150

825 52 0
                                    

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*150*

*Ummulkhairi* kema kina son littafin nan nagode sosai da kulawar ku.


Karfe sha daya suka fito daga wajen bikin. Khaleel ya kalla ya ce,
"Muje mu ajiye ka. A gida ne?"

"Ina zakaje kai."
"No wai kar mu takura maka."

"Haka ne amman ai ma kai mu airport ko?"
"Kuma fa haka ne. Muje gida na dauko kaya na."

"Toh!"
Ya fada, suka dau hanyar gida, Najwa na zaune tayi shiru, dan Mamin ta, ta fada mata a gidan Mamin Najib zata zauna kafin su dawo.

Kanta jingina a jikin kujera. Kallon sa ya maida kanta.

Hannun ta ya kamo ya rike yana matsa shi,
"Baby!"

Kallon sa tayi, tai masa murmushi, idon ta ya canja kala. Ta kuma yin sanyi da ita.

"Baby kiyi hakuri, ban san ya zanyi bane, naso na tafi dake amman Mami taki yadda saboda abinda Sumaiyya ta hada mata karya da gaskiya. Kiyi hakuri bazan dade ba zan dawo, saboda ke. Kiyi hakuri kinji."

Ya fada murya a sanyaye. Kallon sa tayi ta girgiza kai, ta ce
"Haba Hamma me kake fadi haka, kadaina bani hakuri dan ba abinda kai min. Ka kwantar da hankalin ka, ka je ka dawo lafiya kaji. Kada kasa damuwa a kai na. Ina nan ina jiran dawowar ka."
ta kara sa fada tana kama hannun sa."

Jawo ta yayi, jikin sa yana me kwantar da kanta a jikin sa,
"Ina son ki Najwa. Ina sonki. Allah ya barmin ke. Allah ya barmin ke. Kice farin cikina, kece ruhina. Ina kaunar ki Najwa."

Ya dago kanta yana me kare mata kallo, bakin su ya hade waje daya yana kissing din ta.

Najwa kuwa tini jikin ta yayi sanyi, in banda rawa ba abinda jikin ta keyi dan yana karbar sakon da be saba karba ba.

Yafi minti Goma yana kissing nata, hannun sa ya saka ta cikin rigar ta, wannan ya dawo da hankalin ta jikinnta.

Taso ta cire hannun, amman yace,
"Dan Allah Najwa kada kimin haka, ki barni daga yau sai wani lokacin in ina raye fa."

Hannun sa ta saka wanda ta rike, abinda yake yi ya cigaba dayi, har sai da ya samu nutsuwa sannan ya sake ta yana rumgumeta tsam a jikin ta.

Sai da suka dau mintina a haka sannan ya gane ashe sun jima da zuwa gida har Khaleel ya fita.

Kanta ya dago mata dashi, ya ce,
"Ina zuwa kinji."

Ya saukar da ita daga kan cinyar sa. Ya bude ya fita.

Akwatin sa ya dauko ya saka a boot sannan ya koma cikin gidan.

Najwa kuwa kai ta jingina a jikin kujera tare da lumshe idon ta.

Yana shiga bangaren  Sumaiyya tana zaune ta zuba uban tagumi. Tsugunawa yayi, ya ce,
"Lafiya uwar gida na."

Dagowa tayi, kamar zatai kuka sai kuma ta share ta ce,
"Ba komai. menene?"

"Ba komai tare muke da Najwa na ce ki fito muje mu kaita wajen Mami sai mu zarce airport."

Kai ta girgiza ta ce,
"A'ah kuje zan sa driver ya kawo ni."

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now