143

625 42 0
                                    

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online WRITERS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH DAUKAKAKI YASA KI GAMA DA DUNIYA LAFIYA.*

*REALLY LOVE U ANTY NA*

*THANKS FOR UR LOVE ND SUPPORTING*

*PAGE*
*143*

*Maryam Yusuf* Tnc for ur supporting really love u.*

*Ure so special to me. Tnc for ur care.*

Kwansa uku a kano yaso ya kuma dan yanzu bikin sauran kwana goma sha daya.

A daki ya same ta tana kwance kamar yadda ya zame mata jiki a kwana biyun na.

"Amarya ta."
Ya fada yana leka fuskar ta.

Mikewa tayi zaune, kanta a kasa.
"Ina yini?"

Ta gaida shi,
"Lafiya lou. Ya jikin?"

"Lafiya. Baby na gobe zan tafi kinga abun sai karatowa yake, ya zancen abubuwan da za'ayi. Ko da yake, ga kati nan, komai da abubuwan da za ayi suna jiki."

Ya mika mata wani karamin akwati. Amsa tayi ta ajiye a gefe.

Fuska ya bata ya ce,
Haba Baby na, dauko ki gani man."

Daukowa tayi ta bude kati nan ne wajen kala hudu ko wanne a wajen sa a ajiye, na dauri  auren ya ban banta da sauran dan ya fisu girma, fari ne an masa rubutu da ruwan omon. Za ayi daurin aure a sharada gdn Baffah, ranar lahadi.
Sai na yinin su ranar asabar, sai dinner Ranar juma'a,
Sai budar kai, ranar Alhamis kamu kuma ranar laraba.

Kallon sa tayi, ta ce,
"Hamma abubuwan sunyi waya fa."

"A gun ki ba da bakya son auren."
"Hamma ba haka bane."

"To yaya ne?"
Ya katse ta.

"Yi hakuri."
"Baki min komai ba."

Shiru tayi, kallon ta yayi ya ce, jibi za'a kawo miki kayan da zaki saka zan turo miki da duk shigar kayan da zaki a waya.

"Nagode!"
"Kinsa me?"

"A'ah, aikin da zanje nayi a England ya fito, ranar daurin aure suke son zuwa na kinga tare zamu tafi."

Kai ta girgiza ta ce,
"Aah Hamma kar ka so ma, ni dai ka bar ni a nan kawai har kaje ka dawo."

Kallon ta yayi ya ce,
"To ni ban amince ba."

"Kayi hakuri."
Shiru yayi dan da har ya dau zafi. Najwa na kara burgeshi da bada hakurin nan. Kafin kace tayi laifi ma zata baka hakuri a wuce wajen.

"Shikenan zan turo miki da kudin gyaran jiki da kayan ado kinji."

Kai ta gyaada masa kawai.
"Baby yaushe rabon da naga murmushin ki."

Kwalla ce ta ciko mata ido, tuna irin soyayyar da suke sha da in dai suna tare bata son su rabu, sannan fuskar ta bata taba rabuwa da murmushi.

Ita kanta tasan bata kyauta masa amman bata san yada zatayi bane.

Murmushi yayi, ya ce,
"Zaki shigo hannu ne."

Mikewa yayi ya ce,
"Ki fito muje gidan su Ummah na fadawa Mami tace ki shirya."

Fita yayi. Kanta ta kifa akan gado tana matsar kwalla.

Mikewa tayi ta saka wata bakar doguwar riga ba karamin kyau tayi ba.

Fuskar ta, ta daurayo ta zo ta shafa hoda. Turare kawai ta fesa ta fita.

A falo ta same shi, shida Mami, kallon ta yayi ya ce, ki kwason katin na goma goma zamu biya mukai wa Khadija.

Komawa tayi ta debo masa

Sallama sukai wa Mami suka fita. Mami kanta sai da suka burge ta. Dan ba karamin dace da juna sukai ba. Shi ya bude mata motar ta shiga.

Gidan su Ummah suka fara zuwa, Ummah da Baffah na zaune.

Ummah na gano su, ta fara fadin.
"Kaga amarya da ango, kaga har wani sheki sukai."

Najib sai dariya yake, Najwa kuwa kan ta na kasa.

Gefen su Umma suka zauna, Najwa ta gaida Ummah. Kanta a kasa.

Baffah ta gaishe, yana sa musu albarka.
"Allah muku Albarka, Allah ya bada zuri'a daiyiba ya kade fitina."

