165

710 51 0
                                    

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*165*




Magariba da tayi ne yasa ba a tafi kai Najwa ba.

An ajiye ta a dakin Mami, inda dakin yake a ciki da yan uwan Mamin ta, da yan uwan Dadyn ta.

Duk addu'a suke mata, Najwa na kwance cikin sitirar ta.

Kuka kuwa gidan duk a rikice yake. Mamin Najwa sam bata zo ba.

Ta ce,
"Da zuwana da ba zuwana duk daya ne, addu'a ce dai kuma bakina bazai taba daina yiwa Najwa addu'ar samun Rahama ba."

Mami dake gefen Najwa ta zuba mata ido taga kamar likafanin na motsi,

Bude fuskar Najwa tayi, ji tayi, tana cewa,
"Hamma! Hamma!"

da sauri Mami ta kalli jama'ar dakin tana cewa,
"Najwa bata mutu ba."

Da sauri jama'ar dakin suka yo kan ta, Kuje ku kira min driver.

Mami ta fada tana dauko wani katon hijab.

Najwa ta sakawa sannan ta kira Dady da kansa yazo ya dauke ta suka yi asibiti.

Suna zuwa aka amshe ta aka yi office din Najib inda ake duba ta.

Ruwa suka jona mata, Dr Farouk kuwa sai Hamdala yake ga Allah da yasa Najwa bata mutu ba.

Cikin ikon Allah wajen karfe Dayan dare sai ga Najwa ta bude ido, Mami ta gani zaune a gefen ta.

Mami ta kalla, ta ce,
"Mami, ina Hamma?"

"Sannu Najwa, sannu kin tashi?"
Ta danna bell da sauri Dr Farouk ya shigo, dudubata yayi, ya ce,
"Alhamdulilah! a samu a gasa mata jiki sai a bata ruwan zafi ta sha."

Mami da kanta ta hada mata ruwan wanka, wanda Najwa kasa tafiya ma tayi sai a kujera aka daurata aka kai ta ban daki.

Mami da kanta ta gasa mata jiki, suka fito ta canja mata kaya sannan Dady ya tayata daura ta akan gado.

Duk abinda Likita ya ce ai mata sukai masa.

Sai dai duk yadda ta motsa jikin ta sai ta ce,
"Wash!"

Mami sai sannu take mata, ai dole jiki yai ciwo ace kana kwance kwana da kwanaki.

Mami tausayin Najwa take dan har hawaye sai da ta zubar mata.

Najwa ta rame sosai, tayi haske idon ta duk sun zurma.

Allura aka karai min na koma bacci.

Da safe ina tashi Mami ta karai min wanka ta gasa min jiki, Dr Farouk ne ya bata wani magani ta shafa min a jiki na.

Ruwan Zafi kadai ake bani tin daren jiya.

Ganin har lokacin Hamma Najib be zo ba yasa Najwa mamakin ina yake, ko tsoron ta yake ji ne?

Kasa daurewa Nayi na kalli agogon office din, karfe Takwas da rabi, amman har yanzu ba Hamma wanda duk jama'ar da suka zo ta'aziyya ta kowa yazo yai min sannu.

Har su Mami nah duk sun kira suna min sannu, Basma kuwa ai sai murna Addu'ar ta bata mutu ba.

Ina kwance ina tunanin Hamma, abin na damuna na rashin ganin sa.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now