DA AURENAH Page 4

1.3K 70 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociationkainuwawritersassociation

07081095452

Page 4

Kullum na wuce sai nadan dakata naga ko Habeeb xai tsaidani yafadamun abunda yake boyewa amma ina baitaba hakanba wasa wasa naji kaunarsa sosai a raina
Ran wata talata danaje islamiyya nida kawayena ana maganar samari nikam murmushi kawai Nike Dan banda tacewa
Hafsat ta kalleni Huwai anya kuwa babu magana bakinki naga kinata murmushi
Bakomi kawai dai tare suka dau ihu inkunji Huwai tace kawai dai to akwai maganganu bama dayaba
Zainab tace kawai kifada mana muji abunda ke faruwa
Sanin bama boyema juna damuwa nafada masu komi akan nida Habeeb yan iskan tare suka saka ihu wlh kundace inji Hafsat
Akwai yanda xa ai Habeeb ya furta maki kalmai so kobaiso Huwai cikin murna da jin  Haushin sunan da suke kirana nace tayaya kenan Zainab
Tayanda dole ya furta inkuma ba sonki yakeba xamu gane saimu sake shawara dass gabana yafadi inbai sonafa
Dana shiga damuwa kuwa Dan Habeeb kawai xuciyata ke Kauna 
Zanyima Anas magana kan inason ya dinga tareki a hanyar gidansu Habeeb kuna gaisawa sannu a hankali kuna nuna ma Habeeb akwai wata a qasa sannan ke kuma ya xama dole kidaina masa murmushi koda yaimaki hakan xai sakasa tsaka mai wuya yaji gara yafada maki abunda ke damunsa kai tsaye
Wani sanyin dadi naji naratsa duk ilahirin jikina sai dai bansan a gd a lurafa Zainab kinsan su Yah Abba basa barina da saurayi
Haba Huwai kamar ba maceba kina ta bada mata
Nan suka gama caccakata muka rabu kan gobe xamu fara gwada Habeeb

Washe gari kau da wuri na shirya kamar yanda nasaba nafito ina xuwa anguwansu Habeeb na hango Anas xaune kan dandamalin wani gida yana latsa waya sadda kaina nayi amma kamar ance dago mukai ido hudu da Habeeb yasakar mun murmushi amma Dan cimma burina na matse na maida masa martani a xuciyata
Ina cikin tafiya naji sallamar Anas a gefena nadan waigo na dubesa naci gaba da tafiya shima yana bina a baya baifi taku biyar na isa gun Habeeb ba naja na tsaya na xubama Anas ido inasan jin meke tafe dashi
Anas ya gyara tsayuwa yace malama Huwailat kenan inata binki kina guduna bakisan abunda Allah ya tsaraba a tsakaninmuba
Dan satar kallon inda Habeeb yake nayi naga gaba daya hankalinsa akanmu yake Dan haka nasaki murmushi nace hakane
Malama Huwailat Tun randa nadora idanuna akanki naji sonki ya shiga xuciyata inata maki hannunka mai sanda kinki ganewa Dan haka nake gudun kada wani yaimun kafa naxo gareki da qoqon barana
Abaxata mukaji tari ya turnuke wani muduka muka waiga saiga Habeeb yanata tari damm gabana yafadi
Miyasaka Habeeb kwarewa haka banda amsar tambayana Dan haka na dubi Anas nace kai hakuri sainayi shawara nayi gaba abuna
Tun daga nesa su Hafsat ke mun dariya Dan haka ina isa na banka masu harara na shige get din islamiyyar
Sanin hali yasa suka biyoni suna guntse dariyansu wai wane iskanci ne haka xaku sakamun dariya daga xuwana
Bafa dake mukeba dafa Habeeb muke munsan saiya afka tashin hankali yaganki dawani
Hmm yan iska nan dai nabasu labarin abunda yafaru suka saka ihu dama munsan xa a rina Kawata kinci gari
To idan antashima Anas xai rakaki gida cikin dariya nace bansan iskanci sokuke Ku kashemunshi ne
Ohhh kaga farin shigan love fa to ai duk cikin kankaro maki sone kawai kedai muje xuwa
Haka kuwa akayi muka jero muka tafo nida Anas Yanaban labarin yanda yake matuqar Qaunar Zainab inata murmushi Dan sun birgeni dago idon daxan muka hada ido da Habeeb ya hade rai yayi kicin kicin abunsa kamar xai fashe na matse naikamar bangansaba muka rabasa muka wuce yabimu da kallo rai bace nace bakai taurin kaiba yanxu akafara axuciyana nayi wannan furucin  
Tun daga nan Sai Habeeb ya tsiri yimun Sallama idan xan wuce nikam na ansa naqara gaba inkuwa yaganni da Anas saiyaita baqin rai yana maxurai ko Anas yai masa sallama bai ansawa

Ran wata juma a narakosu Hafsat sunxo duba mama bata lafiya muna tafe muna labarin Habeeb yacika xurfin ciki kawai muka tsinkayi muryansa yana sallama ya dubi Zainab yace malama nadan ganki mana inba damuwa
Bansan yanda ake samun faduwar gabar baxataba sai a lokacin karfa Habeeb yace yanason Zainab cab Dana shiga Tara ni Huwailat
Inaji inagani Zainab ta ware da Wanda nake kauna dare da rana mukai gaba muka barsu baya suna tattaunawa
Hafsat tadubeni karda kidamu insha Allahu xamuji alkhairi kidaina damuwa yake naimata kawai amma banda bakin magana
Wasa wasa mukai nisa ba Zainab ba labarinta wani xaxxafan Hawaye naji a gurbin idanuna cikin dabara na goge kada Hafsat ta gani
Can saimukaji Zainab na kwadamana kira damm gabana ya buga tana xuwa ta rumgume Hafsat tace nayi sabon kamu qawayena tabbas wannan yafi Anas Dan haka nayi mijin baxatani
Yasalam tafaru ta qare kenan ni Huwailat narasa Wanda nakeso sai hawaye sharrr
Cikin tashin hankali suka dubeni lafiya Huwailat
Bakomi kawai dai
Kawai dai me ko kina mun jin xafin samun saurayi Dan unguwarkune Huwai
Gaba nayi kawai nabarsu agun sunata faman kwadamun kira nai kunnen uwar shegu dasu
Ko a class ban yarda na xauna waje guda dasuba Sam har aka tashi nakamo hanyar gida dai dai inda muka saba rabuwa Zainab taban takarda gashi Huwai kimaida masa tunda naga baki amince dashiba amma kifara karantawa nagode da nuna mun jin xafi Huwai
Nai tsaye da takarda a hannuna na dai lallaba natafi yau banma ga Habeeb ba nace taya daman xan gansa tunda ya isar da saqonsa ga wadda yake mawa nikuma awa yanxu
Ina shiga gida nafada dakina na rike takarda ina tunanin nabude ko karna bude

Tofa koyaya xata kaya kenan

Shin da gaske Habeeb Zainab take so

Miye a cikin takardai da Habeeb yaba Zainab

Anya kuwa Huwailat xata iya karanta takardai

Duk kubiyo Haupha danjin amsarku
Nagode

DA AURENAWhere stories live. Discover now