31-35

916 81 0
                                    

NAJWA*
.

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

Na gaidaku Allah kara mana hakuri da juriya Ameen.


*31-35*

Dedicated *Rashida A Kardam*
*Aunty Rash*

Suna gamawa, Mami ta mike, ta dauko jakar ta. Najin ya dauki Kayan da sukayi amfani dasu ya fitar.

Ya dawo falo, inda Mami take. Ta ce,
"Yaro, dankali buhu nawa aka kawo ne?""

"Mami buhu takwas ne sai doya kwarya hudu,"

"A saka buhu hudu da doya kwarya biyu a mota, akai dankali buhu biyu da doya karya daya wajen Baffa, haka ma Abbah, nasan zasu sallami masu aiki a ciki."

"Toh Mami."
"Yauwah buhu daya a rabawa masu aikin mu, dayan kuma a diba akaiwa, su Uncle Marzuk da Uncle Adana, da Uncle Ahmad da Uncle Usman a aika musu da doya da atamfo fi kowa turmi uku uku."

"Toh! Mami,"
"Je ka hadawa Salau driver ya ka kai. Kazo mu tafi."

"Toh!"
Ya fada ya fice,

Ban garen me gadi, ya nufa da fara'ar sa. Ya gaida Baba me gadi.
"Baba ina kwana?"

"Lafiya lou. Kun tashi lafiya?"
"Lafiya Alahamdulilah."

"Baba ina Salau kuwa?"
"Yana can bayan gida."

Ya mike ya ce,
"Bari na kira shi."

"A'ah! Baba,Barshi bari naje can din."
yana fara tafiya, sai gashi ya fito yana kade rigar sa.

"Ah ranka ya dade barka da asuba."
Drivern nasu ya fada yana russunawa.

Hannun sa, Najib ya kamo, yana cewa,
"Yauwah Aboki na ka tashi lafiya."

"Lafiya lou ranka ya dade."
"Mami tace kaje ka kaiwa Su Baffa. Buhun dankali biyu da kwaryar doya biyu haka ma Abbah shima haka zaka kaishi."

"To ranka ya dade."
"Sannan a rabawa, su Uncle Marzuk, Adanan, Ahmad,  Usman da Aunty Bilki bugu biyu da kwaryar doya biyu. Akwai, atamfofi ka dibi guda sha biyar ka kai musu.

"To ranka ya dade."

Najib ya cigaba da yi masa bayani,
"Ragowar dankalin ka fito dashi, a bawa Baba me gadi, da iya abu, da Tanni sai kai ku rabe su. Snnan ka dauki turmin a tamfa gudu hudu ka dau daya Baba me gadi ma haka sau iya da tanni ma haka. In na dawo zan bako shadodin ku."

"Toh Alhaji Angode Allah kara budi da daukaka. Allah sa ka gama lafiya Allah yasa kafi haka. Allah baka zuri'a ta gari. Allah yasa kuma gama da duniya lafiya."

"Ameen bakomai."

Sai da yaga ya diba ya saka a mota ya dau hanya, sannan ya bar wajen ya koma ciki.

Mami ba zaune a falo. Ya zauna gefeen ta.

Ya ce,
"Mami an gama."

"Yauwah Allah maka albarka."
"Ameen Ya Allah. Mu tafi ko."

"Toh!"
Ya dauki jakar ta, suka fita. gidan gaba ya bude mata, suka shiga.

Suna tafiya, a hanya sai hira suke. Sharada suka nufa, nan wajen police station.

Wani katon gida suka nufa. Tin daga gate ake, musu sannu da zuwa,

Katon gida ne. Bashi da bene amman ya tsaru, dan ko harabar gidan, zataci motoci guda Goma.

Suna gama gaisawa, suka shige cikin gidan. Katon falo ne wanda yake da ruwan kasan, kujeru hade da labulaye.

Dakin ya gama haduwa. Sallama sukayi shiru babu amsa.

Gaba Najib ya karayi, ya kutsa cikin wani kafar yana kwada sallama.

Wata tsohuwa ce, me kyau da kamala, wacce hutu da jin dadi ya zauna a jikin ta.

Zaune a wani dakin alfarma, wanda dakin ma kansa abin kallo ne.

"A'ah! Mijina ya karaso kenan."
Ta fada tana shirin mikewa. Dai dai nan ya karaso da sauri ya karasa gun ta,

"Hajjaju barka da hutawa."
Ya fada yana mata murmushi.

"Barka kadai Me gida na."
ta fsa cikin fara'a

Najib ya durkusa. Kan sa a kasa, ya ce,
"Ina yini Ummah?"

Ummanh, ta amsa masa da,
"Lafiya lou, kun iso lafiya."

"Lafiya lou Alahamdulilah!"
"Masha Allah, Ina tsohon ne."

"Me gidan nawa."
"Haba Ummah, wane ga sabon jiki ba me zakiyi da tsoho."

Dai dai karasowar Mami cikin dakin da sallama.

Fuskar Ummah cikin fara'a da jin dadi ta amsa mata sallama. Karsaowa tayi cikin dakin.

A gefen kafar ta, ta zauna,
"Barka da hutawa Ummah!"

"Yauwah, Aisha."

Mami ta dukar da kai kasa! Ta ce,
"Ina yini?"

Ummah cikin kulawa ta amsa da,
"Lafiya Alhamdulilah ya gidan."

"Lafiya. Mun same ku lafiya."
"Lafiya lou."

"Masha Allah!"

Wayar ta, ta dauka ta kira Jamila me aiki akan ta kawo abinci anyi baki.

Ummah ta kalli Mami ta ce,
"Ina Abubakar din."
"Ai kinsan be dawo ba."

"Haka ne. Munyi waya dashi dazu ma."
"Kuma kike tambayar mu shi."

Najib ya fada yaan dariya.

Ummah ta ce,
"Yo ai ita tasan akan me na tambaye ta."

Ya juya ga Mami. Ya ce,
"Wai haka."

Harara sa tayi ta dauke kai.

Yana gefen kakar tasa sai damun ta yake.

Har Jamila me aiki ta dire musu abinci cika tana gaisar dasu.

Shigewa tayi, dai dai lokacin lawali me kula da gidan ya shigi dakin.

Ya gaisa su Mami sannan ya juya wajen Ummah. Ya ce,
"Hajiya drivern gidan su Hajiya ne ya kawo kaya."

"Wace Hajiyar."
"Ranki Ya dade, gidan su Najib."

"Oh Aisha bakya dai gajiya."

Kasa Mami tayi dakai tana murmushi.
"Ummah ai ba yawa."

Mami ta girgiza kai Ummah tayi, ta ce,
"Haka zakice daman. Toh Allah saka da alheri Allah muku albarka tare da ya'yan ku."

Najib ne ya amsa da
"Ameen Ameen Ummah mu."

Ummah ta ce,
"Ka sallame sa,"







*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Onde as histórias ganham vida. Descobre agora