Najib ne me amsawa da
"Ameen! Ameen"

Najwa kuwa kanta a kasa, sai da ya gama sa musu albarka, Sannan ya ce,
"Amman dai yanzu komai ya dai dai ta ko?"

Najib ne, ya ce,
"Eh Baffah gamu ma tare."

"Masha Allah ana cigaba da hakuri da juna. In anyi auren ma haka za'a nayi. Sai hakuri."

"Insha Allahu, Baffah baza kuji komai daga gare mu ba."
"Allah yasa."

"Ameen!"
Daki Ummah ta ja, Najwa, zaunar da ita tayi, ta na bata sirikan aure. Tin Najwa najin kunyar Ummah har taga abin ba na kare bane.

"Najwa a aure babu jin kunya, ba wai kunya ba a'ah kunya wajen farantawa me gida, bama ke da kike da kishiya sai kin mike tsaye wajen gyara kan ki, ki karanci duk abinda ya fiso a tare  da ke, da wanda yafi so kina masa."

Ummah ta ce,
"Bari kiji na fada miki Najwa babu Namijin da yafi karfin mace sai dai in bata san yadda zatayi mu'alama dashi ba.

Mace 'yar ce me baiwa, ke mace, Ubangiji Allah ya bata wata baiwa da daraja ta musamman mace ita ce rufin asirin 'da namiji, abinda zakiyi ki kara karkato da hankalin da namiji kanki shine, biyayya ki bishi sau da kafa kiyi masa biyayya ki kula dashi kamar yaro dan goye.
Duk abinda kika san yana so kifi shi so, haka nan duk abinda kika san baya so kifishi 'ki."

"Sai *Hakuri,* ki zamo mai hakuri da kamun kai, ki zamo me hankali da nutsuwa ki zamo mai tatausan lafazi ga mijin ki.
Kiyi hakuri da abun da ya kawo ya baki kada ki zamo me hangen na sama dake rinka kallon na kasa dake ako da yaushe."

"Sai *biyayya,* biyayya ta zamo jigon zaman auren ki, Najwa yana yi bari na bari, idan ya dawo daga wajen neman abinci, ki taryo shi kina sannu da zuwa megida kina goge masa gumi, ki zaunar da shi kan kujera ki cire masa kayan jikin sa, wato ki rage masa kayan dake jikin sa kamar takalmi, in court ce ki cire masa ta sama, in babbar riga ce ki cire masa, kiyi hanzarin kawo masa ruwa me sanyi ko lemi, ya zamo kin shayar dashi.
   Ki hada masa ruwan wanka ki kai shi yayi, ko ki taya shi koma kuyi tare, ki bashi ko saka masa kaya mara sa nauyi, wanda zai sake a cikin su, ki rike hannun sa, ko ki fada jikin sa ki jashi gurin cin abinci. Ki zuba masa ki tura gaban sa yana ci kina  kara masa wani a haka se yaci da yawa ba tare da ya sani ba. Kar ki damu da sai kinci ke dai burin ki, ki ga megidan ki ya saki jiki ya ci abincinki ya koshi."

"To ya megida ze rinka cin abincin ki yana koshi, dole ne ki gyaragirkin ki kisan irin kalar abinci megidanki yafi so,
Kada ki yuwa  mijin ki girki daya saboda sauri gudura kiyi masa abinda ki kasan ransa yafi so."

"Akwai kalolin girke girke na hausa na gargajiya na turawa na larabawa ke har da nasara kai. Najwa ina son ki kasan ce wacce mijin ta ba ya iya cin abinci a wani waje duk in da yaje ba ze ci komai ba har sai ya dawo yaci girkin ki. Ko tafiya ze yi wata kasar sai dai ya tafi akan dole in ba halin tafiya da ke,"

Sai *Tsabta* nasan kina da ita na kuma tabbatar, ki kara dage dantse, ki kasan ce mai gyara gidan ki, ki tsaftace shi ko, da yaushe falonki ya kasance cikin gyara ki turare shi da turaran wuta me dadin kamshi.
  Dakunan ki da na megidanki dan Allah k rika tsabtace su da kanki kada ki bari 'yar aiki ko yaron gida su gyara miki, dakin miji wannan kamar kin bayyanar da sirrin ku ne, ki gyara dakin mijin ki ko ina ki kade ki share ki goge, ki turare su, su rinka fitar da dadin kamshi wanda zai na kwantar da hankali, ban dakin ki na masa turare ya kasance kullum shi ma ciki kamshi, Kananun abubuwan sa, irin su shimi, gajeran wando, hankici ke zakina wanke masa. Ki goge ki sa musu turare ki adana su."

*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now