151

793 60 0
                                    

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*151*

Najib dai be samu zuwa ba gaba daya dan har lokacin da zahra ta haifi danta namiji be zo ba. Haka Najwa ta ce zata je, amman ya ce ta bari sai ya dawo.

Najwa baiwar Allah bata nuna damuwa ba. Dan haka sai hakuri ta bawa Zahra, Zahra ta ce, bakomai in sunyi arba'in tazo ta kawo mata Baby.

Bayan shekara daya.

Abubuwa da yawa su  faru a ciki har da shakuwar da Najwa a tayi da mutanen gidan Mami inda take daukar gidan kamar gidan su.

Haka nan Kullum sai sunyi waya da Hamma saalim da Basma. Bata da damuwar komai sai na Najib da take son ya dawo.

Mami ma kuma ba abinda take mata sai kyautata mata tare da gatan ta ta. Dan komai ta samo zatace, Najwa. Komai Najwa

Dan wannan shekarar tare sukaje Umrah da ita da Dady da su Baba. Sai bayan sallah suka dawo.

Gaskiya Najwa ba karamin kyau ta kara ba. Dan hutu ya kara ratsa ta.

**********
Bangaren Najib kuwa sai hakuri da yake da Sumaiyya dan shi, be ga amfanin zuwa da ita ba, ita ba girki ba ita ba gyara ba haka nan sai ya neme ta sau goma befi ta kula shi sau daya ba.

Bai da wani sassauci sai a gun Najwa in sunyi waya. Haka nan Khaleel.

Su Khaleel har Abuja sunje gun Najwa inda sukai kwana biyu shi da Khadiya dan alokacin ma tana da ciki.

Lil N kuwa be manta da Maman sa Najwa ba dan da gydu yayi gun ta duk da ya kara zama saurayi.

Tin last month yake ce mata gasu nan gasu nan har ta gaji da gasu nan.

Kamar ko da yaushe in karshen wata yayi Mami kan dauko musu me gyaran jiki, ai musu lalle in kitso suke so ayi in gyarawa za ayi ayi.

Haka yau ma Mami ta kira da har Najwa ta ce baza tai ba saboda ko da yaushe Najib zai iya cewa zai zo in zai zo tayi.

Sai kawai ta fasa ta sa akai mata. Lalle ja da baki akai mata me kyau kai ka zata amarya ce wacce za ai shagalin bikin ta a satin.

Haka aka gyara mata kai dan Najwa ba ma'abociyar kitso nace, gashin nan ta faka shi a tsakiyar kanta.

Karfe biyu aka gamai mata komai wannan yasa tayi bangaren Najib.

Wanka tayi ta shirya cikin wata farar riga marar hannu, sai dogon wando da ta saka, bata saka dankwali ba, ta feshe jikin ta, bata sallah, wannan yasa ta yi, kan gadon ta, ta fada tana mai yin salati, Number Najib tai ta trying tai kira amman wai akashe.

Abin ya dame ta dan tin jiya da safe rabon da suyi waya dashi. Abinda a rana sayi waya fiye da sau goma sha. Amman kwana daya ba kiran sa.

Addu'a tayi Allah yasa lafiya. Ta gyara kwanciyya. Bata jima da kwanciyya ba bacci ya dauke ta.

Mami ma ana gama mata taje tai wanka ta shirya cikin shigar alfarma.

Bangaren Baba tayi, daii dai shigowar wata katuwar mota gida.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now