135

623 52 0
                                    

*NAJWA*

🌐  *HAJOW*  🌐

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

By *MARYAM  S  INDABAWA*
*MANS*

DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

*ALLAH YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA.*
*AMEEN*

PAGE
*135*

*Fatitih kema kina raina. Nagode da kwarin gwiwa da addu'ar ku gare ni. Allah ya bar kauna.*


Har bakin mota suka rakosu suna sa musu albarka.

Sannan suka tafi da kewar ta. Itama ta yaba da su dan mutanen kirki ne.

Gidan Khaleel suka tafi can rigiyar zaki. Yana gida yana jiran zuwan su.

Dan har girke girke Khadija tayi musu.

Suna zuwa Khadija ta taro ta, ta zaunar da ita.

Haka Lil N na ganin ta shima yayi wajen ta.

Daukar sa tayi tana masa wasa. Khaleel ta gaisar, suka gaisa kamar sun san juna.

Lemo da Ruwa Khadija ta fara gabatar musu dashi, ruwan ta kurba kadai.

Sai wasa takewa Lil N, Najib kuwa ya zuba mata ido dan ba karamin kyau yaron yayi mata ba.

Hoto kawai yake daukar su ita bama ta sani ba.

Dagowar da tayi ta ya zuba musu ido yana musu vedio.

Hararar sa ta faki ido tayi, murmushi yayi, yai mata gwalo.

Kitchen Khadija ta shiga, Khaleel kuma yayi cikin daki.

Kallon ta yayi, ya ce,
"Baby nah Yaron ya miki kyau kamar naki."

Murmushi tayi kawai.
"Allah ya baki kamar shi nan da wata goma."

Kai ta girgiza kawai ta cigaba da yi masa wasa. Ta dauke hankalin ta daga kan sa ma.

"Tashi muje kuci abincin."
Kallon Khadija, Najwa ta ce,

"Ki bari sai anjima ko?"
Ta kalli Najib.

"A'ah ban yadda ba. Haka fa a gidan su Mamah ma, bata ci abincin ba."
Najib ya bata amsa.

Murmushi Najwa tayi ta kalli, Khadija ta ce,
"Allah Sis naci abinci, kafin mu fito, na miki alkawarin kafin mu tafi zanci."

Murmushi tayi, ta ce,
"To shikenan ai tayi alkawari kaga."

Khaleel ne ya fito, ya ce,
"Kanwata yana ta kura miki ko?  Allah sai kin dinga maganin sa dan akwai takura kina ganin shi nan."

Ita dai Najwa murmushi kawai take yi, fita sukai suka barsu Najwa kadai.

Dakin baccin su ta ja ta, suka je tana kallon hotu nan bikin ta.

Dan Lil N ma goya shi tayi har yayi bacci a bayan ta.

Khadija tayi tayi ta sauke shi taki.

Zaman da suka danyi da Khadija ba karamin sabawa sukai ba.

Khadija aranta ta ce,
"Yanzu Najib zai yi aure mace mai mutunci da iya zama."

Suna cikin daki suka dawo wajen magariba. Falon suka koma har lokacin tana goye sa Lil N.

Najib na ganin su ya dauko waya ya fara daukar hoton su.

Da taga abinda yake ma kai kawai ta girgiza tayi shiru dan baza ta iya masa magana ba.

Sallah magariba sukayi, sannan suka dawo. Abinci suka ci suka mike zasu tafi.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now