DA AURENA page 36__37

703 41 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452

Page 36 37

Allah kai kadai zaka iya kawomin dauki a duk inda nasamu kaina ya Allah kasa na mutu kona huta da bakar rayuwar danakeyi ta gararanba.

,,Pretty mizan gani hakan .

Wane marai imani da tausai yayi maki hakan.

Tabbas bazan kyale kowayeba anzo gun dazan fito na fito da duk ubanda yaja da ke .

Kuka ya kwacemun mai tsuma zuciyar mai saurare.

Uncle kowa ya koreni duk inda naje yau banda wajen da zan zauna .

Insha Allahu pretty zaki samu gunda zaki zauna indai ina raye zan kaiki gun mahaifita yanzu kuwa tana Aure a garin sokoto ne.

Sosai naji sanyi a raina hakaini gun mai gyara aka gyaramun kafa da hannuna.
Muka biya gidan abinci yasaimun amma nagaza ci ko ruwa bai haduwa ta dadi a bakina .

Sai danaga yadamu kwarai sannan na dan tsakuri abincin nace masa mutafi dan wallahi na tsani garin gaba daya sonake nabarsa barina har Abadan.

Nan yabarni yaje gida yadauko kayansa muka nufi tasha cikin tsakiyar rana.

Mundan jima sannan motarmu ta tashi ga zazzabi dake dagargazar jikina tun ina daurewa har uncle yafahimta.
Janyoni jikinsa yai duk da akwai mutane a motar yaci gaba da min sannu a kai akai .

Da kyal  barci ya shareni a jikin uncle Wanda zafin jikina yaba nasa zafi sosai.

Jiyake da yana da hali ko dama ba abunda zai hana ya maida ciwon jikinsa.

Yusuf tunda motar ta daga gabansa ke faduwa sosai dan yasan halin mahaifiyarsa idan taso mutum zaiji dadi idan kuwa taki mutum yabani.

Fatanshi ta amshi pretty da hannu biyu idanta koresu tabbas saiyafi pretty  shiga matsala.

Kamanta maganar aurenka da maryam ne ???

Wata zuciyar ta sanai dashi .

Zufa ta yanko masa tabbas ko mama ta hanshi Pretty maryam zatasa ta koreta saboda gida daya suke maryam diyar mijin mamace.
Allah gatan bawansa.

Sai gab magrib muka isa Wanda nayi barci harnaji ba dadi sosai.

Keke napep muka hau daga tasha zuwa gidansu uncle.

Kofar wani babban gida muka tsaya mai kyau dan yafi gidajenmu kyau da fasali.

,,Fito pretty munzo.

Bansan munzoba na fada duniyar tunani.

Kamar wadda kwai yafashemawa haka nake takawa har muka isa get din gidan yabudemin muka shige .

,,, kai wanake gani kamar Yusufu,
inji wani wanda ko tantama banyi mai gadin gidanne.

Cikin dariya suka gaisa da uncle nima nagaidasa muka durfafi cikin katon gidan.

Wani hadadden floor muka shiga Wanda wani matsiyacin sanyi da kamshi keta reto cikinsa . abunka ga mai ciwo dan da nan nafara kyarma .

,, Sannu pretty zauna nakira maman.

Yabi wata kofa ya shige wani daki.

Bai jimaba yafito wata mata na biye dashi daka ganta kasan mahaifiyarsace .

Cikin sauri na sauko kasa na gaidata.

Sosai naga tana kallona sannan ta dubi uncle ,,ina kasamo wannan yarinyai kuma kaida baka rabo da kwashe kwashen tsiya.

Dan kwantawa yai saman kafarta ,,mama ina Abokina danake fada maki ina zaune a gidansu a school ?
Tace Naganesa ince dai lafiya ?

Yace ,, kanwarsace jiya sunje bikin kawunsu duka gidan sukai hadari ita kadai ta rayu gashi ba nan danginsu sukeba suna Sudan can zasu suga danginsu abun yafaru.

Cikin fuskan tausai Mama tace Allah sarki sannu yarinya Allah yajikansu .

Kayi kyan kai daka kawota nan ai dan suma sun maka halacci ai .

Bakomi saita zauna anan har agano danginta.

Yasunan diyar tawa.

Huwailat amma gidansu pretty ake kiranta.

Dariya tadanyi aitaci sunanta zonan diyata .

Cikin kukan nakoma marainiyar karfi da yaji na matsa gunta ta rumgumeni nasaki kuka sosai .


To jama a yazaman zekama kenan🤷🏻‍♀

Kubiyo Haupha

DA AURENAWhere stories live. Discover now