar jiya ya hango, dan haka ya dago mata hannu.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now