154

733 67 0
                                    

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*154*

*Sandaf Aikin ki yana kyau. Allah kara basira da zakin hannu. Allqh ya dafa miki.*

*Ameen!"



Tana sauka kasa, ta saki murmushi tayi wajen kawayen ta

Ta ce,
"Sannun ku da zuwa,"

"Yauwah Hajiya ya gidan ya amaren."
"Lafiya Alhamdulilah. gata can an gama shiru ku take jira kawai."

"Allah sarki su Najwa an zama manya, Allah duk lokacin da zan kai amarya sai na tina lokacin mu. Allah dai ya bada zaman lafiya."
Wata daga cikin kawayen Mami ta fada.

"Ameen!"
Duk kansu suka hada baki suka amsa.

Waya Mami ta daga, ta kira Bara'atu, tana dagawa ta ce,
"Kuna ina ne, ku fito zaku tafi fa."

Ta kashe wayar cikin minti biyu sai gasu nan sunco kwalliya sai kace masu zuwa wajen biki.

Sama sukai, Mami tabi bayan su. Dakin da Najwa take, suka isa, tana zaune a gefen gado ta lula can tunanin Najib.

Suka shigo dakin, buda Talle ta saki,
Ta ce,
"Amarya kinsha Kyau."

Ta fada tana daga mayafin kanta. Hawaye taga yana zarya akan fuskar ta.

Hawayen ta hau goge mata tana bata hakuri.
"Haba Najwa me ne abin kukan ke da zakijr wajen me sonki. Dan Allah ki daina wannan kukan abinda kullum muna tare."

Hawayen idon ta, ta goge jin shigowar Mami, Mami ta kalle su ta ce,
"Mene ne?"

"Ba komai."
Wajen Najwa ta karasa ta dago ta, hawaye ta gani a idon ta, ta ce,
"Haba Najwa mene abin kukan, ki daina kinji kiyi hakuti kije kema kiyi zaman auren ki. Allah bada sa'a da zamna lafiya kinii. In kina da matsala kina fada min kinji."

Kai ta gyada mata,
"Yauwah ko kefa,"
Ta fada tan goge mata hawayen fuskar ta.

Kamo ta tayi suka sauka kasa, Bangaren Baba sukayi, Mami ta ce,
"Baba Najwa tazo miki sallama."

Baba ta ce,
"Masha Allah. To Najwa Allah bada sa'a ayi hakuri dan aure dan hakuri ne. Allah miki Albarka. Allah bada zaman lafiya."

Mqmi ce ke amsawa da
"Ameen Ameen."

Daga nan ta fito da ita kawayen Mami suka tafi kai ta gidan ta.

Najib na can Hankalin sa gaba daya yana wajen Najwa, sam yau be samu zama da ita ba.

Lallai ya yadda Najwa ta zama farin cikin sa, dan yau wani iri yake ji, haka nan duk kewar ta, ta dame shi.

Allah Allah yake ya gama da Sumaiyya ta tafi yayo gida. Yana gamawa da ita kuma Dady ya kirasa akan yaje.

Zancen tafiyar su Honeymoon ne, amman sai nan da wata biyu, saboda be dde da dawowa ba, ya kamara yaje asibitin su yaga me yake faruwa bayan tafiyar sa.

Ba samu famar komawa gida ba sai bayan magariba lokacin an tafi da Najwa.

Yana zuwa ya fara leken da ya fara, Mami na kallon sa tai masa banza.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now