DA AURENA page 77__78

728 32 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452


Page  77 78

A gaggauce suka gama kimtsawa suka nufi motar major da nufin yau zasu isa Samaru komin dare .

Sai dai Captain ya tsaidasu da labarin yazo da wata rikitattar maganar bacewar princess dinsa dole major ya dakata dan koshine wa bazai iya tafiya yabar Captain a halinda yake cikiba dole suje gidansu yarinyai aji dalilin bacewar tata sace ta akai koko ita ta gudu da kanta ?

Mustapha ya fara tsinema yarinyai a zuciyarsa ba kakkautawa danta zama katangar hanasu zuwa gida yau suji gaskiyar lamarin Huwailat .
Ga burinsa na ganin yai ramuwai gayya gun Amadu da shegiyar tsohuwar nan da yaso zubdama hakora duka randa yatafo .

Major ya karanci rashin jin dadin mustapha tsab daga fuskaisa amma dole hakuri yabashi dan bazai iya share captain a wannan yanayinba .

Sanin koyace yasaka mustapha a case din bawani maida hankali zaiba ya kira su musa ya dorasu kan case din yaja Captain Ahmed suka koma gidansa yana kwantar masa da hankali dan yagane ba karamin so yakema yarinyaiba .shifa yanzu yana matukar tausan duk Wanda yasamu hatsari a soyayyaisa dan yasamu ko yacema yana ciki baiji da dadiba .sai dai shi tashi kaddarai sanadin wani dan iskan kauyene ya sameta dan haka kozai ragama kowa banda Amadu ,

Nace Amadu kana wuta suna binka da fetur😂








Sosai suka saba da zaman dajin duk da yawan mafarkin yaran nasu da suke kwanan nan yayi yawa Wanda har takai basu da wani labari saina abunda suka gani a mafarkin nasu.

Maharbi daya jima yana dan dube dubensa ya dubi Baba da fara'a tabbas na hango nasara na hango tashin hankali amma kuma karshe kwanciyar hankali zai wadata ga zuri'arka Alh.

Sannan kun kusa haduwa da yaronka sai dai naga bakar zuciya tare dashi wadda saikun sha wahala kafin ya manta abunda kukaima sa da yar'uwarsa .

Sannan naga wani dan uwanka shima yana shirin daukar fansar duk Wanda ya tabaka ciki hada mai dakinka dan yayi bincike yagane tayima asiri ta rabaka dasu ta mantar dakai kasarka iyayenka harma da mahaifiyarka abun yakona masa rai kwarai da gaske .
Fatana naga yaima 'yar wajenka kiranye idan ta isa akan lokaci to komi zai zama dai dai dan zai sassauta matakin dayai niyyar dauka fatana taje cikin lokaci sannan a yanayi mai dadin gani .

Tunda yafara magana mama keta kuka ,, tabbas na cancanci kowane hukunci daga danginka dan nazama mai son kanta da yawa na rabaka da danjinka tsawon shekaru masu yawa bantaba  jin na aikata ba dai dai ba dan burina narayu dakai da yaranmu kada kaje su kwace mana kai ko kace zaka koma can da zama .
Yau gashi an wayi gari nida nazabi muzauna cikin dangina zaman bai amfaneni da komiba dan ba Wanda yake taimakonmu kojin tausanmu tunda mahaifina ya fadi ya mutu komi ya dakata tsaninmu dasu dan kawai munshiga tawayar rayuwa .

Cikin kuka Abba yace ,,nafiku laifi nida narufe ido na dinga aibanta yar uwata nafada mata munanan kalamai nacusa mata bakin ciki fiye da Wanda bata zataba nakasa gane itadin kanwatace da tashi gabana sannan itadin nine nake mata komi dan farin cikinta tabbas dole naga jarabawa kodan zunubin dana aikatama kanwata sai Allah ya tambayeni da hannuwana na daketa da kafafuwana nadinga halbinta yau gani banda kafafuwan tabbas na cancanci kowane kalan hukunci .

