DA AURENA page 93__94

767 37 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452


*Wayyo Allah , da gaske mura ta dameni yakamata kui zanga zangar min Addu'a inba hakaba na dage typing din sai karshen shekara 😎😎😎*


'''Wannan page kyautane ga Prince na Princess dinsa Allah yabar kauna da Amana tsakani Ameen'''



Page 93 94



Cikin dari dari suka nufi cikin gidan hankalinsu tashe dan basusan abunda zasu iskeba .

Umma da ke zaune tanajiran taga bakinda Hassan ya fada zasu shigo ta gansu hajaran majaran dan saurayinne kawai keda kyan gani .dan haka ta dauka neman taimako suka zo .

Kasancewarta ba mai wulakanta mutaneba ta tarbesu fuska a sake hakan yakara masu kwarin gwiya sosai .

Bayan gaisuwa sukai tsit da kunya su fadi tarin abun kunyar da suka aikata .
Umma ganin shirun nasu yai yawa ta dubi uncle dake da kyan gani tace ,,Bangane kuba samari ,

Gyaran murya yayi ya nuna inna yace ,,kiyi mata bayani .

Cikin matukar nadama inna takwashe komi ta fada mata .

Bata bari ta gama fadaba tace ina zuwa ta dauki waya takira mai gidan da Hassan gabansu ya kamata ai wannan maganar tafi karfin kunnueanta ita kadai .

Basu wani jimaba suka shigo Hassan sai wani ciccijewa yake yana kara bata rai .

Umma dariya tai mai hali bai canza halinsa shidai haka yake ba fara'a .
Bayan sun zauna inna ta sake maimaito labarinta tundaga farko har karshe .

Ba Wanda ya ankara da tashinsa sai gani sukai ya rufe Hafsat da wani bala'in duka tako ina .
Abun mamaki yaba uncle yaro karami da bakar zuciya dukanta yake ba wani magana da yake tamkar kurma haka ya koma .
Saida suka tabbatar da yai mata dukan ladabin gaske sannan Alh ya janyesa idanuwansa jajir ya kalli inna ,,wallahi ki godema Allah banine na iske dan iskan dankiba da wannan cikakkiyar marai mutuncinba , danine tsab zan nakasa masa rayuwa yanda zai mutuwar tsaye shegen .

Alh ya janyosa jikinsa ya shiga bubbuga bayansa dan yasan halin bakar zuciyar yaron sarai .

Umma dai kasa magana tayi dan fadan yafi karfinta .

Da kyal dai Alh ya kashe rigimar ya fiddo waya yakira major

,,salamu alaikum

Major ,, wslm Abba barka da warhaka

Alh,, wane yarone kake neman kashewa gunka ?

Major ,,Abba ba kowa wani abune ?

Alh ,,bansan shirme ina nufin Amadu

Major ,,Abba Amadun da yaci amanar Huwailat da iyayenta kake magana ?

Alh ,,daman kasani kasani wahala ?
To maza ka sakoshi mota yadawo gida .

Major ,,Abba dakun barshi ya gane kuransa da kyau

Alh ,,nagama magana kasako yadawo gida .yakashe wayai

Sosai su inna sukai godiya suka tafi Hassan nata mazurai  jiyake tamkar ya shake tsohuwar guzumar canma amma zai nemi gidansu dole ya daukarma Auntynsa Fansa komi zai faru ya faru .

DA AURENAWhere stories live. Discover now