DA AURENA page 43__44

719 37 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452

Wannan page kyautane gareki daga kungiyar kainuwa writers sukace sunji dadin kirarin da kikai mana dan haka wannan page nakine ke kadai kiyi yanda kikeso dashi  *SISTER UMMI TANDAMA*   Allah yabar kauna .

Duk mai son kainuwa dashe Allah namune muma munayinsa over over wallahi 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Page 43 44

Zaune yake yasaka saka kafafuwansa cikin swimming pool yanata zukar karan taba ba kakkautawa gefensa tarin takardune barbaje . idanuwansa sun kada sunyi jawur sosai yake jin ciwo a kasan ransa .

Yakasa manta yarinyai .
Sosai yake jin kaunarta duk dadewar da yai baije  ganin gidaba dan kada yaje ya iske yarinyai nada Aure ne.
Sosai yake mamakin kansa yanda wai shine da kansa yaba wani damar aurenta bayan damar gareshi take.

Sosai yake hango randa yaje yaci mata mutunci wanda hakan ba halinsa bane yarasa yanda akai yaimata hakan .

Takarda daya ya bude.

'''Inafatan duk randa kika zama matata kikasance tamkar sarauniyar da tafi kowace sarauniya .
Fatana ace dakin fito ki banbanta da kowa hakan zaisani farin ciki sosai'''

Ahankali ya aje later  .

Dole nacikama alkawarinka Brother koda zan badda duk Wanda yashiga lamarina kan cika burina .

Sir

Cikin yangarsa ya juyo captain Ahmad na magana .

Banfada maku idan ina nazari kudaina damunaba kowaye yazo?

Sorry sir

,,U are vary stupid . yajuya yaci gaba da bankar tabarsa.

Kowa nagun yasan idan ya zauna agun bai bukatar hayaniya dan haka kowa ke shakkarsa .

Uncle 
Uncle
Uncle

Kazo Daddy nakiranka yanzu wata kila tasamu inji maryam .

,,Banhanaki guduba inkina tafiya ba . inji mama dake zaune tana duba jarida.

Sorry mama kinsan inasan duk abunda zaisa uncle farin ciki ne.

,,Wai yaushe yazama uncle dinki ne.

Dariya tayi ,,inafa taya sis fadane mama.

,,yana dakinsa inaga tafiya zaiyi yau ko gobe wai anata kiransa .
Yafadan mama nasan sallamaisa zaiyi kinsan Daddy baisan jira .

Kwance yake yana son yasamu damar dazai ga Pretty dan yaimata sallama sannan yai mata wayau yanda bazata kwabsa masaba koda bainan.

Wata dubara ta fado masa . ayam tafado tana kwada masa kira ,,yah kazo . auh🙊 Uncle .
Dariya yai ya bude mata hannu tafada kansa ya sauke ajiyar zuciya .
,, my Angle koda yaushe jinki nake kina yawo a cikin jinin jikina sonki ba karya bane a zuciyataba na kagara na hada karatuna nadawo a mallakaminke kodan nasamu kwanciyar hankali .
Lub tayi tana sauraran dada dan kalamansa dake kara rura wutal kaunarsa a zuciyarta.

,,Fatana koda yaushe Allah yarabaki da son karya. Kigane nine kawai mai kaunarki da zuciya daya .

My Angle yakirata da wani murya mai bin jikin masoya .
,,inasan kimun alkawarin bayan bannan bazaki taba barin Pretty tagane nine zan aurekiba dan bazata nake son muyi mata hakan zai burgeta sosai .

Taci gaba da shafa kirjinsa karka damu yah komi kace haka za ayi nima zanso naga sis a bazatarnan kau.

,,Lahh yah Daddy ke kirankafa namanta ina ganinka na manta kowa da komi .

Dan dungure mata kai yayi ,,ba ruwana idan yayi fada kece .

Shagwabe fuska tayi zata saka kuka . sanin hali yasa ya lallasheta yace idan yadawo ta turomai pretty zai magana da ita sui bankwana yaji ko tanada wata matsala da zaman gidan.

OK yah saika fito .

Zaune ya iske Daddyn yana juya wani kwalin waya sabo dal a hannunsa .

,,Daddy barka da hutawa .

Yauwa Son duba wannan wayai kagani tayi ?

Cikin mamaki ya ansa dan bashike sai masu wayaba kudin kawai yakebasu .

,,sosai matayi Daddy yana mika masa wayan .

Barta gunka Huwailat nasiyo ma ita maryam tace batada waya.

Allah ya saka da alkhairi Daddy yanzu zan kaimata kuwa saimuyi bankwana .

Kai yaune zaka tafiko ?
Shaf na shafa a ta Huwailat kawai nake naga ta samu farin ciki kota iya mota kuwa ?

Nace banda sakin layifa Daddy🤣

,,Bata tuki da kanta gaskiya tukata ake Daddy.   

Su uncle ma an sharota😜

To to ba damuwa nace ko siyayyai tayi mata kyau kuwa ta rannan din.

,,Sosaima Daddy dan baka gari muka dawo daka shaida yanda tai murna .
,,yayi kyau sakonka naturama ta acct sainace Allah ya kiyaye hanya .

Cikin farin cikin pretty tasamu wayai dazasu dinga chat yakoma dakinsa.
Number Angle dinsa yakira kituromin pretty ya kashe wayan irintasan ba wasa dinnan☺

Huwailat tagama shiryawa kenan cikin riga da wando masu masifar kyau ga gashinta dayasha gyara sosai yasamu masauki a kafadunta ya kwanta kaika rantse da Allah daga ketaren kasa tazo ziyara.😎

Masha Allah sis kije uncle nakiranki tafiya xaiyi yau.

Daram gabana yafadi duk da bamuda sakewa amma duk yamma muna satar jiki muje garden din gidan musha love .

Cikin sanyin jiki najawo hijab dina nasaka bance kalaba nafita na nufi dakin uncle .

Cikin tafiyarta ta yanga ta shiga tare da sallama .

Kallonta kawai yake karshe yafashe da kuka .

Sosai jikinta yai sanyi uncle na matukar kaunarta sosai yake mata son gaskiya .
Ahankali ta isa gabansa ta sadda kanta kasa.

Nayima alkarin nunama soyayyai da baduk wani namiji zai sametaba  uncle kariga kagama kama zuciyata sonka yana  kara ninkuwa a koda yaushe .

Cikin zubar da kwallah ya kama hannayenta

,,Kimun alkawarin duk rintsi kina tare dani bazaki gujeminba .
Idankika gujemin tabbas zan shiga tashin hankali na bugawa a jarida.
Pretty wallahi idan kika juyamin baya bansan inda zan jefa kainaba.

Pls pretty kirike alkawarinmu dan Allah

Cikin kuka ta rike hannuwansa gam itama

,, Uncle dan Allah kadaina maganar rabuwa nidakai har abada muna tare .

Naji dadi sosai pretty  but inason kimun kokarin boye soyayyaimu dan sonake saikin kafu a zukatan mutanen gidan saina fito da bukatar aurenki nasan bamai musawa

Kuyi hkr ba caji👏🏻👏🏻

DA AURENAWhere stories live. Discover now