114

533 49 0
                                    

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHODA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *114*

Summy kuwa tana can tana zuba ido taga kiran sa amman shiru kake ji.

Bayan kwana biyu ta shirya ta tafi gidan amarya Hauwa.

Hauwa ba karamin jin dadin zuwan ta tayi ba.

Nan ta tare ta da kayan motsa baki da abincicika.

Summy kuwa wannan abin ba karamin burgeta yayi ba, hakan ya kara mata kwadayin auren mutum me kudi.

Sun sha hira, inda anan take bata labarin Najib da yadda suke ciki.

Hauwa ta jinjina kawai wai da Najib yace yana son Summy dan tasan halin sa sosai.

"Summy Kuma Najib din ne yace yana sonki."
Ta fada cikin mamaki.

"Eh shine, menene?"
Summy ta fada.

"A'ah babu komai. Summy in kika samu Najin kin huta, amma ina mamakin yadda ya ce yana son ki bayan shi baya kula yan mata."

"Haka ne Hauwa, Khaleel ya fadan komai, yanzun ma ya kasa sakewa dani sosai."

"Sai kinyi hakuri, sannnan sai kin canja hali da Najib akwai shi da son girki da tsabta."

Hararar Hauwa tayi ta ce,
"Ni ban da su ko?"

"A'ah nufina ki kara dagewa kisan wanda zaki aura. Dan nason ki da son jiki."

Haka suka dinga hira Hauwa na yiwa Summy nasiha.

kafin magariba ta mike ta ce zata tafi. Ba karamin mamaki abin ya bawa Hauwa ba dan tasan kawar ta,, bata fita in ba dare ba dan tana cewa da dare anfi yin babbar harka.

"Kallon fa?"
Summy ta tambayi Hauwa

Murmushi hauwa tayi ta ce,
"Summy kin canja fa."

Dariya Sumaiyya tayi ta ce,
"Dame fa?"

"Da na san ki da son fitar dare saboda ki samu saurayi, kuma kin fi jin ddi a lokacin amman yanzu kince zaki tafi ko da inda zaki biya ne."

Murmushi Summy tayi ta girgiza kai. Ta ce,
"Hauwa wallahi aure nake bukata ne yanzu, kuma na samu a hannu me zan tsaya kulawa a mayaudaran mazan nan. Yan sukai su baro ka."

Baki Hauwa ta saka tana kallon Summaiya cike da mamaki. Yadda take fado wadan nan magan ganun.

"Kuma yanzu Mama tana fadan kaiwa dare."
Sumaiyya ta fada.

"Gaskiya ne gara mubi iyayen mu, dan in sukace A'ah, ka 'kiji to zakayi gamu da ba dai dai ba."

"Wallahi kuwa!'
Sumaiyya ta fada tana mikewa."

"Ina zuwa."
Hauwa ta fada tana shiga dakin baccin su.

Minti kadannta fito rike da leda a hannun ta, hannu Sumaiyya ta kamo tana damka mata, tare da jan ta waje.

Drivern gidan ta kira dan ya mika Sumaiyya gida.

Godiya Sumaiyya tayi mata sanna sukai sallama ta shiga mota yaja suka tafi.

Kamar ko da yaushe Mami ce zaune sai Najwa da Basma dake gefen ta.

Duk lokacin dasu Najwa suke zauna da Mami mami bata barin lokacin ya kare a banza.

Sai ta san tambayoyin da tayi musu dan daduwar su. yanzu ma haka ce ta faru.

Najwa ta kalla ta ce,
"Najwa, kiyi min bayani game da sallah baki dayan ta da farillan ta mustahabai da sauran su"

"To Mami
FARILLAN SALLAH sun kasu ne gida 2:
1. Sharuddan Sallah
2. Rukunan Sallah

Kuma akwai bambanci tsakanin Sharadi da kuma Rukuni. Sharadi ana samunsane kafin a shiga cikin ibada, shi kuma Rukuni ana samunsane a cikin ibadar, kuma dole sai kowanne yasamu sannan ibada take cika.

SHARUDDAN SALLAH
1. Muslunci
2. Hankali
3. Balaga
4. Tsarkin kari
5. Tsarkin dauda
6. Shigowar lokacin sallah
7. Suturce al-aura
8. Fuskantar alqibla.

Kuma gabadayan Malamai sun yi IJAMA'I akansu, sai dai Malamai sun yi sabani akan cewa shin NIYYA da KABBARAR-HARAMA su ma sharadi ne ko kuma ba SHARADI ba ne?

RUKUNAN SALLAH
1.Tsayuwa
2. Ruku'i
3. Sujjada
4. Zaman karshe.
5. Daidaituwa acikin Ruku'i
6. Zaman da'akeyi tsakanin sujjada guda 2
7. Tahiyar karshe
8. Salati ga Annabi(ﷺ)
9. Sallama.

*FARILLAN SALLAH*
1. Niyya
2. Kabbarar harama
3. Tsayuwa dominta
4. Karatun fatiha
5. Tsayuwa dominsa
6. Ruku'i
7. Dagowa daga ruku'i
8. Sujjada
9. Dagowa daga sujjada
10. Jeranta tsakanin farillai
11. Nutsuwa
12. Daidaituwa
13. Sallama
14. Zaman karshe wanda za'ayi sallama acikinsa
15. Kulla niyyar koyi da liman,*

*SUNNONIN SALLAH*
1. Karatun Sura
2. Boye karatu
3. Bayyana karatu
4. Kowacce kabbara in banda ta farko
5. Sami'Allahu liman hamidahu
6. Zaman tahiya na farko
7. Karin addu'a a zaman tahiya na 2
8. Sanya sutura a gaban mai sallah

Saidai kuma Malamai sun yi sabani dangane da zaman tahiya, akwai Malaman da suka ce zaman tahiya dukansa farilla ne, to amma mafi rinjayen Malamai sun tafi ne akan cewa zaman tahiya na farko SUNNA NE, amma zama na biyu FARILLA NE.

*ABUBUWAN DAKE BATA SALLAH*
1. Rashin yin niyya
2. Yin dariya a cikin Sallah
3. Wasa mai yawa a.

"Masha Allah! Najwa nasan kin sani. Sai dai ina son na kara gwada basirar ki. Bama yanzu da kike daukar kananun yara karatu ya kamata kina sanar dasu dukan wadan nan."

"Mami Nagode, dan wani abun da kin tambayen anan na baki amsa, sai kiga washe gari an min tambaya, ina jin dadin gwajin da kike min. Dan in ban san abu ba kina dada tada ni."

"Ba komai *Najwah* kema ina son ki kula da ilimin ya'yan ki bama na addini dan neman dace duniya da lahira."

"Insha Allahu Mami."
"Yauwah Dadyn ki ya ce, jibi zakije Abuja da kin dawo sai tafiya."

Kai tayi kasa da shi, Ta ce,
"Allah ya kai mu."

"Ameen!"



*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now