26-30

957 82 0
                                    

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*


🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾




Page *26-30*


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

LOVE U







Najib ne ya bude mata mazaunin gaba ya rufe ya koma mazaunin driver

Sai addu'a suke musu ta zuwa da dawo wa lafiya.

Driver sune ya karaso, ya ce,
"Hajiya tafiyar ce!'

"Eh wallahi. Ga wannan kaima."

Karba yayi, yana mata addu'a,
"Nagode Allah saka da alheri Allah tsare."

"Ameen! Wannan
Mami ta ce ka bawa yaron can me shara."

Ta bashi wasi kufin.
"To Allah kiyaye hanya."

"Ameen""
Najib yaja motar suna dago musu hannu.

Wajen me gadi suka nufa. Shima kudi ta bashi ya dinga musu godiya da addu'ar zuwa da dawo wa lafiya.

Sannan suka dau hanya. Suna tafe suna hira abin su.

A kaduna suka yada zango gidan wata kawar Mami. Anan suka ci abinci sukai sallah sanna suka dau hanya.

Bayan la'asar suka isa saboda ba gudu yake ba gashi sun tsaya a kaduna.

Nasarawa GRA Suka tafi can gidan su. Yana yin horn me gadi ya bude.

yana ta fara'a dan yasan yau akwai gara da zasu kai gida.

Gida ne kato dan ko harabar gidan zaici motoci shida, Sai katon mension sai wani bangaren me kyau daga gefe.

Shi ya fito ya budewa Mami kofa, ma'aikatan gidan ne suka nufo su kowa da fara'a akan fuskar sa.

Suka hau yi musu
"Barkan ku da zuwa."

Su Mami na amsawa, da
"Yauwah!"

Nan suka fara gaishe gaishe. Sai da kyar Mami ta samu tayi cikin gida.

Katon Falo ne, sai matatakalar bene. falon an cika shi da kujeru. Daga gefe wani daki ne da kitchen.

Sama kuma dakunan bacci ne guda uku. Gidan tsab dashi dan duk da basa nan akwai masu kula da gidan.

Sama suka haye kowa ya shige dakin sa.

Wanka suka shige kowa ya gasa jikinsa. Sannan sukayo alwala sukai sallah.

Dakin Mami ya isa. Ya ce,
"Mami sannu ya gajiya."

"Gakiya akwai ta."

Fuska ya dan bata, na rashin jin dadi. Ya ce,
"Ayya sannu bari na kawo miki magani."

Fita yayi daga dakin. Bai jima ba ya dawo ya kawo mata maganin.

Karba tayi ta sha ta kwanta. Kasa ya sauka. Ya dan zaga gidan.

Ana yin magariba ya tafi massalaci bai dawo ba sai isha'i da leda a hannu ya shigo.

Dakin Mami ya shige,
"Son ka dawo."

Najib cikin fara'a da kulawa, ya ce,
"Eh ya jikin?"

"Gajiya ta tafi."
"Masha Allah sannu."

Ya mike ya fita. Kitchen yaje ya dauko, plate da kofuna da kemo.

Dakin ya dawo ya bude ledar da ya shigo da ita.

Gasasun nama kaza ne, sai hadin dankali a gefe juye musu yayi ya zuba musu lemo.

Suka fara ci. Karfe goma Mami ta canja kaya ta kwanta.

Kafar ta ya dan matsa mata sanna yai mata sai da safe.

Dakin sa yaje yai wanka yayo ya kwanta.

Karfe biyar ya mike, wanka yayo sannan ya fito.

Dakin Mami ya wuce! Ya same ta akan sallaya tana lazimi. Juyawa yayi ya wuce massalaci acan yai karatun sa.

Bai dawo ba sai karfe shida.

Yana dawowa dakin Mami ya shige, tana zaune akan sallaya ya same ta.

"Barka da safiya Mami da fatan kin tashi lafiya."

"Lafiya ka tashi lafiya? "
"Lafiya Alahamdulilah "

Ya mike ya hau kan gadon ta ya kwanta.

Bacci ne ya dauke shi bai farka ba sai karfe goma na safe.

Lokacin har Mami ta gyara gidan ta hada musu abin kari. tayi wanka ta shirya cikin, wata super holland Ruwan omo da ja da baki.

Sai bakin mayafi da jaka dake gefen ta.

Mikewa yayi zaune. Yana salatin annabi.

"Mami har kin shirya."
"Eh! tashi kaje kayi wanka."

Ta fada tana fita a dakin.

Mikewa yayi ya gyara gadon ya share sannan ya fada ban dakin, dakkin Mamin.

Wanka yayi ya fito ya tsane jikin sa, sannan ya shafe jikin sa da mai.

Sannan ya dauko turare me mai ya shafe jikin sa. Wani man gashi ya dauko, ya murj'e gashin sa ya taje shi sai sheki yake.

Sure ya dauka ya saka a hammatar sa sanna ya dauki body spray ya bade jikin sa.

Kwalkwale kwalekwale dai sai kace mace haka ya dinga yi.

Durowar Mami ya mike ya nufa, wani Ruwan kwan boyel ya dauko, bude su yayi ya saka a jikin sa. Sannan ya fesge jikin kin sa da turaruka masu kamshi.

Dai dai lokacin Mami ta shigo dakin. Rike da faranti, Kallo ta bishi dashi.

Murmushi ya saki, ya karasa wajen ta. Ya amshi farantin.

"Mami ko ki tashen na taya ki."
"Ai nasan ka gaji ne."

"Kema kin gaji ai."
"A'ah ni kam gajiya tatafi."

Kofin nan kan farantin ya dauka ya fara hada musu tea, sannan ya budw fulas din.

Potatoe Ball, mami tayi musu, sai faefesun kayan ciki. Sai kamshi ne ke tashi.


*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Onde as histórias ganham vida. Descobre agora