167

743 54 0
                                    

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page *167*






Cikin falon ya koma yana kallon Mami.
"Kazo Dadyn ka na son ganin ka."

Ta juya, bayan ta yabi. Dady ma zaune a dakin sa Najib ya shiga.

A gefen sa ya zauna, ya dukar da kai ya ce,
"Dady gani."

Kallon sa Dady yayi ya ce,
"Me kayiwa Sumaiyya jiya?"

Dagowa yayi ya kalli Dady, sannan yai kasa da kai, ya ce,
"Bam mata komai ba."

"To shikenan kar kai mata komai ka barta da Allah."
Kai Najib ya girgiza ya ce,

"Dady ba irin su Sumaiyya ake bari da Allah ba, Dady niyyar kisa fa tayi, tayaya zan cigaba da zama da ita na tabbata wata rana ni zata so kashewa. Ko ya'ya na."

Mikewa yayi ya sauka, ya bar mahaifin nashi.

Wajen ginin da yasa a ke masa ya nufa ya ce, yana son a tada ginin a gama nan ba dadewa ba.

Shifa sam bazai iya cigaba da zama a gidan can ba.

Najwa kuwa tana zuwa gun Baba suka zauna hira ita da Su Bara'atu.

Anan ta yini dan sunyi dan malele ta zauna suka ci suka koshi.

Sai la'asar ta koma bangaren Mami. Mami ce zaune kadai a falo.

Gefen ta ta zaune wajen kafufun ta.,   ta ce,
"Mami sannu!"

"Yauwah Najwa."
Kallo suke babu wanda ya kuma magana a cikinsu.

Can Mami ta ce,
"Najwa komai ya zama ready gobe sai gaban Mami ko?"

Fuska ta rufe tana gyada kai,
"to ga kaya can a daki inji Dady ya ce, ki bawa wanda kika ga ya cancan ta, sannan ga dubu dari can ya ce, inda abinda zakiyi da su."

"To Mami nagode Allah saka da alheri Allah dara girma da arziki."
"Ameen Najwa Allah miki albarka ya baki zuri'a ta gari."

Tashi tayi da sauri ta abar dakin, Mami kuwa murmushi tayi.

Najwa dai har tai bacci ranar bata ga Najib ba. Kuma ta kira wayar sa duk a kashe. Da kyar ta iya bacci.

Washe gari kamar yadda ta saaba komai haka ta kimsa, kayan da Najib ya debo mata su ta hada a akwati ta saka da kayan da Mami ta bata, atamfofi ne turmi ashirin da yadika sai kudin gun Dady.

Har lokacin in ta kira wayar sa a kashe take.

Wata zuciyar ta ce,
"Kila yana gun Sumaiyya."

Wanna yasa ta fita falo ta sha tea kawai ta koma saama ta kwanta da tunanin Najib a ran ta.

Wajen karfe goma tana kwance sai gashi ya shigo.

Gun ta ya karaso ya dago ta yana kallon ta.

Kuka ta saka masa, ta ce,
"Hamma ina ka tafi ka barni ina ta neman ka wayar ka ma duk a akashe."

Lallashin ta ya fara, yana cewa,
"Kiyi hakuri Baby na. Aiki ne yai min yawa amman kina rai na."

Jikin ta ta kwace daga gare shi, ta ce,
"Kaje na barwa Aikin kai."

NAJWA Complete ✔Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin