81-85

630 61 0
                                    

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻


PAGE *81-85*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*



Sai karfe shida su *Najwa* suka dawo daga makaranta.  Lokacin Mami Najib da mami suna saman bene a dakin Mami suna hira.

Saman suka hau, suka nufi dakin Mami. Danyi mata sannu da gida.

Sannan sukayi dakin *Najwa*   dan cire kayan makarantar su.

Suna cirewa, *Najwa* tasa Basma dauko jakar makarantar ta, dan yin homework din ta.

Suna gamawa suka shige sukayi alwala dan yin Sallah magariba.

Mamin suna hira, Basma ta shiga dakin.

Kallon ta Mami Najib, tayi, ta ce,
"Ina *Najwa* ?"

Basma! Ta ce,
"Adda tana daki."

Mami ce ta kalle ta. Ta ce,
"Tashi kije ki kirata."

Basma ta amsa da
"Toh!"

Basma ta fice a guje tayi dakin *Najwa* tana kwada mata kira.

Tare suka dawo da *Najwa* na sanye da hijab din ta har kasa.

Da sallama suka shiga dakin. *Najwa* ta zauna a kasa gefen kafar Mamin Najib.

Fita Mamin *Najwa* tayi dan hada wajen cin abincu.

Mamin Najib ce, ta kalli, *Najwa* ta ce,
" 'yata yanzu ajin ki nawa."

Murmushi *Najwa* tayi, ta ce,
"Mami nayi candy wannan shekarar."

"Masha Allah! Yanzu kuma sai ina?"
"Katsina zan tafi, wajen Anty Hauwa."

"Anty Hauwa ta dauke ki, da na dauke ki ai."
"Amman kafin a fara makaranta zaki kawon ziyara ko."

"Eh! Mami insha Allah!'

Dai dai shigowar Mami da kayan abinci a hannun ta, *Najwa* ce ta mike, ta amsa ta dire a gaban Mami.

Fulas din ta bude, wainar shinkafa ce a ciki, sai miyar agushi da Mami ta saka mata nama.

Sai lemon abarba da kwakwa. Zuba mata *Najwa* tayi sannan ta mike tayi dakin su.

Kur'anin ta, ta dauko, tana muraja'a.


Duk yadda Najib yaso yau yaga yarinyar be samu dama ba, dan basu dawo gida ba sai bayan sallah isha'i duk jikin sa yayi sanyi dan jin sa yake kamar mara lafiya.

Suna shigowa gidan suka zauna a falo, wayar sa ya dauko, ya kira Mami.

"Hello Mami ki fito mu tafi."
Mami dake cin abinci, tace,

"Najib ai ka bari kuci abincu ko?"
"Na koshi ki sauko mu tafi "

"To shikenan gani na."

Ta katse wayar tana kallon Mami. Ta ce,
"Dan naki ya tada darunsa muzo mu tafi."

Mami ta ce,
"Najib kenan har yau yana nan da rigimar sa kenan."

"Gashi nan kuwa kin gani."
"Dan ma Allah yasa, Yaron nawa akwai hankali."

"Daman haka zakice."

Mamin Najib ta mike,  tana cewa,
"Bari mu tafi kar muyi dare a waje."

"Dama kwana kukayi."
"Mamin *Najwa* kenan. Muje dai."

Suka fito, Mamin Najib ta ce,
"Ina *Najwah* ne?"

"Tana daki, bari na kirata."
"A'ah barta, bari naje na ganta."

Murmushi Mamin *Najwa* tayi sukayi dakin *Najwa*

Tana zaune tana koyawa Basma karatu suka shiga.

Tsayawa tayi, taba murmushi. Mamin Najib tace,
"Sannu da kokari *Najwa* mu zamu tafi, ga wannan."

Ta mika mata wata katuwar bakar leda.

Hannu biyu *Najwa*  Tasa ta amsa, tana godiya. Mikewa tayi da niyyar rakata.

Amman tace tayi zaman ta, komawa tayi ta zauna tana musu addu'ar komawa gida lafiya.

Mamin Najib ta tafi da son yarinyar dan *Najwa* abar burgewa ce ga kowa saboda hankalin ta da nutsuwar ta

Suna sauka Najib ya mike, Mami ce tayi kitchen, ta dauko masa abincin da ta zuba masa a basket.

Ta foto, ta mika masa, ta ce,
"Gashi in kaje gida kaci abinci, tinda kaki ka zauna kaci."

Najib ya ce,
"Mami ba haka bane."

"Toh! Ba komai."

Tare suka fito har Salim dan sai da suka ga tafiyar su sannan suka koma cikin gida.

Tin a mota Mami, ta gane Najib din nata ba dai dai yake ba. Batai masa magana ba har sai da sukaje gida, suka zauna. Ta ce,

"Son lafiya kuwa?"
Murmushin karfin hali yayi. Sannan yace.

"Momy ba komai."
Kallon sa tayi cikin mamaki. Ta ce,

"Wai me yake damun kane yanzu, naga baka da abokin shawara sai ni amman yanzu kana son kadaina fada min damuwar ka."

"Mami ba haka bane bana son kema ki shiga cikin damuwar ne."
Ya fada cikin sanyin murya.

"Amman kasan ai dole na shiga damuwa. Dan ko ta kallon ka nasan akwai abinda ke damun ka. Kuma in ka fadamin zan taya ka da addu'a."

"Haka ne Mami, akan Yarinyar nan ne wallahi, har yanzu ba nasara ban ganta ba dazu, gashi munyi dare dazu har sun tashi. Gashi gobe alhamis. Ga lokacin tafiyar mu na karatowa."

Murmushi Mami tayi duk dan ta karfafa masa gwiwa. Ta ce,
"Son ka kwantar da hankalin ka. Insha Allahu zaka ganta. in ma baka ganta ba ni na gano maka wata ma."

Murmushi yayi. ya ce,
"Wace Mami."

"Yar wajenka mana *Najwa* mana "
"Mami *Najwa* kuma."

"Eh ita, wai yaushe rabonka da *Najwa* ma tukkunna."

Murmushi yayi, sannan yace,
"Mami tin bayan dawowata befi sau biyu muka hadu ba! Shekaru biyar baya."

Kai Mami ta jinjina. ta ce,
"Lalai to baka ga yadda *Najwa* ta koma ba. Sak irin yarinyar da kake son aura. Dan *Najwa* akwai ilimi hankali, nutsuwa, ai dai kasan ko wace Mamin *Najwa* kuma kasan irin tarbiyyar da yake baku."

"Gaskiya ne Mami amman ni *Najwa* a kanwa na dauke ta."

"To shikenan Allah nuna maka waccen din."
"Ameen!"

"Tashi kaci abinci. Dan Mamin *Najwa* kamar tasan zamuzo tayi abinda kake so."

"Mami me ta dafa mana."
"Duba kaga."

Da sauri ya janyo fulas din, ya bude. Wata ajiyar zuciya ya sauke lokacin da idon sa ya sauka kan masar da tayi.

Murmushin fuskar sane ya dadu, sannan ya zuba yace, Mami tazo suci.

Ta koshi tace masa, haka ya ci abincin duk ransa ba dadi duk yadda ya kai da son masa kadan yaci ya mike.




*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now