11-15

1.3K 108 1
                                    

*NAJWA*


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*




🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾

PAGE *11-15*





DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

SO MUCH LOVE U








"Honey!"
Dady ya fada daga dayan bangaren.

Ido Najib ya zaro ya sheke da dariya.

Hararar sa Mami tayi. Ta amsa da
"Na'am sweety nah'

Ido ya kara warewa yana dannen baki dan kar dariyar sa ta fito.

Kai Mami ta dauke. Ta maida hankalin ta kan wayar.
"Baby na kina lafiya ya gidan wallahi sai kewar ki nake."

Wani murmushi ta saki me kayatar wa.  Ta ce,
"Nima haka ya aikin?"

"Aiki Alhamdulilah! amman ba kamar yadda zaiyi sauki ba in kina gefe na."

Mami ta rausayar da kai. ta ce,
"Ayyah kayi hakuri ai yanzu ma kana dauka ina gefen naka."

"Zan na gwadawa."
ya fada daga dayan bangaren.

Sannan ya ce,
"Me kike yi yanzu."

Mami cikin sanyin murya, ta ce,
"Bacci zan kwanta."

Murmushi yayi me sauti sannan, ya ce,
"Kin min kwalliyar da kika saba min."

Ido Najib ya kara ware wa ya mike zai fice. Janyo shi tayi.

Sannan ta ce,
"Wallahi ba inda zaka, sai da nace a'ah ba kaki."

Dady ya ce,
"Ke da waye ne?"

"Kai ma ka sani ai."
Dady yayi dariya dan yadan Najib da tsokana.

"Me yayi miki."
Ya tambaya daga dayan bangaren.

"Ka kira ya nace sai nasa a speaker. Shine yake ta wani ware min ido da yin dariya yanzu kuma ya mike zai fice."

Dady ya kira shi.
"Son!"

Najib ya sunkutar da kai, ya amsa da,
"Na'am Dady!"

"To ai sai ka zauna ka koyi soyayya tinda abinda kake son gani kenan."

Najib ya rufe fuska da hannun sa, ya ce,
"Nifa Dady ba haka nake nufi ba. Kawai hira nake son muyi gaba dayan mu."

"Kai ka sani dai. Ka bari in kayi budurwa da kai na zan na koya maka yadda zaka sace zuciyar ta. Kamar yadda na dauke ta Mamin ka."

Dariya sukayi gaba daya daga nan kuma yake tambayar sa ya aiki.
sai hira ta barke kamar duk suna tare.

Sun jima suna hira sannan sukai sallama. Alwala Mami ta mike tayi ta canza kaya ta kwanta.

Najib ne ya gyara mata rufa sannan. Ya duka gefen ta. Ya ce,
"Mami sai da safe."

"Allah tashe mu lafiya."
Ta sumbace sa a kumatu.

Ya mike ya kashe mata kwai sannan ya fita.

Dakin sa ya nufa yayi wanka yayi alwala sannan ya haye gadon sa.

Addu'ar bacci yayi ya tofe jikin sa sannan ya lumshe idanun sa.

Karfe biyar nayi ya mike. Bandaki ya shiga ya watsa ruwa sannan ya dauro alwala.

Karatun kur'ani yayi na minti ashirin sannan ya wuce massalaci. Raka'atanil fijir yayi sannan suka tada sallah asuba.

Sai karfe shida ya fito daga masallaci sannan yayo gida.

Yana dawo wa dakin Mami ya shiga. Tana zaune akan sallaya tana jan carbi.

Durkuswa yayi. Ya ce,
"Mami ina kwana."

Mami ta kalle shi cikin kulawa ta amsa,
"Lafiya lou Najib. Ka dawo!"

"Eh Mami."
Ya fada yana shirin Zama.

Kallon sa Mami tayi,
"To tashi kaje ka shirya, kar ka makara bari na shiga kitchen nima."
Ta fada tana Mikewa.

Shima mikewa Yayi, ya ce,
"muje tare."

"Kar ka makara fa."
"Bazan makaraba."

Kitchen suka shiga. Dankalin da ta bayar aka feraye mata shi ta wanke ta bade shi da gishiri ta fara soyawa.

Ruwan tea ya daura wanda ya zuba masa kayan kamshi.

Sai kwai da ya dauko ya fasa. Mami kuma ta miko masa albasar da ta yanka.

Magi ya zuba akai ya soya musu. Tean da ya dafa ya juye afulas. Wani ya dauko ya dibi nashi.

Lokacin Mami ta gama suyar dankali. A fulas ya zuba mata sannan ya juye sauran a wani fulas ya dauko basket ya zuba a ciki.

Tare suka wanke kayan da suka gama amfani dasu. Sannan suka fita dakin Mami yayi wanka ya fito ya shafa mai ya bude doruwar ya dauko wata suit ash colour yasaka ta.

Kansa ya taje, ya shafa masa mai sai kyalli take. Sai bakin takalmi da yasaka.

Mami na zaune tana kallon sa. Sai da ya gama sannan ta dauko turaren ta fesa masa. Sanna ta gyara masa kwalar rigar sa.

Murmushi ya sakar mata. Ya duka ta sumbaci goshin sa.

Sannan ya ce,
"Mami na tafi "

Mami ta ce,
"Muje na rakaka."

Suka fice a daining ya dauki basket din sa da briefcase din sa ya fita.

Yana Fita dan juma ya mike. Yana washe baki.
"Barka da fitowa dan Alhaji."

"Yauwah!"
Ya mika masa hannu sukai musabaha.

Durkusawa yayi yana gaishe da Mami.

Ta amsa masa cikin sakin fuska. Mukullin motar ya amsa, ya tafi ya bude masa.

A sit din gaba ya zuwa abubuwan hannun Sa sannan ya juyo.

Najib ya dubi Mami, ya ce,
"Mami na, sai na dawo."

"Allah kiyaye hanya. Allah bada sa'a!"
"Ameen! Mami nah"

Ya shige motar.

Sai da ta daina hango sa sannan tayi wani part dake gefen can.

Tana shiga wata dattijuwa ta karaso wajen ta.

Murmushi ta sakar mata.






*INDABAWA*

*TNX U ALL*

NAJWA Complete ✔Место, где живут истории. Откройте их для себя