166

727 54 0
                                    

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*166*




"Ina ji."
ta fada tana gyara zaman ta.

"Najwa kar ii boye min komai a abinda zan tambaye ki. Dan Allah ki fadan gaskiya."

Gane abinda zai tambaye ta, yasa ta kwanta, ta ce,
"Kaga anjima mayi maganar bacci kaji."

Daga ta yayi, ya kalle ta. Fuska ta marairaice masa.

"Shikenan!"
Ya fada yana kwantar da ita, jijjiga ta yake yana matsa mata jiki har tayi bacci.

Ya jima a dakin yana kallan ta, tabbas Najwa ta gane abinda yake son tambayar ta. Kuma yasan indai Najwa ce to bazata taba fada masa abinda zai tambaye ta ba.

Ta ina zai fara tunanin inda zai gano wanda yai mata wannan abun.

Ya  jima a dakin. kafin ya mike ya fita.

Gida ya koma dan debo wasu takardu, bangaren Najwa yaje yana zaune a falo yana tunanin abinda ya faru.

Kai ya daga ya daura akan jikin kujera kamar ance ya kalli sama, yaga CCTV camera da akan saka masa

Da sauri ya mike har yana tuntube ya shige bangaren sa

Dakin da ya zuba computer da kayan karatun sa ya shiga.

Connecting yayi ya sako abinda ya faru tin daga saka camerar tin daga dakin Sumaiyya.

Da lokacin da ta sha maganin ta na karshe da maganar cire mahaifar ta, da lokacin da ta balli magani ta fita daga bangaren ta, har ya zuwa yau da yagansu da kawayen ta.

Shige da ficen ta duk sai da ya gani, lookacin da baya gidan bata fiya awa biyu a gidan bama.

Ta bangaren Najwa kuwa yana ganin yadda take gudanar da gyaran gida da su karatun alkura'ani.

Duk yana gani wani abin in tayi yayi dariya wani kuma ya kasa magana ma.

Bama in tana zaben kayan da zata saka masa, sai tasa kaya kala nawa kafin ta zabi wanda take so.

Haka wajen kwalliya, in ta gama ta juya can ta juya can ita kadai dai.

Najwa na burge shi matuka. Zuwan Sumaiyya bangaren Najwa ya gani nan da nan ya maida hankalin sa kan naurar.

Tambayar ta abinci da tashin Najwa, daukar Maltinar Najwa da zuva mata wasu kwayoyi duk ya gani.

Hana ta sha da tafiyar ta.
"Innalillahi wainna illahir rajiun."

Kawai Najib yake fada, be taba kawo wa aransa Sumaiyya zata iya abinda ta aikata ba.

Wani iri yanayi ya dinga ji, fadar bacin ran da ya lullube shima bata baki ne.

Rasa me zaiyi yayi, mikewa yayi da sauri, yai waje. Zai shiga bangaren Sumaiyya kenan Dady ya kirasa.

Dauka yayi yana futar da wani irin numfashi.

Dady najin haka ya ce,
"Son lafiya?"

Bai tsaya jin amsar sa ba yace,
"Kaga ka zo yanzun nan ina jiran ka."

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now