DA AURENA page 14

808 42 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452

Page 14






Cikin hanxari Uncle ya afko dakin Dan ganin meke faruwa

Hafsat da Amadu da rudewa tasa suka kasa sakin junansu ballema su nemi kaya su saka yagani Hafsat ta duqa shikuma yana riqe da kugunta sun xubama Huwailat idanu a firgice tsaki yaja ya wucesu ya dauko ruwa ya xuba mata sai dai me jini yaga yana yawo kasa cikin tashin hankali ya shiga girgixata Huwailat Huwailat pls kitashi bakin ciki baxai xama ajalinkiba Dan Allah kitashi inagunfa dubeni kigani nine Uncle gani kiganni

Iyakar rudewa yayita Wanda hakan yasa yafara fita hankalinsa

Cikin qaraji ya nuna su Wallahi idan wani Abu yasameta saina dai daita rayuwarki banxa qaxama kiyi gaggawan barin gidannan kafin nai maki tsinennan duka wallahi

Cikin rawai jiki da kukan nadama tafara saka kayanta shima ogah yanemi wandonsa yasaka da Riga yasunkuya xai dauki Huwailat cikin bacin rai Yusuf yace yaya baxaka tabataba da najasa a jikinka kai hakuri

Cikin borin kunya yace wasa nake dakaine Yusuf da xaka dakatar dani Dan xan taba Huwailat
Taimakonta xanyi Dan tana gab da rasa rayuwarta bakaga yanda jini ke xuba bane yasabata yai waje da ita yana kiran Makwabcinsa Musa dakeda mota

Zaunewa yai agun yacigaba da wani shegen kuka yagaji yagaji yakamata yai wani Abu baxai sakenda Yarinya xata mutu da bakin ciki ba bayan shima yana da damarsa kanta

Tofa nace wace damace Yusuf 🤔

Sanin kuka ba abunda xaimasa yafice ya nufi gidansu inna na ganinsa yafara sallallami kai Yusuf miyafarune ina Huwailatu take kaimun magana dan uwaka

Wasu Hawayen suka sake xubo masa sosai ya sadda kansa kasa  tayaya xai fada mata abunda danta kwaya daya ke aikatama yar mutane bayan yasan inna da son kanta indai lamarin daya shafi Amadu ne shikansa ba qaramin banbanci take gwada masaba akansa
Maganafa nakema kai shiru nace meke faruwane
Ayam yafado dakin Huwailat cefa suna dawowa daga ta iskeni da kawaita tana jiranta shine ta yanke jiki ta fadi yanxu haka daga Asibiti nake wai tayi barin cikinta

Wani uban salati Inna tajawo yanxu saboda tsabar kishi ta xubarma da ciki amma harka iya kaita Asibiti koda naji Dan uwanka yadawo cikin bacin rai Ashe Huwailat batada wayau nake mata kallon mai wayau tobaxai yiyuba tun wuri aima tubkar hanci baxan lamunci sakarcin banxabani
Cikin mamaki yabi Dan uwansa da kallo amma yaqi barima su hada ido ya girgixa kai lallai Yaya baida Imani amma akwai Allah

Ahankali nafara bude idanuwana da sukaimun nauyi naxubama qarin ruwan dake shiga jikina ido
Ahankali nafara tunano abunda yafaru daxun kamar magiji haka abubuwan sukaita dawomin a idanuna
Hawaye suka xubomin bansan wane laifi na aikataba da Amadu yaxamo Miji gareni haka bansan abunda naima Hafsat ba taimun wannan cin Amanarba sosai nakeson yin kukan amma hakan yagagara saima wani uban ciwon ciki daya turnikeni jinai kamar ana daddauremin yan hanjina
Cikin sauri yashigo dakin danake kwance sannu Matar Allah yabaki lafiya Dan Allah kimanta komi kiyita lafiyarki Dan tanada amfani ga mutane da dama cikinsu hadani

Amadu kuwa tunda yabarni Asibiti yaje ya tsara innarsu saiya wuce gidanmu a can kuma yafada masu nasha maganin xubda ciki Dan bansansa nayi nayi yasakeni ya qiya Dan haka nasha maganin xubda ciki yanxu haka ina asibiti anamun Karin jini

Cikin fada Mama tace Allah ya kyauta  kagaya mata ta kyauta tayi abunda ake son kowane Dan kirki tayi amma muddin ta kaso aurenta badai nan gidanba wallahi kama fada mata

Baba yace kema kebata bakinki Aida baka kaita Asibitinba da kabar yar Banxa ta mace  kowa ya huta

Haka yafito xuciyarsa fes yanufi gidansu Hafsat amma taqi fitowa yaso ta fito yabata shawaran ta rabu da Huwailat dansuci gaba da alaqarsu cikin kwanciyar hankali

Asibiti


Matar kinsan kowane bawa da qaddaransa shin baxaki dauki Aurenki matsayin qaddaraba
Shifa Aure nashajin anacewa Dan hakurine toke baxakiyi hakurinba
Kuka baimaki magani da yanayi da ba axo nanba
Wallahi kukanki xafi yakemun a xuciya bansamun natsuwa innaganki a damuwa amma kebaki damuda nai farincikiba kullum a damuwa kike

Akanki naqi Neman Aiki Dan nasan nesa dake xan hakan kuma xai jefaki a wata damuwar pls kimun alqawarin mantawa da komi
Cikin kuka nafara  magana
Uncle kasan yanda natsani maxinaci kuwa
Kasan yanda natsani cin Amana kuwa
Kasan yanda natsani a ha inceni kuwa
Tabbas abunnan baxai taba wucewaba guna sai dai kai hakuri

Karma ya wuce yar sarakan kishin duk duniya cewan Innarsu Amadu dake shigowa dakin

Yarinya kindaura karenki rana kuwa indai kikace kishi xaki nuna Dan Aure xansama ya qara inyaso yanxu ki kashe kanki karewan Dan cikinki

Banda kuka ba abunda nake tagama masifarta ta koma gida
Saiga Baba yashigo rai Bace ya nuna ni da yatsa
Wallahi Huwailatu idan kika kashe Aurenki badai gidanaba baxan iya xama dakeba marai jin magana yajuya fuu yabar dakin

Ni Huwailat yaya xanyi kenan

Kubiyoni Haupha danjin Amsar

Ina matuqar godiya gareku mutanen Da Aurenah Fans Dan kunnunamin kauna sosai akan wannan book nawa Allah yabar tare Ameen 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻

07081095452

Nagode

DA AURENAWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu