138

829 54 0
                                    

*NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya online writers*
*Allah kara hada kanmu. Allah kara mana hakuri da juriya*

*Ameen*

Dedicated *Rashida Abdullahi Kardam*
*Aunty Rash*

*Really love's u. May Allah bless you.*
*Ameen*🙏🏻😘😍

Page
*138*

*Khadija Sallehu. Marubuciyar nida Abba nah.*
na gaishe ki jinjina gare ki. Allah kara basira da daukakka.



Cikin ikon Allah, har Najib na kokarin zuwa Birthday din Lil N da za'ayi na shekara uku.

Yaso suzo da Summy amman ta ce, ita bazata je ba.

Dan yanzu shi da summy abin har mamaki yake bashi dan ko ya neme ta bata yadda bare har ya samu nutsuwa.

Haka ya shirya da farin cikin xuwa ganin masoyiyar sa.

Bama tasan da xuwan sa ba sai fitowa tayi falo kawai ya ganshi yana ci abinci.

Komawa daki tayi da saurin tin kafin ya ganta. Nan kuwa bata san ya ganta ba.

Sai da Umma tayi sama ne, ya mike ya nufi dakin.

Tana kwance a kan gado ta lumshe idanun ta ya shiga.

Ko bude kofar ma bataji sanda aka yi ba tana can tunani.

Kallon ta ya tsaya yi, yana daukar ta a hoto. Motsi taji a kuda da ita wannan yasa ta bude idon ta.

Tana ganin shi ta zaro ido, murmushi ya sakar mata.

Mikewa tayi da sauri ta ce,
"Hamma mu koma falo."

Tayi hanyar fita. Hannun ta ya kamo. Juyowa tayi, cikin tsoro da faduwar gaba.

"Hamma ba kyau fa. Ka sakeni mu koma falo."

ido daya ya kanne ya ce,
"Mene in mun zauna anan?"

Kai ta girgiza ta ce,
"Hamma ai bai  dace ba mu kebe dagani sai kai. Dan Allah ka taho mu fita."

Kallon ta ya tsaya yi, shi dariya ma take bashi. Idon ta ya ciko da kwalla, daga gani kuma a tsorace ta ke.

Hannun nata ya saka, ya ce,
"Muje!"

Da dauri tayi gaba kamar zata fadi. Sai da suka isa falo ta sauke wata ajiyar zuciya, wacce sai da yaji saukar ta.

Kallon ta yayi, kasa tayi da kanta. Ta durkusa, ya ce,
"Ina yini Hamma ya hanya?"

Murmushi yayi ya ce,
"Lafiya Alhamdulilah."

"Yasu Mami da Anty na."
"Suna lafiya suna gaishe ki."

Ido ta rufe, kallon ta yayi ya ce,
"Na samu Baby na lafiya."

Kai kadai ta daga masa.
kallon sa tayi ta ce,

"Amman shine baka fadan kana hanya ba. Bayan dazu ma munyi waya."

Ido daya ya kanne ya ce,
"Surprise ne."

Murmushi tayi, kallon ta yayi, ya ce,
"Gobe birthday din Lil namesake fa."

Murmushi tayi ta ce,
"Mommyn sa ta kirani take fada min ai."

"Yauwah kinga dai ki je ki kwana ko?
Ido ta zaro ta ce,

"Kwana kuma."
Dariya yayi, ya kura mata ido. Kasa tayi da idanun ta Ya ce,

"Tsokana nake. Idon ki nake son kawai naga kin bude su. Kuma nasan hakan bazai faru ba sai na kawo abin mamaki. Ina son idanun ki Najwa suna burgeni. Suna sani nishadi."

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now