129

553 61 0
                                    

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE
*129*




Lokacin bikin Zahra yazo, Amman Wannan karan ma Najib baya kasar.

Najwa ba karamin jin haushi tayi, inda ya ce, in ya dawo zasu karayin wani reception din nasu.

Ba yadda ta iya sai dai hutuna da vedio da take tura masa.

Amman gaskiya yayi missing dan kyan da Najwa tayi kwayi tsammanin ita ce amarya.

Ji yayi kamar yayi tsuntsuwa ya dawo to ba yadda zaiyi karatun yake dadawa, na wata takwas inda yanzu wata daya ya ci.

Gashi gab da bikin ya tafi. Duk dai abinda zata bukata sai da ya dire mata. Dan wani lokacin sai dai kawai taji alert ta account din ta.

Mamin sa ma taje bikin haka Dadyn sa amman shi besan bikin Zahra suka je Katsina ba.

Anyi biki lafiya an gama lafiya inda aka kai amarya gidan ta kato me kyau da shi.

Ba abinda babu a cikin gidan nan. Tare suka cigaba da bautar kasar su da Najwa.

*Bayan wata biyar*

Su Najwa an kammala service inda tana ta shirye shiryen tafiya gida.

Su Momy kuwa duk basuji dadin tafiyar da zatayi ba.

Ana ya gobe zata tafi a gidan Zahra ta kwana kuka kuwa akarasa me rarrashin wani.

A haka a gida ma daga Najwa har Kannen Zahra kuka suke.

Da haka suka rakata. Sai da sukaga tafiyar ta sannan suka dawo gida da kewar ta.

A gida kuwa ai dan party Hamma Salim da Basma suka hada mata.

Da murna suka tare ta. Dan  Dady ko fita beyi ba.

Wanka kawai tayi, akai mata kwalliya ta shirya cikin wani material baki, jikin sa duk stones ne kala kala.

Sosai tayi kayi, yan uwa da abokan arziki duk sun zo.

Inda Najwa ta samu kyatutuka masu yawa, ansha hotuna an ci an sha.

Inda sai dare ma aka tattafi.

Su Baffah da Ummah duk sun zo.

Sai isha'i tayi, sama tayi wanka tayi sallah.

Kan gadon ta, ta fada ta kwance wayar ta janyo taganta airplane mode.

Ido ta bude dan tasan Najib ya kirata be samu ba.

Cireta tayi, ta shiga hotuna tana son ganin wanda sukai ita da Mami, Dady, Hamma Salim da Basma.

Amman sam babu, wannan yasa tayi tuna ashe me camera da aka dauko ne ya dauke su.

Wayar ce tayi kara sakonni ne suka shigo.

Kafin ta bude kiran sa ta shigo,
"Baby na ina kika shiga wayar ki a kashe."

"Ayyah kayi hakuri, ban ma sani ba sai yanzu da na dauko ta."

"Ina kika je to."
"Wallahi Hamma nane ya hada min party, baka gani ba, har dasu Baffah duk sun zo fa. Kowa na nan ban da kai."

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now