131

596 40 0
                                    

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE
*131*

*Hajiya Nafisa. Our lovelly Anty. U are like Mother to us. Really love u. Tnx for ur Care. May Allah bless you.*
Ure  so special to me. Tnc for ur love.

*Allah ya barki da mijin ki ya yara Ya'yan ki, Allah kara miki lafiya da nisan kwana.*

*So much love Anty na.*

*Allah kara hade kan mu, dukkan marubuta.*
*Ameen*

Kallon sa Dady kawai yayi, tunani Najib ya tsaya yi.

Number Najwa ya kira bugu daya ta daga, kafin tayi magana ya ce,
"Wai Number wa kika turon ne?"

Shiru tayi, ta ce,
"Wacce Number?"

"Number da Address da kika turon jiya."
"Oh na Uncle dina ne."

"Uncle din ki?"
"Eh! Menene?"

"A'ah babu komai zan kira ki anjima."
Ya kashe wayar kan sa ya dafe.

Kara kiran ta yayi, dagawa tayi,
"Please dan karai.min resending kinji."

"Toh!"
Ta katse wayar. Ta tura masa.

Number Dadyn ce dai, wayar Dady ce tayi kara,

Dubawa yayi yaga dan uwan sa ne, dagawa yayi, da sallama.

"Assalamu Alaikum!"
A can bangaren ne aka amsa masa da.

"Wa'alaikum Salam Dan uwa."
"Na'am dan uwa ya gida ya iyalai."

"Lafiya Alhamdulilah!"
Najib mikewa yayi ya hau sama dakin Mami ya shiga.

Mami na zaune ta kalle shi, gani tayi ya canja lokaci guda.
"Lafiya Najib?"

Kan gadon ta ya fada yana fitar da wani irin numfashi, dafashi tayi, ta ce,
"Najib lafiya?"

Zai yi magana Dady ya shigo kallo  su ya tsaya yi.
"Mami na kasa ganewa ne?"

"Me ka kasa ganewa?"
"Mami ta kuma turon Address din da Number duk na Dady ne wallahi."

"Toh!"
Mami ta fada tana Kallon Dady da sai murmushi yake yi.

"Dady kana jifa."
"Naji Mamin Najib, kinsan wa Najib yake so ne?"

"A'ah!"
Ta fada tana zukuwa taji wacce yake so.

"Najwan kice fa?"
"Najwa ta."

"Eh Najwan Ahmad."
Ido ta zaro, ta ce,
"Da gaske?"

Murnushi yayi, ya ce,
"Yanzu Ahmad ya kira ni yake fada min Najwa an fito amman ya bada Number ta da addrss dina. Kinga kuwa ai ita ce."

Najib dake kwance tini ya mike da sauri yana kallon Dady.
"Dan Allah Dady da gaske."

Ya fashe da Dariya, Dady ya rumgume yana murnar da farin ciki.

Mami kuwa kallon sa ta tsaya yi, a ranta ta ce,
"Allah ya amsa addu'ar ta da ta su Baffah kenan. Ba ahada su ba sun hada kan su."

Najib ne ya kalli Mami, ya  ce,
"Mami tunanin me kike?"

Murnushi tayi, kawai ta zauna a gefen su.
"Wai kar dai kace daman baka san Najwa ba yarinyar da rainon ka ce,"

Dariya yayi ya ce,
"Mami kibar wannan zancen, wallahi abin ma abin kunya."

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now