51-55

814 62 0
                                    

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻


DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

PAGE *51-55*

Rumanat, ta dan kara matsawa kusa da shi, ta ce,
"Kai man"

Kallon ta yayi daga sama zuwa kasa sannan ya kawar da kansa, dan sam bata burgeshi ba. Sannan ya ce,

"Allah ya kiyaye ni da hada hanya dake, yanzu ma kula kin da nake Allah ya yafe kin,"

kallon sa ta tsaya yi,
"Wai ke tayaya kike zaton ma zan so ki, ai baki da abinda zan so ki, ni ba irin ki nake nema ba, mace ta gari me hankali, ilimi,  da tarbiyya ita nake so. Duk namiji me hankali, ilimi da yasan abinda yake bazai taba tunkarar ki da batun aure ba. Sai dai in Allah ya jarabce shi."

Murya ya sasauta ya cigana da magana,
"Rumanat! Ki nutsu kisan abinda kuke ba dai dai bane kuma Allah zai kama mu in har muka kauce hanya."

"Ki tuba, ki koma ga Allah.  Allah gafuri Rahim ne, kinji. Duk lokacin da ka aikata abu ka tuba Allah zai yafe maka ne."

Baki ta tabe, ta ce,
"Naji, amman please, Najib kasan abin yi dani kaji."

"Rumanat gaskiya in har na amince miki ma to karya zan miki kuma kin san ba kyau karya, kiyi hakuri Allah zai kawo miki wanda ya fini."

Ta wani shagwabe tana jijiga jiki duk dan ta dauki hankalin sa ta ce,
"Haba Najib!"

Tayi maganar tana yin wajen sa kamar zata shige jikin sa.

Ture ya yayi ta fadi kasa. A ransa yana mamakin yaribyar duk abibda ya fada mata bama ta ji ba kenan.

Kallon ta yayi, ya ce,
"Wai bama kiji duk abinda na fada kenan, kike neman kusantar ni da ba muharamin ki ba."

Bene ya haye, dakin sa ya shiga ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin, ruwan kasan wando, da ruwan madarar riga me dogon hannu.

Sosai yayi kyau, sai tashin kamshi yake, sandal din brown takalmi ya saka.

Tabarau ya dauka me garai garai a idon sa, sai agogon azurfa da ya saka a hannun sa.

Yana yarda ita, bayan ya haye sama. ta fashe da kuka ta mike ta fita, gun motar ta ta nufa ta fice a guje daga gidan.

Ko da ya sauko, ba kowa a falon! Murmushi yayi ya wuce can bayan gida inda yasan Mami na zama.

Tana zaune gaban ta lemo, sai wayar ta da take dannawa, gefen ta Baba Tani ce zaune.

Da fara'a ya karasa wajen ta, sai da ya gaida Baba Tani sannan ya juya ga Mami.

"Mami ni zan je wajen Khaleel."
"Ina Rumanat da zaka fita ka barta."

"Mami yanzu dan Rumanat tazo sai naki fita."
"Eh maza koma."

Kansa ya dan sosa, ya ce,
"To ni ban ganta a falo ba."

"What! (Me) me kayi mata?"

Mami ta tambaya. Cikin tsawa da firgita. Dan tasan watakila wani abu yayi mata.

"Me zan mata kuwa."
"Najib!"

Najib ya kalle ta, cikin yanayi na tausayi, ya ce,
"Na'am!"

Mami ta kuma tambayar sa, cikin yanayin na ba wasa
"Me kayi mata?"

Fuska ya bata ganin akan waccan yarinyar Mami na son bata ranta.ya ce,
"Mami Yarinyar ce bata da kamun kai, wai taba ni fa zatayi, shine na ture ta na haye sama."

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now