DA AURENA page 51__52

752 43 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452


Page 51 52

Cikin tsananin damuwa ta shafi fuskai yarinyai dake rumgume a cinyarta. Hawaye suka zubo mata ,, ina cikin kewarki kawata , bansan inda kikeba Allah yasa kin fada hannu na gari Huwailat , inata zuwa gida bansamunki karshe nasamu labarin irin korai Karen da sukai maki , insha Allah hannu na gari zaki fada sannan dolene nima natayaki daukar fansa Huwailat ,takamar Amadu boka nikuma takamata malamai zansa aita maki addu'a da fatan karya asirin da yaima duk wani ahalinki saboda ina son naganki cikin rayuwar farin ciki kawata.

,,ya isa haka maman Huwailat kidaina kuka insha Allah komi zaizama normal .

Tun bayan tashinsu zainab zuwa abuja taji shiru shiru ba wayan Huwailat ba message ko chat na Huwailat saita shiga damuwa dan haka ta matsa ma Anas da take kira Abban Khady a time din yakawota samaru taga Huwailat tasan ba banzaba shirun dan tayi yawa.

Bayanda baibata hakuriba yace ta hakura saita haihu tazo tunda watanta ya tsaya na haihuwan amma kullum zainab cikin kuka take hakan yasa Anas shirya masu tafiyar gaggawa zuwa samarun.

Sai dai bata taki sa'ar zuwaba dan aranai kwanan Huwailat uku da barin garin abun takaici mutane kowa da kalan labarin da yake bata na rashin mutuncin da iyayenta sukai mata yake karshe suka wurgota tsakar titi cikin halin suma.

Sosai tayi kuka Wanda atake tace suje gidan Huwailat din tanason ganin Amadu
Sanin halinta na zafi Anas yaso hanata amma saita nuna zata iya tafiya a kafartama .
Kasancewar yanzu yagama fahimtar komi ke faruwa yasa ya dauketa dan yafahimci rashin imanin Amadu zai iya mata wani abun idanta fada masa mai zafi .ayanda yake ji da kudinsa kau wani kato ya nemi dukar masa mata ko marinta ba shakka zai maganinsa .

Suna zuwa kuwa suka iske dillaliya nata saka yara suna fitar mata da kayan Huwailat din Anas baigama parking ba Zainab tafito da sauri kamar bamai tsohon cikiba .
,,malama lafiya naga kina fitar da kayan nan ?

,,Lafiya lau dan siye nayi ba kyauta ko sata nayiba ,kasancewar dillaliyar kamar yar duniya take tawani tabe baki☹ inakan daukar kudina kin tsaidani ta sungumi lokar gado ta nufi motor da take zuba kayan.

Cikin bakin ciki ta shiga gidan Amadu da Hafsat nata dariya ga nama ga lemu sun baje ga kudi gefe ko shakka batayi kudin kayan dakin Huwailat ne.

Abuna farko data farayi daukar damin kudin ta jefa a jaka ta gyara tsayuwarta .
Hafsat tunda taga Zainab wuta ta dauke mata bata manta marin data shaba tasani sarai Zainab masifafface daman can gata da shegen karfi dan haka ta dafe kumatunta duka ta zaro idanuwa 😱 gudun marin bazata daga zainab.

Sosai zainab ta kare masu kallo ,, da kyau matsiyata yan iskan karshen zamani ,wato kin zama karuwai gaske idanda karamace to yanzu kin girma gaskiya mama bataji dadin haihuwaba Hafsat , sai dai kamar yanda kika bada gudummuwa wajen tarwatsewar rayuwar Huwailat to insha Allah itace zata baki gudunmuwa gun dai daita rayuwarki ,
Hafsat inamaki albishir da zuwan makaskanciyar rayuwa ,Hafsat ina maki fatan dauwama da Amadu dan nasan Amadu ba mutum bane a cikin dabbobima Amadu yana sahun Tumadu gayya,( tsinnaka mai fiffike) dan haka kijira sanda zai cijeki ya tashi yabarki kina Sosa zuciyarki.

Amadu dake zaune yanajin tamkar yatashi ya bugeta ta kallah
,,nadawo kanka butulu mai maida sharri ga alkhairi kana nufin ubankane yasai mata kayan dakin dazaka kamasu ka saida 🤷🏻‍♀

,,Wallahi Amadu na hangoka kana gararanba fiye da wadda kajefa Huwailat ,sannan wadannan kudin wlh sunzama haramiyarka zanje dasu in zubasu a kasuwa insha Allah dasu kadaima sai Huwailat ta tallafi mutanen kauyennan ammafa karka saka ran kanacikinsu ninan zan hanata taimakonka dan tanada zuciya mai kyau bakamar takaba.

