163

733 53 0
                                    

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*163*



*INDABAWA Hausa Novel group tnc for love nd supporting.*
Allah barmu tare Ameen.



Kallon sa take a ranta tana fadin sai ta san yadda ta raba Najwa da shi.

"Ya kika tashi?"
ya tambaye ta yana zama a kan kujerar gaban madubi.

"Lafiya lou! Ya Najwan?"
Ta tambaya

Kallonta Najib yayi, kafin yace,
"Tana lafiya, kinsan masu ciki sai da  lalashi."

Zabura tayi jin ya ambaci ciki.
Kallon ta yayi ya ce,
"Lafiya?"

"A'ah ba komai."
Ta fada cikin rashin gaskiya.

Kafada ya dage ya ce,
"To ni zan fita sai na dawo."

Bama taji me yace ba saboda ta tafi tunanin Najwa na da ciki.

"Tab ai bata isa ba, ciki tazo ta haihu, ta gaje dukiyar sa."
Ta fada a fili.

Dakin ta fara zagayewa tana tunanin abinda zatayi.

Ta jima kafin tayi  tsalle na tuna abin yi.

Sai da ta tabbatar Najib ya bar gidan sannan tayi wanka ta shirya.

Najwa kuwa tana can ta raka mijin ta tana masa addu'a.

Falo ta koma tana zaune tana waya da Hamma Salim.

Suna gamawa ta mike dan zagawa bayan gidan.

Sanye take da dogon hijab har kasa fuskar ta tayi kyau tana tafiya tana kallon wajen dan duk kallon da take masa ta taga ne bata taba zuwa gun ba.

Kamar ance ta kalli gefe taga Sumaiyya wata faduwar gaba tayi da sauri ta fara karanta addu'a a cikin ran ta.
*Allahumma inna naj'aluka finuhurihim wana uzubika min shururihim*

Gaba tayi, ta zauna a gun da aka tanadar dan zama a huta.

Ta jima a gun dan sallah azahar ita ta tashe ta.

Bangaren ta ta koma, tayo alwala ta tada sallah.

Tana idar wa ta shiga kitchen, tayi miyar ta tin jiya dan haka ta daura farar shikafa da taliya sai kwai da ta dafa.

Tayi hadin Kabej da dankalin turawa da bama da waken gwangwani.

A firij ta saka sai lemon Mangoro da tayi.

Falo ta koma zama tayi da bismillah tana shafa cikin ta. Addu'a ta tofa a cikin nata. Waya ta dauka, ta kira zahra. Mikewa tayi ta dauko Maltina a cikin firij ta dawo ta zauna.

Suna gama waya tayi waya da Mami, Mami na kara jan hankalin ta akan ta dage da addu'a da karanta alkur'ani ko dan cikin jikin ta.

Godiya Najwa tayi Mami na saka mata albarka.

Tana gamawa ta kira Mamin Najib ta gaishe ta, tambaya ta hau yi mata me take so?

Ba abinda take bukata dan haka Mami ta barta.

Sumaiyya kuwa tana can tana leken Najwa har ta bar wajen sai da ta dauki awa wajen biyu sannan ta shiga daki ta dauko maganin da aka bata da Maganin zubar da ciki tayi bangaren Najwa.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now