124

558 54 1
                                    

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE

*124*

Sai karfe uku suka koma hostel lokacin har Momy ta kai.musu abinci.

Wanka sukai sannan suka ci. Basu dade da gama ci ba akai sallah la'asar suka mike sukai sallah.

Sai da suka idar suka fita shan iska.
kallon ta Zahra tayi ta ce,

"Sis na san kin girme ni. Amman kuma ina da abinda zan fada miki."

Kallon ta Najwa tayi ta ce,
"Ina jinki."

Durkusawa Zahra tayi ta kama kafafun Najwa ta ce,
"Dan Allah ba dan ni ba ki aminta da abinda zan fada miki. Bazanyi abinda zai cutar dake ba."

Dagota Najwa tayi. Ta rumgume ta.
"Zahra nasan kina so na. Son da bazai misaltu ba. Insha Allah zan aminta da duk abinda kike so gareni."

"Promise!"
Ta fada tana mika mata hannu.

"Nayi alkawari."
Ta kama hannun nata.

"Sis yanzu fa mu a level three da mun shiga four zamu ga har mun kammala."

"Haka ne."
"Me kuma zamu zauna yi a gaban iyayen mu. Duk da nasan ba mu wuce zaman gida ba."

"Haka ne."
"Amman dai kinsan aure shine cikar mutuncin yar mace. Kuma suma iyayen namu zasu so su ganmu a gidan mazajen mu."

Duka Najwa ta kai mata. Ta ce,
"Aure dai kike so ko?"

"In naso ma wani abu ne. Dan sunnah ai bazai qi sunnah ba."

"Haka ne Zahra."
Najwa ta fada tana kallon ta.

"Najwa ya kamata tin yanxu ki kama me son ki ba sai lokaci ya kure ba."
Kallon ta Najwa tayi.

"Eh Samari da yawa sun zo amman kin qi aminta dasu, Najwa soyayya bata taba hana karayu wallahi sai dai in kaso ta hanaka."

"To me ya kawo wannan maganar yanxu."

Murmushi Zahra tayi ya ce,
"Wani ne me suna Najib yazo yake son ki kuma da aure.
Najwa wallahi kika ganshi sai kema ya miki yana da hankali da nutsuwa ga tarbiyya ta magana ma sai kingane hakan.
in har kika bar Najib ya tafi kinyi asara sosai wacce da wuya ki samu kamar ta."

"Ni da kika ce akwai abinda kike son na aminta dashi me ya kawo wannan maganar."

"Sis! Najib nake so ki aminta dashi ya zamo mijin ki.
Dan Allah kada kice A'ah nasan kinsan girman alkawari. Dan Allah ki cika min wannan alkawarin."

Kallon ta Najwa ta tsaya yi. Kai ta gyada mata.

Rasa me zatayi tayi, dan haka kawai sai ta rumgumeta tana kuka.

"Ya zanyi kinsa na dauki alkawari dole nayi kokarin cika shi. Amman ki sani komai ya biyo baya kece sila."

"Ba komai Sis kuma ba abi.da zai biyo baya sai alheri kinji. Nagode."

Wannan yarinyar ita ta katse musu magana ta ce,
"Anty Zahra, ana kira"

Ta nuna mata wajen da yake tsaye a jikin mota. Sanye yake da bakin wando da farar riga me dogon hannu.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now