DA AURENA page 32__33

737 36 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452

Page 32 33


Tafiya nake ina jefa kafafuwana harna kusa shanye kwanar gidan Amadu naga dacewar zuwana gidan Inna Dan nafadama My Uncle  abunda yafaru.

Haka kau nadawo baya na isa gidansu Amadun tun a zaure najiyo muryai Hafsat da inna nata dariya . labe ba halina bane amma naga dacewar tsayawa nayi laben konasamu wani abun wata rana yaimun tasiri.

,,Nace su Huwailat ko Lauya za a zamane 💁🏻

,,Inna kada kidamu nidai fatana kada kibari Amadu yace zai maida Huwai dakinta dan Iyayenta tare yake dasu sosai sannan ana gama aurena dashi kirabashi da kaf ahalin Huwai idan bahaka saita zame maki kadangaren bakin tulu wallahi.

,, ke daina bata bakinki yarinya indai zaki soyo mun kaji ki dafo munsu da shinkafa kullum mai jar miya aiba mai jin kanmu.

Shewa naji sunyi kamarma hada kashewa.

,, indai wannan ne damuwarki anyi maganinta har kudi zansa yabaki kifara sana a yasha fadamin Huwai ceke hanasa baki jari wai kin tsufa sai son kudi kamar tsohuwar jawara.

Nace batai karya ba sabuwar jawarace 🤷🏻‍♀

.Inna ta lailayo wani uban ashar ya makamun.  ,,bar yar banza yanzu ainaga inda zata dan dawowata kenan daga gidansu inata kuka nace ta zazzageni dan kawai naje kaimata kayan fadar kishiya.

Bakiga yanda iyayen keban hakuriba uban yace ,,barta damutake magana indai tasake tabar gidan yaron kirki kamar Amadu na sallama duniya ita wallahi.

,,dan haka kike birgeni Innar Amadu . ( hakan shine sunanda Hafsat ke kiran inna daman)

Toke ba uwarki bace kenan Hafsat 😜

Ganin zawo na niyyar kamani dan ruduwa na fada gidan da sallamata.
Ganin nice ba wadda ta amsamin saima harara da kallon kyama da Hafsat kebina dashi.

To uwar kishi yanzu ubanme kikazo yi nan gidan koko biko kika zo dan anfadamin wasu matan dadin aure kesa in ansakesu suje biko basu bari a je a maidosu .
Wata matsiyar dariya Hafsat tasaka ,, inna kinsan kau abunda yakawota kenan amma bata labari itada komen gidan Amadu har abada badan kunyar ubanki da uwarkiba da uku zansaka yai maki ringis amma biyunma ba laifi kije ta isa .

Yau dai yakamata nafara daukar mataki kan iskanci da Hafsat kemun .

Cikin tafiyar isa da takama na ida isa gunsu na kallesu nai dariyai manya masu hankali nace .

Hafsat kenan akafada maki nayi takaicin barin gidan Amadu ne ?
Barina gidan Amadu tamkar samun damar shiya aljannai duniyane .

Kedai da kika gama bashi kanki a titi yagama sissikeki kije kita kaya.

Nasake gyara tsayuwata .🚶🏻‍♀

Atunaninki ke kadai Amadu ke bi Hafsat 💁🏻
Idan kinada wannan tunanin kiyi gaggawan ajesa dan Amadu karuwansa yawane dasu kece dai yaga yakamata yakawo danki cigaba da tarbai masasu idan yakawo. Ina tayaki murna🤝🏻

Najuya gun Inna datai mukus dan bata taba ganin namaida maganaba kona bata rai koda yaushe cikin kuka da damuwa nake a tsorace kamar bera yaga mage 😁

Inna ke tsohuwace bazan iya zakinkiba ko aibatakiba amma nasani kin janyo wadda wata ran zatai maki mugun duka harta jaki waje danda kike takama yadawo yarufe ki dafadan kin cika shiga sabgar yara .
Indai muna da rai zaki tuna hakan .

Kaf sunyi kasake suna kallona suna raba idanuwa koban fadaba Hafsat nasan maganar matan Amadu ceta razanata.
Ita kuma inna maganar sakayyai da Hafsat zataimata take tunani.

Nabarku lafiya .

Amarya kigaida Angonki.
Innarmu nabarki lafiya .

Najuya na nufi dakin uncle danagani bude sai dai me zan gani ni Huwailat 😱







To kubiy Haupha danjin meta gani din😁😜

Sosai da sosai nakejin dadin yanda kuketa yabon book dinnan kuna sambadamun addu o inku masu daraja Allah dai yabiya yabar kauna.

Bawulakanci bane yasa bana kula masu turamin text wallahi kunsan idan dambu yai yawa baijin mai 😂😂

Amma wallahi ina son duk mai sonah

Haupha nkuce💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

DA AURENAWhere stories live. Discover now