DA AURENA page 15

816 51 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452

Page 15












Dandanan naji kukana ya koma xuciyata na xafi kaina nacigaba da sarawa na koma kan gadon na kwantsa sharaf

Kiyi kuka kibude bakinki kiyi kukanki matar
Kada kimaida hawayenki kukanki samun saukin xuciyarkine
Wani marayen kuka nasaki uncle mike shirin faruwa da rayuwatane
Uncle ina xansaka kaina naji sauki
Tabbas banda sauran gata ko yanci naxama tamkar baiwa baiwarma marai yanci agun ubangidanta

Sosai muketa kuka nida uncle Wanda nidashi baka banbance Wanda yafijin kuna a xuciyarsa

Wasa wasa saida nashafe kwana uku kwance ba Amadu ba yan gidanmu sannan ba Innarsu Amadu dagani sai uncle Wanda nakeda tabbacin cikin masallacin asibitin yake kwana
Yau Likita ya sallamemi Wanda araina jinake xaman asibitin yafimun xaman gidan Amadu Dan koda yaushe Uncle kokari yake yaga yasani dariya
Wata shaquwace ta qara ratsa xukatanmu a cikin kwana ukunnan
Tunda yafara hada yan kayanmu nafara hawayen takaici
Da ace inada gata da yanxu gidanmu xan koma
Kai da mamace xatayi jinyatama ba waniba amma ina bansan minayi da xafi hakaba suka juyamin baya sukaimun kashe da xuwa gidansu ohh ni Huwailat naga takaina

Bakiga ta kankiba Matar kinada ni nayi alkawarin xama jigo a rayuwarki
Baxan taba baki damar xubar hawayen bakin ciki ba indai ina tare dake Matar sai dai kiyi kukan dadi

Inama wadannan kalaman daga Amadu suke fitowa
Inama Amadu namun kwatankwacin abunda uncle kemun

Karki damu akwai lokaci

Cikin jin kunyar subutar bakin danai na sadda kaina kasa

Tashi muje mai mota najiranmu pls
Haka muka taho inata sake saken matakin daxan dauka kan Amadu

Kofar gidansu Amadu naga mun tsaya na juyo na kalli uncle yai murmushi yace yana da kyau kije ki gaidata tunda hakan ya faskara daga gareta
Badannasoba nakutsa kaina cikin gidan
Inna naxaune tana cin Abincinta Redio nagefenta natayi nayi sallama tunda tadago taganice ta kauda kanta ta tattaro bakin rai ya yafama fuskanta
Ahankali nadubi uncle dake gefena ya girgixamun kai
Jikina sanyi kalau na ida isa na tsugunna Inna ina kwana
Tai banxa dani
Innarmu ana gaidaki fadan uncle kenan

Tawani tabe baki au sarakan kishine tafe gidannawa

Hawaye suka nemi xubomin uncle yai mun alamar karna fara
Nadaure na maidasu
Yanxu ke Huwailatu Ashe daman baki da wayau bakisan makanwacin takashinkiba Ashe
Nidai kaina kasa xan magana kenan saiga Amadu

Auh kenan dai da gaske ban isanba kamar yanda kika fadamin nace kibari naxo muje gida tunda kin matsa a sallameki shine kikace baki so nan kike son xuwa waini Huwailat yaushe xaki aminta danine

Caraf Inna ta amshe
To datace nan xataxo uwarmi xataimun kota daukarmin a gida
Koko nima haukan kishin naki xaki gwadaminne har gida
Ahhh lallai naki abun aximunne yarinya kina tare da wahala uwarki bata dauraki kan hanya madaidaiciyaba
Tunkan ranki ya baci maxa kibarmun gidana Ai duk Wanda baison naka kaike beso

Gaxa daure kukana nayi dole nabasa damar fitowa Dan kiransa akai
Cikin tausayin kaina na nufi kofar gida ko gani sosai banayi sama sama nake jiyo masifar inna tana sai dai ciki uwaki ko ubanki wannan kukan badai Danaba

Allah ne kawai yakaini gidan Ashe Amadu na bayana yasa keys ya budemin yanata murmushi kamar anbiya masa Makkah
Kan gadona nafada takaici kamar xai sukeni
Kamar mahaukaciya nafara hada kayana xanje gidanmu ko Baba ya koreni Mama xata riqeni

