DA AURENA page 83__84

704 37 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452


*Gaisuwa gareki my mom fatan alkhairi gareki dasu Badariya kannenah* 🤝🏻👏🏻

Page 83 84



Sosai ya shaketa Wanda idanunta suka firfito tamkar zata sheka lahira .

Gardi daya kula Amadu zai kisan kai a shagonsa yaita maza ya bangajesa .

Cikin dacin rai Amadu ya bude baki   ,,wallahi bazan yardaba Hafsat kije gidanku . . . .

Gardi yai wuf ya dade masa baki .,, baka da hankaline 🤷🏻‍♂ kamanta cewa duk randa ka saki Hafsat saika haukace ne ?
To wallahi a kul dinka kakiyayi abunda zai faru gareka bamai kyau bane .

Kuka Amadu yasaka hada majina wai Abokinsa da matarsa 😭
Shikam dama gawarsu ya gani da wannan mugun ganin ?

Hafsat ta saka kayanta ta sungumi 'yarda har yau bata San sunantaba bayanta ta ruga gida .

Amadu ya dubi Gardi ,,yanzu abunda kaimun ka kyauta kenan ?
,,kada ka manta nidakai tare mukai karatun almajirci amma ka runtse ido kaimun wannan ha'incin ?
Allah zai sakamun bazan taba yafemaba danka muzanta Abokantaka kasani danasanin Aminta da kai .

Sosai Amadu ke kuka jiyake yafi kowa damuwa da matsala a wannan bakar rayuwar .

Inama baikai tsawon raiba 😰

Gardi yai gyaran murya ,,amma yau na tabbatar da cewa wanzami baisan jarfa .
Ka manta wacece Hafsat ko ince ya take da matarka Huwailat ?

To kusancinsu yafi kusancina da kai ,amma saboda kai shegen kankane sai da kasan yanda kai ka dinke da Hafsat .

Da yake a cikin 'yan awakin kamafi bunsuru iskanci gaba da gaba kadinga nunama Huwailat yanda kake da Aminiyarta Hafsat .
Da kaso a tabbatar da kafi bunsuru iya bunsurincin ba sakin baiwar Allah kaiba bayan ka rabata da kowa nata kasata ta fada yawon duniya .
Hakan baimaba sai da ka tatse duk wata dukiya kadara ta mahaifinta sannan kai masu wulakanci son ranka .

,,Dan haka Amadu bazan baka hakuriba danka iskeni da matarka kai matan mutane nawa ka taushe 🤷🏻‍♂
Shawarata daya gareka ka koma kafara Neman hanyar da zaka tunkari bala'in da zai tunkaroka dan kadauki hakkin baiwar Allah da yawa .

Yasa rigarsa ya shige gidansa yabar Amadu zaune tamkar dutse .





Kuka sosai ya kwacema Amadu tabbas komi Gardi yafada gaskiyane yayi abubuwa da dama amma ai ya jima da gane kurensa ,yanada tabbacin idan yaga Huwailat zai maidata dakinta dan saki biyu yai mata akwai igiyarsa daya kanta yanzu haka .







😱Ruwa kake Amadu tsundum ycn😂






Cikin katuwar nadama ya dawo gidan kuka yaki tsaya masa ya iske inna nata bala'in tagaji da cida katuwar banza tamaji da yaronta da shegiyar diyarsa da tanada tabbacin Sheri akai masa kilama da hadin bakin Hafsat ciki .

Cikin nadama ya rungume inna ya fayyace mata duk abunda ya aikatama Huwailat tun daga farko har karshe .

Kuka ta saka itama ,,,dole bala'i yaita bibiyarka yaro amma bakai halin Babankaba ,

DA AURENAWhere stories live. Discover now