155

857 53 0
                                    

*NAJWA*

BY *Maryam S Indabawa*
*Mans*

Dedicated to *Rashida A Kardam*
*Anty Rash*

*Allah dafa miki. Allah karawa Mama lafiya da nisan kwana. Ameen*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya online writers*

*Allah kara mana hakuri da juriya.*
*Ameen*

*Gidan aminci da karamci. Allah kara basira Ameen*

Page
*155*

*Zainab Suleiman (Zetty) Maman Hanan*
Allah kara basira da zakin hannu. Na jinjina miki Allah ya raya Hanan ya karawa Mama tafiya.
*Ameen!*

So much love u.



Da asuba ya tashi yai wanka yayi sallah ya zuba wa Najwa ido, tana ta shakar baccin ta. Sonta da kaunar ta ya kara ninkuwa a zuciyar sa.

Hannun sa ya dauka yana shafa fuskarta ta dan bude idon ta da suka kumbura sukai jajir dasu.

Murmushi yayi mata ya ce,
"Najwa tashi kiyi sallah kinga gari ya waye."

Marairai ce masa fuska tayi kamar zatai kuka, ta ce,
"Hamma!"

Da sauri ya tari nunfashin ta ya ce,
"Yi hakuri Baby na, Hamma ne ko? Rabu dashi ba ruwan mu dashi."

Ya dungure kan sa zai kuma kenan ta rike hannun nasa. Tana masa wani irin kallo.

"To yi hakuri, tashi muje."
Kai ta gyada masa sai dai ta kasa tashi.

Da kansa ya dauke ta ya kai ta bandaki. ruwa ya hada mata me zafi ta gasa jikin ta, shi ya daura mata alwala ya fito da ita ya saka mata wata doguwar riga, ya kai ta kan sallaya.

Tana idar da sallah ta kwanta a wajen, da sauri ya isa gare ta,  ya dago ta ya rumgume ta a jikin sa.

Kallon ta yayi cikin so da kauna, ya ce,
"Nagode miki Najwa, Allah miki Albarka Allah ya bamu zuri'a ta gari."

Kanta ta kwantar a kirjin sa tana lumshe idanun ta, da suka kumbura saboda kuka.

Gado ya dauke ta suka hau, a jikin sa tayi bacci yana jijjiga ta kamar wata yarinya, shi kuwa ya kasa baccin ma sai kallon fuskar ta da yake yi yana sa mata albarka.

Sai karfe sha biyun rana suka tashi shi yai mata wanka ya tsane mata jikin ta sannan ya shafe mata jikin ta da mayukan ta.

Hoda ma shi ya shafa mata da man lebe kwalli ne kawai ta saka da kanta.

Wani milk din less ne wanda akai masa ado da purple colour ya dauko mata wanda akai masa dinkin riga da siket.

Dinkin ba karamin kyau yayi ba. Rigar ta zauna a jikin ta sosai haka siket din eight pieces ne, ya zauna shima a jikin ta.

Ba karamin kyau tayi ba, shi ya fesa mata turare ya gyara mata kai, bayan ya busar mata gashin ta, yai mata parking da ribon.

Be daura mata dankwalli ba dan yana son kallon gashin ta a haka.

Sai da ya gama da ita tsab sannan ya nufi bandaki dan yin wanka.

Shima yana fitowa ya shirya cikin milk din wando da riga yan kanti, ba karamin kyau sukai ba. in ka gansu sai kayi zaton gasar fitar da me kyau zasu.

Duk kan su sai tashin kamshi suke, kamar wandan da sukai barin turare.

Najwa kuwa na jikin Najib tana zuba masa shagwaba, shi kuwa ya gigice sai lallashin ta yake yi.

Falo ya dauke ta suka yi, Abincin da Mami ta aiko musu dashi ya dauko.

Lafiyayen abinci me rai da lafiya ta hada musu.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now