Talla-----Talla

457 16 2
                                    

KISA KO AURE ?

      NA

Hawwa'u Salisu (Haupha)

Talla ce wannan gare ku masu buƙatar littattafaina.


Kotun ta cika maƙil, cikar da ta jima batayi irinta ba, ko da yake ba abin mamaki bane idan mukai duba ga shari'ar da ake yi a cikin kotun, wanda wasu mata uku reras suka kashe mazajensu har lahira.

Sai dai shari'ar Rahma da marigayin mijinta Rahim tafi ba kowa al'ajabi da mamaki, domin yau shine zama na uku da akai amma Rahma bata taɓa magana ba, duk tambayar da za ai mata da manyan idanuwanta take bin mutanen gun tare da Alƙalin, wani abu daya ɗaure ma mutane kai da Rahma shine bata taɓa zubar hawayenta ba tunda aka kamota aka fara shari'ar .

"Awwal dan Allah ka taimaka mun ka aure ni saboda kai ne kawai wanda kasa na kashe aurena, kaine ka bani ƙwarin gwiwar da na addabi mijina na wulaƙanta shi naci amanarsa duk dan ka tabbatar mun da cewar zaka aureni ne Awwal."

Wani banzan kallo ya watsa mata, kafin ya ƙara haɗe fuskarsa yace "Hadiza ke yanzu ko wani yazo ya gayamaki cewar ni Awwal nace zan aureki zaki yarda ashe ? To bari kiji ni bazan iya auren ƴar iska ba,gantalalliya marar godiya irinki ba." Mtss yaja tsaki ya wuce ta wurin tsaye zuciyarta na kaiwa da komowa.

"Haƙiƙa yau ba sai gobe ba, zan kashe mijina! Tabbas sai na kashe shi ! Wasu hawaye suka zubo mata masu zafin gaske, bata damu da gogewa ba.

"Ke akan kawai nayi ma ƴar cikina fyaɗe ta mutu zaki tasani gaba kina mun wani wa'azin banza da wofi ? To ki sani ba Husna bace ta farko ba ita ce ta cas'in da takwas saura biyu nake buƙatar samu na yi masu fyaɗen na kashe su, to burina ya cika kuma abin da nake nema zai samu cikin sauƙi."

Kallon gawar yarinyar take gabanta cikin wani yanayi wanda ba wanda ya isa ya fassara ainihin abin da ke ranta.

Kowa jikinsa yayi sanyi a gun sai kuka suke suna girgiza kawuna kamar wasu ƙadangaru.

Cikin ɗaga murya tace "Ni ce na kashe shi ! Tabbas nice na kashe Rahim kuma banyi nadamar kisan ba, na rantse da Allah idan yanzu Rahim ya dawo duniya sai na sake kashe shi !

Sai kotu ta ɓarke da hayani, kowa da abin da yake cewa .

Alƙali ya dubeta yace "Rahma ko zamu iya jin dalilinki na kashe mijinki Rahim ?

Dariya ta fashe da ita mai amsa kuwwa tace "KISAN KO AUREN WANE ZA A FASA ?

Gamai bukatar jin wannan cakwakiya zai iya biyan kuɗi naira ₦200 kacal ta wannan account 3121773501 Hawwa'u Salisu first bank .

Idan kuma ta katin waya ne zaku iya turowa ta wannan number tare da shaidar turowa ta WhatsApp 07081095452.

Haupha ce ✍🏻

DA AURENAWhere stories live. Discover now