107-110

802 64 0
                                    

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *Maryam S Indabawa*
*MANS*

PAGE *107*




Ita kuwa Summy ranar bata tashi daga bacci ba sai karfe dayan rana. Sallah ma sai alokacin tayi.

Wanka tayo sannan ta shiga kitchen dan samun abinda zata ci. Dankali da kwai akayi musu sai kunun gyada. Diba tayi ta shige daki ko gaishe da iyayen ta bata yi ba.

Sai da ta cika cikin ta sannan ta dauko wayar ta. Hoton Najib ne akan wayar dan tana kallon hoton bacci ya dauke ta bata sami ba.

Wani murmushi ta saki tina mafarkin da tayi da shi. Data ta kunna ta hau online, tana duba messages.

Tana zuwa kan Khaleel taga messages nashi wajen guda ashirin. Dariya tayi ta bude, duk rokan ta yake da ta amince.

Ita kuma sai jin dadi take, ta kasa tunanin me ya hana shi wanda yake son ta yi mata haka. Ita dai kawai hankalin ta yayi wajen Najib din ke saka shi.

Sai da ta ja aji sannan tayi masa reply da.
"Haba Khaleel daga ganin sarkin fawa sai miya tayi dadi. Ban san ko shi waye ba haka nima ban san sa ba."

Turawa tayi ta sauka dan tasan yana ganin sakon ze dawo mata da amsa

Waya ta dinga yi da samarin ta wanda ta dauki wajen awa daya ko me suke fada oho.

Khaleel kuwa sosai ya shiga damuwa na rashin ganin bata hau online ba har dayan rana.

Kai kace shi ke son ta. Amman wannan abin duk abokin sa yake yiwa.

Shi kuwa Najib ba abinda ya dame shi sai na yarinyar da ya gani ta daga masa hankaki.

Wanan shi ake kira, son maso wani. Ita Summy ta macewa Najib shi kuma yana son wacce bata son yanayi ba.

Karfe daya suka tafi massalaci sukai sallah suna fito wa. Khaleel ya dauki waya ya duba amman har lokacin bata hau ba.

Sai da suka je gida suka ci abinci sannan ya kara dubawa sai a lokacin yaga sakon da ta turo masa.

Duk da sakon ba abinda yake nema ya sanar masa ba amman yaji dadi ganin ta dai hau har ta bashi amsa.

"Sumaiyyah ki yadda dani da kuma aboki na, abokin na mutum kirki ne, yan mata dayawa na son sa ba dan kyan sa ba kawai dan hankalin sa da ilimin sa both (dukka) yana da dadin mu'amala. Be kula yan mata, dan be son yaudara kuma a Shirye muke ko da kince mu fito."

Ya tura mata haka.
A kunne ta bar datar ta, dan jiran jin sakon sa. Yana shigowa ta fara ganin sa a notification din ta. Kin budewa tayi dan ta ja aji. Duk da zuciyar ta, ta kwadai tu da taga me ya rubuto mata.

Sai da ta bada minti goma baya sannan ta hau ta bude sakon. Murmushi tayi, ta ce,
"Nasan da haka dan daga gannin sa ma ya wuce duk tunanin me tunani."

Ta fada tana tura musu da sakon.
"Naji Khaleel amman kuma kasan ni wace da har zaku soni, kasan yaya nake, kasani ko ina da wanda nake so."

Khaleel kin sauka yayi tinda ya tura mata sakon ta kawai yake jira ta maido masa. Ko da sakon ya shigo ya duba sai ya kara nutsuwa da yarinyar.

Murmushi yayi ya tabo Najib.
"Aboki yarinyar nan fa ta hau."

Baki Najib ya tabe, ya ce,
"Ai naga alama tin da naga kana ta wani danne danne."

"Allah zakayi farin ciki da zabi na, bari nasa ta turo min pics nata."
Khaleel ya fda.

Ko kallon sa Najib beyi ba, bare yasa ran samun amsar sa.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now