133

582 53 0
                                    

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE
*133*

*UMMU AFFAN MY KAWALLI. REALLY LOVE U. TNC FOR UR CARING ND LOVE. ALLAH KARA MANA ZUMUNCI YA BARMU TARE. AMEEN*




Ita tsoro ma takeji gaba daya. Dan Najib yadda yake son kasancewa tare da ita tasan bazai taba daga mata kafa ba.

Gashi taji ana yawan fadar First Night akwai wahala. Wata faduwar gaban ta karaji.

Juyi tayi, tana tina yadda take da raki ciwo kadan tai masa kuka, bata son komai ya taba ta.

Ba abinda ta kuma tinowa sa lokacin da cinnaka ya cije ta a makaranta ta saka kuka ita ce har clinic.

Bare kuma first night. Bata taba mantawa wani littafi da Zahra ta karanta take bata labaton yadda amaryar ta sha jiki, wai jar da su dinki.

Idon ta, ta bude ea sauri wanda suka rine sukai jajie dasu alama ta jin tsoro.

Lumshe su ta kuma yi, a ranta kuma tana cewa,
"Ai kowa da haka ya saba. Da kuma haka duk aka same mu. Abinda baya kisa a da sauki."

Ta fadi hakan ne dan kawai ta bawa zuciyar ta hakuri.

Wani tunanin ya kuma fado mata, tab kuma ace da safe da wane ido  zaka kalli mijin.

Tab ai shikenan kuma, kullum idon mutum a rufe zasu kasance.
Zahra ta tuna, wacce ko a washe gari ma sai nan nan take da Mustaphan ta.

"Tab!"
Ta fada a fili, tana mikewa zaune.

Kayan jikin ta, ta cire ta shiga bandaki tayo wanka.

Kayan baccin ta, ta saka, ta dauki hijab ta zira ta nufi kitchen dan taji tana jin yunwa.

Cake ta dauko ta lemo, tayo Falo, su Ummah suna zaune suna hira.

Sai da taci ta koshi ta dauke kayab da tayi amfani dasu sannan ta yi musu sai da safe.

Har ta juya Baffah ya kira ta. Komawa tayi ta zauna a gefen kafar sa.
"Najwa!"

Ya kira sunan ta, amsawa tayi da
"Na'am."

"Allah yayi miki albarka. Allah ya baki zuri'a ta gari."

"Ameen Baffah."
"Najwa ki rike Najib hannu biyu dan Najib mijin aure ne. Kinji."

Kai ta gyada masa,
"Shikenan dauki kayan da ya kawo miki kije ki gani kema."

"Toh Baffah nagose Allah daxa girma da lafiya."
"Ameen Najwa."

Kayan ta dauka, tayi musu sai da safe.

A kan gado ta juye kayan, wasu hadaddun Dogayen riguna ne, sai riga da siket da mayafai masu kyau.

Hadi da jaka da takalma masu kyau dasu. Sai turare kala biyar duk masu kamsgi da tsada.

Kai ta girgiza, ta ce,
"Hamma badai son wahala ba. Nagode Allah kara budi."

Kayan ta mayar cikin leda ta saka a durowar Ummah.

Alwala tayi ta kwanta, lokacin karge sha dayan dare.

Wayat ta, taji tana kara, dubawa tayi, murmushi taui ta dauka da sallama.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now