Garba ya goge hawayensa shima ya tabka nasa laifin dashi Amadu yaita hada baki sanda Kaka bai lafiya akaita zagin Huwailat dashi akai mata dukan tsiya shinema ya janyota ya watsota waje yai tafiyarsa. Yau gashi suma sunbar gidan cikin wahala da ciwo karshe suka zama daya da ita yanda bata mori zaman gidanba da kudin da aka saida gidan haka suma .

Nace haka daman abun Allah yake .🤩









Amadu yai turjiya kofar gida yana ta zare idanuwa shidai yanzu Allah ya jarabceshi da son Huwailat yafara tunanin fita nemanta yadakatane Yusuf yadawo yaji koyasan inda take dan inna tafada masa shine yabata kudi aranai da ta bar garin da tuni ya bi duniya nemanta .

Hafsat ta dubi zainab ta sadda kanta kasa kuka ya kwace mata sosai ta kasa magana .
Zainab tai dariyar manya tace ,,uwargida kuma Amarya a gidan Amadu kintare gaba kin tare baya komi dake ciki matar Amadu .


,,dan Allah zainab kiyi hakuri kitayani ba Huwailat hakuri tabbas naga iyakata .

Amadu dai na auresa kuma nasamesa nadan wani lokaci amma yanzu kashi yafini daraja gun Amadu duk wahalan da Huwai tasha gunsa nata nafilane kan wadda nakesha saboda Amadu bai iskanci gaban Huwai sai dai ya korata wani gun ance kazantar da baka ganiba tsabtace Zainab .
Ta share majina daketa zuba .
,,Toni Amadu gabana yake kawo mata yace na zauna na kalla dan nadau darasi wai nawa yazama tsohon yayi .

,,gabana yake shiga wanka da mace sannan nice Ke wanke masu kayansu ga Amadu yadaina cidani bai ban abinci bai ban kudi na siya komi ya dai na yanzu haka idan kinga nashiga dakin can to kirana yayi yazo da wata ne ko kuma bukatarsa ce ta motsa .




,,Ke kam anyi bakar makira bankadaddiyar banza da wofi . inji inna data shigo gidan taji abunda Hafsat din Ke fada .

,,wallahi niba banka daddiya bace sai dai inkece banka daddiyar tsohuwa , Hafsat ta maida mata .

Zainab saita samu waje ta zauna ta rike diyarta da kyau tai kallon fada 😂

,,banda kaddarama yarona na zamansa lafiya da matarsa mai lafiya kika shiga kika fita saida kika rabasu kika shigo kika hanasa zaman lafiya da rayuwa mai inganci.

Hafsat ta zaburo kamar zata cinyeta danya ,, naje na hanasan ai garani da uwarda batasan ta kwabi danta inyana aika aikaba shegiyar tsohuwa mai bakin kwadayi .


Inna ta kwalalo idanuwa waje 😳
Tambadewar taki harta kai kina zagina yar matsiyata ?
Uwadda ta haifenice Ke dabazan zagekiba 💁🏻

Sun fara kokowa kenan Adamu yashigo da wata mace da yarta sak fuskai Amadu.

Tsawa ya daka masu ,duk suka natsu .

Ya nunama matar Hafsat yace bata ita  kibarmun gida .

Hafsat ta anshi yarinya tanajiran taji abunda yafaru yace diyatace saiki kula da ita saura kidinga cutarta naci ubanki la'ada waje.




Ko sallama baiba yafado gidan Amadu ya taresa lafiya ?

,,Wallahi shagunanka duka sunkama da wuta ba'a samu komiba wutarma taki kasuwa .
Basu ankaraba Amadu ya yanke jiki yafadi sume.


Zainab tace ,,Alhamdulillahi.
Ta dubi Hafsat dake riqe da yarinya tace ,,wani haninma baiwane ba rabon kawata tai ronon shegiya .
Tashafa fuskai yarinyai tai gaba tabarsu suna Neman taimakon motar da zasu kaishi asibiti tace badai Motar Zainab ba ta budesu da kasa ta bar unguwar

Nace da kin taimaka zainab 😜



Toyaya abun zaikasance kenan 🤷🏻‍♀

Kubiyo ni Next page

DA AURENAWhere stories live. Discover now