157

746 55 0
                                    

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*157*



*Basira Sabo* jinjina gareki. Allah kara basira da zakin hannu.
*Ameen!"

Nagaishe ki.





Wai ina Sumaiyya ne.

Tinda Sumaiyya ta isa Kano take neman Antyn ta wacce bata gari, duk neman da tai mata a waya bata same ta ba.

Bata tashi samu  ta ba sai da tai sati biyu a kano sannan a lokacin Antyn ta ta ce, ai bata kasar amman zata dawo nan da sati biyu duk abinda ya kamata

Sosai Sumaiyya tai murna. Kullum kafar ta a waje yawo kamar ba matar aure ba.

Duk fadan da Mama take bata ji, kawayen ta kuwa duk sun kara junewa.

Dan har hotel rake binsu, ita bata ganin aibun su ma yanzu.

Abu daya shi ya fi damun ta shine ta raba Najib da Najwa.

Bata da buri da ya wuce wannan dan ita ce daga gun wancan malamin sai gun waccan malamin.

Kowa da abinda zai fada mata ba gaibu dan da akwai wanda ya ce, kafin ta koma auren zai mutu.

Amman komai aka fada mata shiru baya faruwa.

Duk ta daga hankalin ta, ta rame tayi baki, bata samun kwanciyar hankali.

Mama kuwa ba abinda take sai addu'a da take mata.

Sam bata kiran sa, sai dai in ya kira ta.

Duk kudin da ya bata sun kare a bin malamai, wannan yasa tai sa Najib ya kara turo mata kudi.

Be tambaye ta abinda zatai da su ba kawai ya tura mata.

Amman suma cikin sati  sai da ta gigita su.

Kawar ta daya ke mata fada ta nuna mata ta daina abinda take sannan ta bar Najib da Najwa.

Amman sam taki ji abinda yasa ta daina zuwa gun Hauwan ma kenan.

Dan wai da taje zata fara gaya mata Allah yace Annabi ya ce. Ita kuma abinda ta tsana kenan.

Yau tana zaune a gida sai kawai tajoyi sallamar Anty kaltum.

Da sauri ta mike ta taro ta ta a murnar dawowar ta

Mama bata nan dan haka a falo suka zauna.

Anty Kaltum ta ce,
"Sumaiyya ya na ganki haka duk kin rame sai kace ba Summy gaye ba."

"Uhmm kedai bari Anty. Dan Allah ji yadda kika kara haske da kiba har wani ja kike. Mene sirrin ne."

"Sirrin zawarci. Ba abinda yafi zawarci dadi yarinya. Kinga da Alhj lukuman fa muka dawo  jiya. Kudi sai dai na diba abinci sai wanda zanci mota sai wacce nake son haka. Ba ruwana da bacin rai bare nasa damuwa a rai na."

Kallo ta Sumaiyya take, ta ce,
"Anty wai ya zamuyi ne da wannan shegiyar Najwan. Anty kinga inda Najwa ta koma kuwa."

"Kinga ki kwantar da hankalin ki, kafin na dawo na kira wani malamina dake madobi, mu yake jira kawai  tashi muje."

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now