DA AURENA page 17

765 33 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452

Page 17

Kasa magana kaka yayi sai Uncle ne yasamu damar debo ruwa masu sanyi yaban kisha matar kina furta innalillahi wa inna ilaihirra un

Hasbunallahu wani imal wakim

Xakiji sassauci ko yayane a xuciyarki

Kitsananta addu a  Allah maji roqon bawan sane tabbas kina cikin jarabawai ubangiji madaukakiya wata rana sai dai inkin tuna kiyi dariya insha Allahu
Kaka dayaimun quri yace mi mahaifinnaki yace dayazo gunki can asibitin
Cikin kuka na maimata masa abunda Baba yace ya girgiza kai kada kiyi wasa da addu a tabbas komi zaizo karshe daga nan can gidannaku zan nufa Allah ka shirya Amadu

Cikin tashin hankali kaka yatafi yabarni inata kuka Uncle na aikin lallashina karshe saida naga ransa ya baci sannan nayi shiru na koma na zuciya

Aranai uncle yaimana sanwar abinci badan dadiba naci sai Dan nasan idan banciba uncle baxaiji dadiba dole nadinga tusa abincin Dan farin cikin uncle

Kije kiyi wanka zanje na dawo zamuyi wata magana dake Matar

Kaina kawai nadaga masa Dan magana wahala takemun yanzu
Yauwa yakamata kimanta da komi ki rungumi wayarki Dan nakula tanasaki nishadi kobaki da katine

Saurin girgiza kaina nayi danna tunada mutunina koyaya zaiji kwana biyu bani online Allah kasa ya manta dani a lamurransa
Sainaga kamar kina tunani Matar daga maganar ki kunna wayarki lafiya daiko
Nace lafiya lau ba wata damuwa ina tunanin indama na jefar da wayanne
Kiduba tana nan dakinki ina zata

Bayan dana fito wanka naga yakamata na leka group dinmu naji me suke toyawa da bana nan sannan yanada kyau na nemi shawaransu kan zaman Aurena da Amadu harma da kawancena da Hafsat
Na am nayi da wannan shawarai da zuciyata tabani najawo wayata na kunna abun mamaki karan cajina ko daya bai saukaba na kunna data na fara bincikar massage da akaimun

Hafsat naga ta turomin

Kiyi hakuri Huwai zuciyace tajani ga aikata maki hakan sainaga kamar bazaki damuba tunda ba son Amadun kikeba amma naga kindau abun da zafi hadasu suma to Allah yabaki hakuri matar Amadu

Wasu hawaye suka tsiyayomin kawai nasaka kuka a fili
Na daure na bude na Zainab
Huwailat kwana biyu kina cikin raina Dan haka na matsama Abban khady yakawoni gidanki amma bakinan sai Hafsat na iske da Amadu waitana maki girkine baki lafiya kina asibiti

Huwai nidake da Hafsat tare muka tashi tun yarinta amma bazan baki shawaran sakarma Hafsat akalai gidankiba saboda su maza tamkar kitse suke dasunji rana narkewa suke duk daskarewarsu
Dan haka kikula Allah yabaki lafiya

Wani matsiyacin kuka yasake kamani wato inama kwance saida Hafsat tadawo gidana kenan ohh ni Huwailat yaya zanyi da wannan Aure nawa

Nikam nace hakuri zakiyi 🤷🏻‍♀

Ina cikin kukan zainab tasake mun magana ashema tana online

Amaryai Amadu ya jikin naki

Cikin kuka na latsa voice massage nace
Zainab Ina cikin tashin hankali da damuwa

Hafsat ta yaudareni ta ha inceni Da Aurenah taci amanata

Bansan mezance makiba amma Hafsat tagama dani banzaci hakan daga garetaba
Acikin gidan Aurenah da mijina na iske Hafsat na shaidana da Amadu
Zainab wace kalan kawace Hafsat

Nai mata forward na massage din da Hafsat tayomin

Ba a jimaba ta maidomin voice

Nabude

Wani uban ashar ne ta lailayo ta makama Hafsat
Maza maza ki share hawayenki yanzu yanzu zanzo muje gidansu shegiya
Ai walahi bazaki barta haka babu hukunciba yazama dole mudauki mataki kanta
Ganinan zuwa ko bainan kizama ready Allah saikinje inyadawo yabaki takardaiki tafi nono fari
Keni da Allah zaisama na iskesa gidan ba abunda zaihanani cimasa mutunci
Saikinzo na maida mata replay

Yunkurawai dazan muka hada ido da uncle duk abunda muka tattauna akan idonsa ashe na sadda kaina kasa da wahala yabarni naje Dan baida son rigima uncle sanyin haline dashi
Yakamata kisani shi sure konace rayuwai aure dole saida sirri banso kizama daya daga matanda komi na gidan aurensu ke bankade Matar

Amma yanada kyau konace ba laifi bane inkika ware kawaiki guda daya dazaku dinga tattauna damuwarki amma kikula mutane basu da amana
Bazan hanaki zuwa gidansu Hafsat ba saidai inasan inkunje kada kiyi hauka ko zage zage kitanadi kalamanki masu ma ana kifadamata wadanda zasu nutsar da zuciyarta harma da Wanda ke kusa da ita shawarata kenan ya tashi yabar gidan
Inagama shiryawa Zainab nazuwa har yanzu da sauran masifar a fuskaita muka rankaya gidansu Hafsat

Sai daime muna shan kwanai gidan muka hango Mashindin Amadu dauke da Hafsat sunbar anguwar zubewa nayi agun nafasa kuka
Zainab datai suman tsaye ga uban ciki taja hannuna muka shiga gidan batareda na daina kukanba
Mamarsu mai mutunci ta taso ta taremu da fara aita ganin kuka nake tafara tambayai lafiya
Cikin yan mintuna Zainab ta koramata bayanin halinda ake ciki
Baiwar Allah zubewa kawai mukaga tayi cikin yayyenta wani ya zuba mata ruwa ta farfado tana kuka tana zainab ba Huwailat kika cutaba kanki kika cuta ba ita kika ha intaba kanki kika ha inta tabbas sai Allah yasakama yarinya Allah kai gaggawai tsine.. Cikin kuka natoshe mata baki a a mama kada ki twine mata kaddaratace hakan nagodewa Allah
Zainab dai nata cika tana batsewa ta jawoni zomuje nasan suna gidanki tunda batada kunya yaukuwa ba abunda zai hanani faskarama yar iska faskare ga kai
Mamarsu ta dubi yayansu tace maza kaje duk inda take ka kawomin ita a sume yar banzar dabatasan darajai amintakaba
Kullum mijinki zaizo yace baki lafiya taje taimaki girki sanin bakida kanwa mace babba yasa nake barinta ashe tsiyar dasuke kenan

Haka muka baro gidan mamarta nata mita tana mata mugun baki mukai gidan Zainab
Sai dai muna zuwa dai dai wani shagon saida kayan makulace mukaga gungun mutane sun yayyabe anata ban hakuri
Harzamu wuce zainab tace kamar motar Abban khady can muje muga meke faruwa

Muna kutsawa na hango ......take idanuna suka fito na dake kaina dake neman tsagewa

Kubiyo Haupha Dan jin mike faruwa ne gun

Bazan daina godiya garekuba masoyanah 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Nagode

DA AURENAWhere stories live. Discover now