Wata matsiyar dariya ya kwashe da ita
Huwailat kenan kokinje koroki xasuyi Dan tun randa nakaiki asibiti nawuce gidan nafada masu kin xubarmun da ciki da gangan wai baki sonah
Sako mai kyau mamarki taban bata baki duk randa kika kashe aurenki
Maganar gaskiya baxan yarda ki hadani da kowaba Huwailat xakiyi xaman qunci a gidana xan dandana maki duk wani bakin ciki da kikejin labari yaja tsaki ya fice

Turus yai Dan ido biyu yai da Yusuf yanata hawaye

Yaya kaji tsoron Allah kasani idanka cuci yarinyar nan kaima duk ba dade duk bajima sai ansamu Wanda yaima mafiyinsa sannan ga hakki Dan Allah bai yafe hakkin wani kan wani

Yaya dakaci gaba da ganama yarinya axaba mixai hana ka saketa takama tsaginta ka huta ta huta
Yaya duk abunda kake mata baimaba saida ka hadata da iyayenta sannan ka kara da inna
Shin miye ribarka a hakan dakayi

Yusuf yaushe nafara wasa da kai da har xaka tsareni da surutun banxa

Inasan naima gargadi na karshe kagani kaki gani inba hakaba ranka xai baci sosai

Tunda suka fara magana naji duk duniya banda kamar   uncle tunda shine kawai yasan damuwata shine kemun uxuri kan komi shine ke lallabani yanason yaga fara ata koda wasa baisan ganina a damuwa
Wani qimarsa da girmansa suka dinga ratsa dukkan gabban jikina

Bayan sati

Amadu ya kyalla ido yaga nafara sallah gashi ba laifi nadan ciko Dan kullum cikin sayomin nama da lemu mai sanyi ko kaxata haka xan ci iyakar cikina nabar sauran
Haka Amadu xaixo yadau sauran ya cinye tas baitaba tambayata ina nasamesuba haka xaiga sabbin kaya amma bai taba tambayata ina nasamesuba
Tun abun nadamuna har yadaina sai dai naima uncle korafi yace toke ina ruwanki karya tambaya man saime

Zamana da Amadu bai sake xani ba saima qarin abubuwa nice wankinsa gugarsa da goge takalmansa
Agefe guda kuma yasamu yancinsa gabana xaikira yarinya suita hiran batsa banjin ko dass Dan yanda natsanesa ko gabana xanga ya taushe mace ko a jikinah xanji

Sai dai Allah yasani ina matuqar kyamarsa duk sanda yai amfani dani sai nayi kuka naji haushin kaina sosai

Wata uku cif da xubewar cikina nashirya nace ma Amadu xani gidanmu Dan haryau banga kowaba a cikinsu nasha ciwona na gama
Dariya ya tuntsire da ita kibari sai jibi kinje yaune ranai xuwana cin nadare da tsohon nan dabai ganewa
Damm gabana yafadi yaushe Amadu kayi kwarin daxaka xagi mahaifina gabana
Wannan ba abun damuwa bane guna yarabani xai fice natare kofar yau inasan Dan Allah kafadan miyasa ka aureni bayan baka sona miyasa ka killaceni gidanka kana ganamun axaba wane laifi naima mai girma hakan

Yau xanfada maki gaskiyar lamari

Baninace ina sonkiba har gida aka kaimun tallaiki tare da jari mai tsoka ke harma da wannan gidan damuke ciki

Cikin kuka nace Kaka kacuceni kagama dani dakaimun wannan xabin tumun Daren

Dariya yasake aiba wannan tsohon bKauna


YAYAN MATACCEN SAURAYINKINE SULEIMAN*  cikin kaduwa nace daman yah Suleiman yaturoka gidanmu Dan kawai anmaida auren Habeeb kansa

Tunda anci sa a kinada ganewa bari kiji yanda akai komi

To masu karatu yaya abun yakene

Da gaske sulaim yakaimasa tallai Huwailat koko dai kullin Amadu yabiyo takansane

Taku dai Haupha

Gaskiya inajin dadin yanda kuketa yaba labarin nan wasu ta comments wasu ta waya suke kirana ina godiya sosai Allah yabar Kauna
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

07081095452
Nagode

DA AURENAWhere stories live. Discover now