DA AURENA page 89__90

688 32 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452










Page 89 90









Yau tunda ya kasa goron yake ciniki abun yai masa dadi sosai yake da burin tara kudin da zai je Adamawa gun danginsa da mahaifiyarsa amma bai tara na kirkiba amma yau gashi yanata samun ciniki wanima alkhairi yake bashi  kyauta .

Itama ba laifi inna tana samun ci gaba gun sana'arta sosai da sosai da rabin kwano ta fara yanzu har kwano biyu da rabi take yi ya kare tsab .
Itama anata ra'ayin tanason ta tara kudin ta da zasu ishesu motar zuwa Adamawane danta nemi yafiyarsu kan abunda ta aikata masu tabbas tayi nadama taga ishara sosai kan abunda ta aikata .

Malam ma yadage yo itace yana kawowa gida yana kasawa yana saidawa hamsin da dari shima abun Masha Allah yana samun ciniki sosai da sosai .
Anashi burin yanason tara kudin da zaije neman 'yan uwansane .









Wani dan karamin daki aka jefasu babu haske ko kankani cikinsa ga wasu masifaffun cinnaku daketa gartsa masu cizo batare da tausayiba  ko ganin sun ciza da yawa su daina cizon .


Sai da suka kwana sannan aka zo aka budesu gaba daya hasken saiya saka idanunsu suka dan daina gani nadan wani time .

Basu zame ko inaba sai gaban wani katon mutum bakikkirin fuska daure ba alamar imani .

Cikin daka tsawa yadubi Amadu yace ,,ina matanka Huwailat ?
Amadu ya hade miyau da kal ,
,,saketa ranka shidade mun rabu .

,,da kinsaketa yana ina ?

Cikin matukar tsoro Amadu ya sadda kanshi kasa .

Inna ya duba kafin yai magana ta rike kafafuwansa ,,yaro kaiwa iyayenka kai hakuri wallahi bansan gaskiyar lamarinba yarone gayanan shine ya haifar da komi wallahi sai dai hakuri amma ai munga ishara dan munshiga wahala sosai da sosai daga baya .

Major da maganar tsohuwar ta cikama kai ya dubi wani soja dake tsaye kawai .

Sai gani nai ya kwashi inna ya watsa waje ,,karda kasake barin naganka harabai gunnan , ya koma office din .

Cikin matukar ciwon jiki inna ta rarrafa ta nufi get din fita barrack din , ganin wani tarin yashi yasa inna fadawa kansa tana sauke ajiyar zuciya tamkar tasha gudun fanfalaki .

Wani soja yazo wucewa ya ganta kwance tamkar mai barci hakan yabashi haushi kunsan soja baison lalaci 😎

Ya daka mata tsawa ta farka a razane .

,,ke uwarmi kike anan ?

,,yaro wallahi hutawa nake ,

Hutu kuma 😳

Wani banzan kallo yai mata ya kwadama wani soja kira ,,maza ka tsareta ta kwashe yashinnan ta maidasa can , ya nuna can cikin lungun barrack din yai tafiyarsa .

Haka inna ta dage iyakar dagewarta ta cire kallabinta taci gaba da dibar yashin tana kaiwa gun da aka sata kaiwa .

Kafin ta gama saida taji jikinta tamkar ba nataba ko kadan batajin zata iya kara moruwa nan gaba da kyal tafito ta kama hanya kasa ta nufi bakin titi dan jin ina take .

Sosai Amadu keshan wahala ba sassautawa koda yaushe tambayar dayace ina Huwailat  ?

Tun yana basu amsar baisan inda takeba harya kaiga dasun tambayesa sai yasaka kuka .

Akallah Amadu na fuskantar horo da matsi kala daban daban daga gun wasu marassa tausan sojoji  
Duk Wanda yasan Amadu yagansa bai ganesa ya canza ya rame ya kwanjame ya fita hayyacinsa  gwanin tausai .



Da kyal inna tasamu Wanda ya taimaka ya kaita samaru kyauta ta iske wani tashin hankalin kuma Hafsat ba hannun dama ya koma tamkar lagwani ruwa masu zafi ta samu ta gasa jikinta  Uncle ya siyo mata shinkafa taci amma takasa ci da kyal ta samu tasha ruwan tea sai barci .













Sai da ta tabbatar ya ci duk abunda ta tanadar masa sun taba hira barkwanci sannan ta saka natsuwa ta bashi labarinta kaf .

Cikin tsananin tashin hankali ya dubeta kina nufin kece kika dandana wannan bakar rayuwar princess ?
Ta goge hawayenta ta daga masa kanta .

Sosai yaji tausanta yakara jin kaunarta sosai a ransa dan haka ya tabbatar mata da ba gudu ba ja da baya zai aureta dan ya bata duk wata kulawa da ta gagareta a rayuwar aurenta ta baya .

Sosai ya kwantar mata da hankali ya shiga suka gaisa da kaka yai mata yayyafin kudi ya kara jajjada bukatarsa na auren Huwailat .

Sosai lamarin yaima 'yan gidan dadi .

Sukai bankwana ya kama hanyar komawa gida .

Amota yaketa tunanin yanda zai bulloma Major yake dan yau yagane itace Huwailat din major .

Maganar gaskiya bazai iya sallama princess ga major ba .

Major ya saki damarsa to shi bazai samu dama yai wasa da itaba .
Dan haka kowa tasa ta fishshesa kawai .



Tofa jama'a kundai ji  abunda captain yace 🤔

Yanda zata kaya muhadu a next page

Haupha ke maku fatan alkhairi 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

DA AURENAWhere stories live. Discover now