DA AURENA page 16

811 47 1
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452

Page 16






Wannan page kyautane gareki Ummu Hafsy ( jikaleta ) 🤣🤣🤣🤣🤣🤣

Zaman dirshan nayi inajiran Amadu yaimun bayanin yanda aka kaimasa tallai Aurena
Cikin ko inkula yace

Dakika ganni nan banda aikin fari kona baki kullum xaune nake kan dakalin kofar gidansu Habeeb nida wani Abokina Hayatu Dan anguwarkune

Kullum ina ganinki idan xaki wuce makaranta harna fara tambayar abokina waccen ko xasu bani ita na afka ciki
Ya tuntsire da dariya yace amma hauka kake ko Amadu insun baka ita dame xaka cidata sannan inama xaka ajeta

Gidanmu xan toshe dakin Innata daya saina ajeta dayan

Aikuwa karma kasa rai Dan waccen tafi karfinka ba ajinkabace

Raina sosai yabaci Dan aganina baikamata ace akankiba anamun gorin matsayiba
Harkuka fara soyayyah da wancan Banxan Habeeb din duk akan idona saidai aduk sanda naganki dashi sainaji bakin ciki Dan tunda Hayatu yafadan wai kinfi karfina nake fatan ki auri irina koma Wanda baikainiba wato jahilin gaske danni nasamu takardai secondary school

Kullum saimun fada da Hayatu kan yanda yake yaba halayenki ga yan uwanki nakula na masifar sonki komi cikin nasara kike yinsa nikuma hakan namatuqar batamun rai banjin dadi ko kadan
kwatsam Hayatu yafadan ansaka ranai Aurenki da Habeeb ranai ban iyacin komiba Dan bakin cikin danake maki na samun Habeeb Dan kowa ya shaidesa sannan xaki huta uwa uba yanda ya mace kanki sakaran
nai duk yanda xan danganin na hadaku da Habeeb amma ina hakan yaki faruwa Dan haka na hakura badan raina yasoba amma sau dubu naganki sainaji haushinki a xuciyata
Bakaramin dadi najiba da nasamu labarin macewar Habeeb dinkiba Dan haka nafara shirin shigowa rayuwaiki takowane hali Dan kawai na gwadama Hayatu nima ba kanwai lasabane amma kash nasamu labarin an maida Aurenki kan Suleiman sojan nan dafari naji dadi Dan nasan can xaita jibgarki yana saki wahala saikuma natuna ai xakici mai kyau kisha mai kyau kilan wata ranama ki samu xaman lafiya dashi Dan naga yana sonki baija ba da aka lika masa Aurenba
Gama wannan tunanin yasakani naje gun wani Gardi ( malaman xaure) abokina nafada masa damuwata
yace kaikaso tun farko akama saka Aurenta da mataccen amma koyanxu inkaso komi xai sauya
Cikin farin ciki nace yataimakamun yaimun mai xafi Wanda saima nasamu alkhairi sannan xan sameki a gabas
Haka kuwa akayi yaban wasu layu yace nai kokari nasaka inda Suleiman din xai wuce yaban wani goro yace na tabbatar tsohon kakanki ya cinye to nakoma gida naita barci
Cikin sauqi Suleiman yataka layar inaganinsa yadafe kansa yai hanyar gidanku ina labe kika fito nine na aika akaimun sallama da yayanki Abba Dan aikomi gabansa inbaki mantaba kin fada kan mutum to nine ai Wanda kika fada kansa
Cikin mamaki nakara kallonsa yace kwarai gun matsiyacin kakanki nasamu matsala Dan da qyal yaci goron nan sannan nakoma gida nafara fafutukar yanda xan Dade dakin innata daya nabar maki dayan
Da dare akai sallama dani nafito naga Suleiman muka gaisa yace alfarma naxo nema gunka Dan inaji a jikina Kaine kawai xaka iyamun ita nadubesa nace wace alfarma kenan ranka ya dade
Yace inada wata qanwa to sonake tai Aure vary soon Dan haka na xaba mata kai Dan Allah karka ban matsala nasan kanada Amana daganinka daxun xuciyata keta axaxxalata naxo gareka da buqatata

Nai dariyar nasara nace dafari ina godiya Sai dai banda halin Aure ni Dan banda muhalli da abunda xan riqe kanwarka kagaba xan anshi wannan tayi nakaba
Yace karka damu indan wannan akwai wani Dan gida qarami Dana siya sainabaka tare da jarin fatana kariqe Amanarta naita masa godiya mukaje naga wannan gida damuke ciki yanxu yabanshi kyauta da kyautar kudi masu tsoka
Haka bamsamu damuwa da kakankiba Dan shima nagama dashi naje asuffar Dan Abokinsa
Shine yaimun tsaye har  akai wannan Aure
Ya kwashe da dariya kamar mahaukaci kinji yanda akai na Aureki ba sonki nakeba

Harkai mata kuwa da abuna kika ganni tunda Suleiman yaban kudin jarina nafara kasuwancina nahada mata kuma abun ba a magana Dan saidai inban taya yarinyaba
Haduwata da kawaiki Hafsat kuwa wata rana ne Dana ce kije gidansu wasilat to aranai nakawo Hafsat nan gidan banwani sha wahalai shawo kantaba daga ranai duk sanda naso muna tare da ita har xuwa yau danake maki magana ina tare da ita danta kware da iya harkai
Kuka ya kwacemun sosai nace nabarka da Allah shine xaisakamun

Aiban gamaba kwana kadan aikin Suleiman yanemi warwarewa yafara bin ubanki da magiyar yana sonki Dan haka nasa akai masa aikin dayabar qasarnan gaba daya
  kai lallai nacika jarumi wallahi bana Neman abuna rasa nidakike gani dama xaki taimakamun dakinje gun Hafsat kince ta Aureni Dan ana hutawa da yarinyai ba karya

Innalillahi wa inna ilaihirraji un

Amma dai anyi mugun yaro anan amma akwai Allah shine xai sakamata duk abunda kaimata
Maganar Kakana kawai mukaji Alhaji Mamuda cikin kuka na rungumesa ina kaka kaji ko kaji abunda Amadu ya aikatamun kaka minaimasa

Kaka yafara shafa kaina yace kiyi hakuri nima yaronnan Yusuf shine yace naxo baki lafiya Ashe rabon naji komine to insha Allahu Sai ya sakeki tunda ba xaman dadi kikeba

Wata dariya ya kwashe da ita yadubi kaka yace ai kamakaro Dan nariga nashige gabanku kaf garinnan babu Wanda ya isa yarabani da Huwailat xan saki Huwailat amma saita xama abun kwatance ta xama mabaraciya taxama abar kyama sannan xan sallameta
Takamarka iyayenta to gaba dayansu Sai yanda nayi dasu atakaicema nasa anmantar dasu ita tsanarta ce kawai ke yawo a xukatansu kaima ga fili ga mai doki nan yasa kai yafice yadawo kitabbatar kin wankemun kayana da kyau kin goge Dan fira xani dasu

Tsoho agaida tsohuwa yawuce abunsa yabarmu daskare agun

Tofa yaya kenan xata kaya ne

Wane mataki kaka xai dauka kenan akan Amadu

Yaya maganar Suleiman kenan da akaima kurciya

Duk kubiyoni Haupha danjin amsarku

Godiya gareku masoyan Book din da Aurenah ban iya jeroku Dana ambaci sunayenku amma kunsan kanku daku nake 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻❤

Nagode

DA AURENAWhere stories live. Discover now