168

778 57 0
                                    

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*168*

*Nagaida ku duk writers ina mika sakon gaisuwa ta tare da jinkinar ban girma. Allah ubangiji ya kare mun ku daga sharrun mutum da aljan da duk abin ki. Allah kara basira. Allah kara hada kan mu.*
*Ameen*

Ina kaunar ku gaba daya.

*kuyi hakiri na jina da kukai shiru kwana biyu.*

*Hakan ya samune na zama na bana samun yi. Amman ayi hakuri.*

Kara gaisawa sukai Mami na tambayar ta ya jikin ta ya su Sumaiyya da me gidan.

Mami dai sai nan nan take da Najwa, Dan ba karamin dadi taji da ta ganta ba.

Haka nan Basma kamar ta goya Najwaa take ji.

Bamma salim ma yana dawowa daga kai. mami yazo ya saka Najwa a gaba wai tayi kiba shi da yake ya ganta da bata da lafiyar.

Ana fadawa Dadyy Najwa ta dawo ya baro office yazo ganin Najwan sa

Kowa yayi murna da zuwan Najwa. Inda aka debi. Kayan ta a kai dakin ta na da.

Mami da kanta ta hada mata ruwan wanka.

Bayan ta fito ne Najib ya kira suka sha hira abin su.



A bangaren Sumaiyya kuwa safiyya nayi ta kwashi kayan ta ta hada ta tafi tasha ta hau mota sai kano.

Ko da ta isa kano gidan su Antyn ta ta wuce, Antyn tasai zuga ta take akan ta bar wani Najib ta shigo gari kawai.

Sai da ta gama ziga ta sannan sukai gidan Mama.

Mama na zaune suka shiga kallon su ta tsaya yi taga daga ina suke tare.

Zama sukai sumaiyya ta mikawa mama takardar hannun ta.

Budewa mama tayi, ta zaro ido tana salati.

Ta ce,
"Yanzu abinda kikai kenan Sumaiyya. kin kaso auren kin dawo. Mene. Najib baya mana amman kika ki zama. Allah ya shirya ki sai kizo mu zauna tare ai."

Mikewa sukai ita da Anty sukai dakin Sumaiyya na da.

Da farko Sumaiyya taso ta sa damuwa aran ta sai daga karshe Anty ta hure mata kunna.

Inda tin kafin ta gama idda suke fita yawon su.

Lokaci kankani Summaiyya tai yi kudi da mota.

Duk yadda Mama zatai mata fada sai ta ce, ai a gidan su Antyn ta suke.

Daga karshe can ta koma da zama. shi kuma baban ta murna yake ta koma gidan Mahaifiyar sa da zama

Mama dai addu'a take mata dan sam ita bata son mu'amalar ta da Amtyn ta.

Najwa kuwa duk tabi kannen Mami da yayan ta da matan yayen ta tai musu alheri kowa da abinda zata kai masa duk da suna da rufin asirin su.

Har wajen Maman Sumaiyya sai da taje tai mata alheri.

Taje wajen su Ummah, inda ummah ta kara gyara jikar ta kamar me.

Najib kuwa yana can yana musu shirye shiryen tafiyar su.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now