122

549 57 0
                                    

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH
*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *122*


*Kuyi hakuri kwana biyu page daya nake turowa. Wamnan yasamu ne saboda bana samun lokaci ssai.*

*Anayin maneji*

*Masoya littafin  nan. Naga sako nagode. Allaah barmu tare*

Ranar sai dare suka bar gidan.

Mami kuwa sai nan nan take da ita.

Ko da yaje Kano damuwar rashin ganin ta bata bar shi ya sake ba.

Dan duk a matse ya ke. yaje gidan Khaleel inda kulawar da yaga Khadija na bashi ba karamin burge shi tayi ba.

Duk da tana da ciki bata da kasala da kwiya. dan gidan tsab dashi abin sha'awa sai tashin kamshi yake.

Yana zuwa aka tare shi da abinci me rai da lafiya ga hadin lemo.

Sosai yaci abincin dan Najib baya wasa da cikin sa.

Ba yadda Khaleel beyi dashi ya kwana a gidan ba yaki.

Zuwan sa Kano yayi ziyara yan uwan da kakanin sa. Inda suke ta masa tsiya be kawo amaryar sa ba.

Wanda ya dade be ganshi bama wannan karan yaje ya yi musu abin arziki.

Ana jibi zai dawo ya fadawa Mami, Mami ganin yar aikin da zata kaiwa Sumaiyya bata zo ba. Tasa su Najwa suka tattara suka tafi gidan Summy dan su taya ta tarbar me gida.

Tunda suka je take cika tana batsewa su kuwa ko ta kanta basu bi ba.

Inda sai hirar su suke, su dafa abinda suke so, su sha abinda suke so.

Duk da abin na mata zafi amman tasan baza ta iya hanasu ba.

Ranar da zai dawo ba ta tashi a bacci ba ma sai karfe Ukun rana.

Lokacin sun gyare gidan tsab sun turare shi.

Najwa da Zahra ne suka gyara bangaren Najib.

Inda suka ce Najwa ita zata Masa girki. Fried rice tayi da hadin salad sai waina masa da yake su Bara'atu su  fada mata yana son ta.

Sai farfesun kayan ciki da tayi masa da hadin lemoka da kunun aya.

Kafin magariba sun gama komai gida sai tashin amshi yake.

Sun shirya zasu tafi Najwa tayi bangaren sa ta hada masa ruwan wanka dan tasan i yanzu dai yana hanya.

Tana dawowa suka shige mota. Jeep ce wannan yasa Najwa ta shige can baya, su kuma suka zauna a tsakiya.

Har an bude musu gate zasu fita ya danno hancin motar sa cikin gidan.

Tsayawa Drivern su yayi har sai da ya fito suka gaisa.

Karasowa yayi wajen motar yana leka kansa ta taga.

Bara'atu ce ta ce,
"Sannu da zuwa Yaya. Ya hanya?"

"Lafiya ya amsa mata da. Gaisar dashi sukai gaba dayan su.

Sai da suka gama sannan Najwa ta ce,
"Ina yini Hamma Najib?"

Tsigar jikin sa ce ta mike, jin muryar ta me dadi da sanyi ta doke shi.

Amsawa yayi yana son ganin fuskar ta. Duk da yaso yasan muryar tata.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now