113

575 54 0
                                    

*NAJWA*

🌐 *HAJOW* 🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHODA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE *113*

Yana zuwa gida ya kira Summy. Dagawa tayi cikin farin ciki dan tana tunanin yau zasu je mata.

Shi ya fara mata sallama. Sannan ta amsa masa, cikin sanyin murya.

"Sumaiyya ya kike yasu Mama."
"Duk suna lafiya."

"Masha Allah. Daman zan fada miki anjima da yamma zan kawo miki sako inji Najib, dan an masa waya ana neman sa awajen aiki, a yau ma zai bar kasar."

Ji tayi kirjin ta ya buga. Mazewa tayi ta ce,
"Allah sarki ba komai. Allah ya bada sa'a."

"Ameen Nagode. Sai anjiman"
Sukayi sallama.

Tana ajiye wayar ta saka kuka, Ita da tayi niyyar rikita shi da adon da zata masa, amman wai bama ya garin, kuma kasar zata bari.

Ita kuma haka Allah ya daura mata son wanda be san yadda soyayya take ba.

Nikam nace son wacce ba ta ita yake ba dai.

Kamar yadda sukayi da yamma ta shirya tsab. Cikin Riga da zani na atamfa.

Sai babba mayafi da ta yane jikin ta dashi, duk wanda ya kalle ta yasan tana cikin damuwa.

Dan Mama ma sai da ta tambaye ta abinda ke damun ta.

Wajen karfe hudu da rabi Khaleel ya kira ya shaida mata ya zo.

Dakin baki tasa aka kai shi, lemo ta aika masa dashi, sannan ta je ta fadawa Mama ana kiran ta a waje.

Ganin ta da shiga mai kyau yasa Mama bata damar zuwa.

Da sallama ta shiga dakin kanta a kasa, amsawa yayi, cikin sakin fuska, yace,

"Sannu da zuwa, Matar mu insha Allahu."
A ranta ta amsa da Ameen.

Can daga gefen sa ta zauna kan ra akasa.
"Ina yini?"

Murmushi kwance a fuskar ta, ta gaidashi.

"Lafiya lou Summaiyya ya gidan ya su Mama."
"Lafiya lou suke."

"Sumaiyya ina kara baki hakuri akan abinda ya faru, wallahi baki damuwar da ya shiga ba da be samu zuwa gun ki."

Wani sanyi taji a ranta jin ya damu da ita. Kai ta girgiza. Ta ce,
"Ayyah ba komai ai."

"Yauwah Nagode. Gaskiya nan indai Najib ya zauna tare dake zai kauna ce ki fiye da yadda yake kaunar ki yanzu haka."

Kai tayi kasa dashi alamar jin kunya. A raina nace sai kace ba Summy ba, wai har da su jin kunya abinda ba halin ta bane.

Hira suka dan taba duk akan Najib ne, yana mata bayanin Najib da abinda yake so, da yadda ya taso da wajen aikin sa da yan uwan sa dake garin nan.

Duk abinda yasan ya kanata ta sani akan Najib sai da ya fada mata su.

Sannan ya daura da,
"Najib nason mace me addini da ilimi, yaba son mace mai tsabta, da tarbiyya, yana son macen da ta iya girki. Kuma duk nasa,n bamu da matsala ta gun insha Alalhu."

Kai ta gyada. A ranta kuwa cewa take,
"Girki dai da sauki, tsafta kuma ai baza arasa masu aiki ba."

A fili kuwa sai murmushi da take yi.
Kallon ta Khaleel yayi, ya ce,
"Toh Sumaiyya gashi inji abokina ya ce, kiyi hakuri ba yawa."

Shiru tayi, sannan tace,
"Har da wahala, toh nagode."

Murmushi yayi sannan ya mike,
"To ni zan tafi, sai munyi waya."

"To shikenan nagode ka gaishe shi."
"Zai ji, zai ma kira ki."

Suka fito sai da ta kai shi har jikin motar sa sanna ta juyo.

Gida ta shige aran ta kuma tana tunanin Najib da tsare tsaren sa, da irin halaiyar sa me kyau da burgewa.

