DA AURENAH page 3

1.7K 62 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


07081095452

Page 3

Baxan gaji da miqa godiya ta da jinjina ga my m k ba Allah yabar tare Ameen




Huwailat Abdullahi Samaru shine cikekken sunana mahaifina Alh Abdullahi yakasance Dan Asalin garin Adamawane Wanda yawon Neman nakai yakawosa jahar Kaduna Har Allah yasa ya xauna a cikin samarun zariya inda yasamu wani Bawan Allah yabashi Shago ya dinga jire masa Dan yaga yana da Amana cikin ikon Allah kuwa akaita samun alkhairi nan da nan ko anbasa Sallamarsa bai ansa Dan Yana masa duk abun buqata da Alhajin yaga haka bayan wasu yan shekaru sai yabude wani shagon ya danqasa ga Abdullahi yace gashinan kaima katsaya da kafafuwanka kamar kowa kaje gidana Ku daidaita da Zuhra nabaka ita xaman haka nan ba Aure ya isa cikin matuqar farin ciki yai Godiya matuqa har yanajin kamar almara wai shine xai Auri Zuhra yarinya mai kyau da kamala koda yaushe cikin shigar mutunci gata da daraja manya gaskiya yayi dace Allah yasa tasosa dayafi kowa murna dajin dadin rayuwa
Abdullahi ko kana da wadda kake sone naima shigar sauri inji Alhaji Mamuda cikin washe Baki Abdullahi yace ko kadan wlh ina matuqar godiya Allah yasaka da alkhairi ya qara girma amma inba damuwa xan shirya naje can wajenmu Dan nafada masu suxo Neman Auren yaqara sunne kansa Qasa Alhaji yace ba damuwa indan wannan inka shirya kaimun magana yai godiya sosai yatashi ya tafi yana tunanin yanda xai fuskanci Zuhra da wannan almari ko xata Amince koko baxata Amince ba fargaba ta samu xuciyarsa karfa taqi yarda hakan baqaramin tada masa hankali xaiba amma dai xai jaraba xuwa anjima da dare gunta yaji ta bakinta fatansa yaji khairan daga gareta

Dare nayi Abdullahi ya shirya tsab yacaba kwalliyarsa ya fesa turarensa yaje gun Zuhra Dan yagabatar mata da kansa da abunda yakawosa abun farin ciki Zuhra tafada masa ita mahaifinta yafara fadamawa kafinshi kuma ta yarda ta Amince fatanta yariqeta da mutunci
Sundan taba hira yafada mata xaije garinsu Adamawa yataho da iyayensa su naima masa Aurenta taimasa fatan alkhairi suka rabu

Bayan sati Abdullahi yakama hanyar Adamawa ya fadama yayyensa da Mahaifiyarsa don Mahaifinsu Ya rasu sun jinjina lamarin inda suka dinga nuna masa yahakura yai Auren gida yafi yaje wata uwa duniya yai Aure ga kuma yan uwansa mata cike da gari amma saiya tsallaka wata Jaha can shidai yadinga kwatanta masu qima da darajan Alhaji Mamuda harmada son da yakema Zuhra
Akan dole suka yarda suka shiryo suka biyoshi da duk abunda yafada masu anayi na al adar samarun
Sai dai suna xuwa labarin yasha banban Dan Alhaji Mamuda yace baxai amshi komiba sai sadaki naira dubu goma wannan karamci ya birgesu sun kuma yarda da maganar Qaninsu daya fada kan Alhaji Mamuda Dan haka cikin mutunci akai komi da komi suka tsaida biki nan da sati guda kacal

Da daddare Alhaji Mamuda ya kira Abdullahi yatambayesa kana da inda xaka aje matarkane
Yace mun magana da Abokina Isiyaku xai nema mun gidan haya kafin nayi nawa in Allah ya hore
Alhaji Mamuda yai murmushi yace to tawa gudummuwar itace gidana dake qasan layin shagonka yasa hannu ya dauko takardun gidan yamiqa masa Allah ya Baku xaman lafiya
Kasa magana yayi Dan Alhaji ya gama masa komi ga mata ga jari ga matsugunni lallai Alhaji mutum ne harda rabinsa ma
Godiya yafara xubawa Alhaji ya dakatar dashi ya shige gida yabarsa cike da farin ciki yaje ya gwadama yan uwansa suka sake Aminta da Dan uwansu yasamu ubangida nagari mai alkhairi dabaya da qyashi
Anan suka dinga masa nasiha da kwatanci kan yariqe matarsa da qima yaqara daraja Alhaji Dan ya gama masa komi ya guji son xuciya duk da ba halinsa bane amma xuciya batada kashi

Ranar juma a yakamata daurin Aure bayan an sauko sallan juma a aka daura Auren

Zuhra Adamu Samaru  da Angonta Abdullahi Garba Adamawa

Amarya ta tare gidanta cikin kwanciyar hankali da lumana
Ahankali Arxiqinsu keta habaka a gefe guda kuma Yakoma karatunsa inda yasamu damar shiga jami ar Xariya cikin nasara da taimakon Allah ya kammala karatunsa Sirikinsa ya nema masa aiki a cikin Zaria
Asannan Zuhra tana da yaranta Hudu Abba ne Babba Mamuda shiyaci sunan Alhaji sai Mustapha nabi masa Garba da suke cema Malam saini Autah Huwailat
Tunda nafara wayau na girma nake da burin karatu mai xurfi Dan akwai wani makwabcinmu Alhaji Sanusi Dr naji ana kiransa amma bantaba ganinsa da kayan malaman Asibitiba Dan haka nake tambayar yah Abba waishi Dr dama basaiya saka fararen kaya bane kuma ba sai yayi alluraba
Sabodame kika tambayen saboda naga Alhaji Sanusi baya sasu amma ana kiransa Dr
Dariya yayi kincika Tambaya Autar Mama Aiba dole saika karanci Likita ake kiranka Dr ba shi akan karatunsa ne yazama Dr dariya nayi to Yah Abba kenan nima xan iya xama Dr Ashe nan gaba ammafa ni nafison naxama Dr din Dalibai manya
Sanin halina da tambayoyi yasa yace to kidage xan saki makarantai kuwa
Ina gama primary naci ta kwana nan kuma Mama tace bata yardaba natafi wani uwa duniya saboda karatun boko naita kwana kodai asakemun ko kuma nabar makarantai
Da Qal akasamo min Jeka ka dawo dake nan cikin garinmu nafara xuwa
Ina Class 3 nafara samari abunda yajamun fada sosai a gidanmu Wanda har kuka yinakeyi in anamun fada
Amma duk da hakan acikin samarina ina matuqar son wani Habeeb a bayan Anguwarmu yake so tari inxani islamiyya ina kamasa yana kallona da mun hada ido xai murmushi baitaba min magana ba amma fuskansa baya raboda murmushi duk sanda muka hadu

Tofa yakenan jama a 🤷🏻‍♀

Kubiyoni danjin ya abun yake

Taku Haupha

DA AURENAWhere stories live. Discover now