Dakin ta, ta shige, ta zazzage kayan rafar yan dubu daya ne suka fado. Dauka tayi tana murna.

Kayan ciki ta dinga dagawa, duk kaya ne masu kyau da tsada.

Cikin leda ta mayar sannan tayi dakin Mama.

"Mama! Mama! kinga kayan da aka kawon."
Ta fada yana juye su akan gado.

Kallo Mama ta bita dashi, tana daga kayan, sannan ta ce,
"Kuma kika karba."

"Mama to yabani me zan ce."
"Ke baki da hankalin ce masa ya bar su,in kuna bashi zaki aura ba, daga haduwar ku."

Marairai cewa Summy tayi, ta ce,
"Kiyi hakuri Mama zan mayar musu."

"Ai kin riga kin karba. Dan Allah Sumaiyya ki rage son abin duniya kina boye kwadayi ki akan abin mutane."

"Ki yi hakuri Mama bazan kara ba, Yanzun ma ban so karba ba."
"Shikenan Amman kin ji dai abinda na fada ko?"

"Eh Mama."
"Tashi kije, ki ajiye kayan kada a dinka."

"To!"
Ta fada tana debe kayan ta fita daga daki.

A dakin ta kuma mita take wai Mama bata waye ba. Abata abu amman wai baza ta dinka ba. Kuma ta maida hannun kyauta baya.

Tsaki tayi sanna ta debe kayan ta saka a cikin durowar ta. Kudin kuma ta saka su a cikin jaka, idan anjima zata tasaka a account din ta.

Wayar ta, ta dauka ta fara duba hotu nan sa, kalla take tana murmushi.

Da haka bacci ya dauke ta, wanda duk mafarken Najib ta dinga yi.

Najib kuwa suna suka har drivern su yazo yana jiran su.

Motar suka shige sai gida. Suna zuwa gida ya hau hada kayan sa, da yamma zasu tashi

Suna zuwa gida masu aikin sai murnar dawo war Mami suke. Dan ba karamin kewar su sukayi ba na kwana biyun nan da basa nan ba.

Baba kuwa sai nan nan take dasu Najib da Mami ko da taji tafiya zai kara yi, sai taji ba dadi. Amman dayake abin karin nasara ne sai ta taya shi da addu'a.

Daga wajen Baba daki ya tafi, Yana hada kayan sa, yana gamawa ya fice ya tafi asibitin sa, abubuwan da zai amfani dasu ya kwaso ya koma gida

Yana komawa yayi wanka, yayi sallah yaci abinci. Zama sukai a falo suna hira da Mami, mami na kara masa fada da ya ji tsoron Allah a duk inda yake. Ka.

"Najib kaji tsoron Allah a duk inda kake, ka sani duk abinda kake Allah na ganin ka, ka ji tsoron sa kaji tsoron haduwar ka dashi. Kai kaga bama nan kayi abinda ba dai dai ba. Ka tsare imanin ka. Kayi riko da addinin ka."

"Mami insha Allahu bazan taba aikata abinda ya haranta ko ya sabawa addini na ba. Mami amman sai kun cigaba da min addu'a akan Allah ya tsare ni dan ba wayo na ko dabara ta ne zai sa hakan ba."

"Ba komai Najib addu'a kullum muna yi, dan Addu'ar iyaye ga ya'ya ba karamar aba bace, kasan Allah yace addu'oi biyu idan har mutum yayi ba a juyar masa dasu, da addu'ar iyaye ga 'ya'yan, da addu'ar wanda aka zalumta."
Kaga kuwa dole mu dage wajen nema muka Lahira me kyau. Dan in har kaji tsorn Allah to komai ya dai dai ta."

"Nagode Mami! Allah ya saka musu da gidan Aljanna."
"Ameen Najib."

Karfe biyar suka daga, yana me kewar barin Mamin sa.

Wanda tafiyar in da bata zama dole ba bazai je ba. To wani course zai kara karantowa na wata biyar, wannan yasa dole sai ya tafi ya bar Mamin sa.

Dan Mami ita ta samo masa karatun tayi masa komai akai.

*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now