Wani matsiyacin ciwon ciki da mara suka taso mata .
Cikin karfi ta kwalawa Abban khady kira .
Bai wata wata ba yafada gidan ya isketa duke ta rike ciki tana yarfa hannuwa .

Kamar wani zaki haka ya shako wuyan Amadu yadinga jibgarsa .
,,wallahi wani abu yasamu matata saina daureka harka manta ya duniya take.

Zainab da ciwo keta gaba tace ,,Abban khady inaga Hauhuwa zan .

Cikin sauri yasaki Amadu yanufeta amma dan bala' I saida Zainab ce Abban khady bazaka dau matakin abunda yaimunba😰
Waya yaima wani Abokinsa police yakwatanta mai gidan Amadu yace ,,kasa akoya masa hankali friend madam ya daka ga ciki yanzu haka ya jawo mata labour.

Banji meyafadaba nagadai ya dauki zainab yakai mota ya rufe kofar gidan yaja mota yakai zainab hospital.
Bata jimaba ta haifi Baby girl dinta Wanda hakan yasa ta kuka sosai ta tuno Huwailat koda yaushe burinta ,,ki haihu musha suna zainab inaga nizanma maki wankan jegon.

Kidaina kuka bani ita naimata huduba gasu mama can waje .
Tabashi yagama yadago sunanta *HUWAILAT* fatan kinyi farin ciki🤷🏻‍♂

Sosai taji dadin karai da Anas yaimata itama sosai taimasa godiya.

Randa zasu koma Abuja ta tambayi Anas ,,Abban Huwailat ina labarin Amadu ne☹

Dariya yadanyi shegen na kulle amma yau zance asakesa dan saura sati bikinsa da Hafsat.
,,Muje tare pls ,
Badamuwa saimu biya.

Haka kau akai Anas yabiya da zainab ta nunama Amadu 'yarta sunanta Huwailat kasani baka isa kabatar da Huwailat a doron kasaba Allah zai sakama kawata kajira karshenka Amadu.

Tundaga sannan zuwa samaru baidamu zainab ba saidai bata fasa addu'a ba akan Huwailat har sadaka take dan bayyanar Huwailat.

Maman Huwailat inaga mufara sawa a karya kurciyar da yaima Suleiman dan yanada zafi nayi bincike kansa baida kyau ko wajen aikinsa shakkarsa suke sannan akado da hankalin yayanta mustapha natabbata sukadai saisun saka Amadu a tagayyarai rayuwa.
,,gaskiyarka Abban Huwailat nagode da kulawanka.





*Adamawa*




Babban gidane mai tarihi Wanda duk dan asalin Adamawa yasan dazaman gidan *Malam Garba na Allah* Wanda duk wasu malamai da Adamawa ke takama dasu nan gidan sukai karatunsu har zuwa sanda Allah yaima malam Garba na Allah rasuwa sai yaransa sukaci gaba da bada fatawa a gidan Wanda mahaifin Huwailat kamar yanda kukaji abaya shine Autan gidan yabar Adamawa yabar gadonsu yaje kasuwanci gari gari kasa kasa harya je Samarun Zaria ya hadu da Alh mamuda yabashi auren Zuhra tundaga sannan baisake waiwayensuba.

Sai kwanakin baya da matashin yaro yazo masu a matsayin dan Abdullahi harma yakara masu bayanin halin da suke ciki da surikin zamani da suka hadu dashi .

Sosai ran Babban yaya yabaci ,,Ashe Auta harya manta daga wane gida yafito ?
,Ashe Auta yamanta muke maganin kanana da manyan hatsabiyai masu shirka ga Allah😡

,,To yaro ka kyauta amma kasani bazan  karya asirin iyayenkaba sainagano Diyata Huwailatu sannan zanbi takansu daman kowa yabar gida ai gida yabarsa.


*Sokoto*

Sosai uncle kemasu yawo da hankali duk sanda maryam tai yinkurin fadama Huwailat yanda suke da uncle saita fasa tanajiransa yabata dama.

Itama dai bangaren Huwailat hakane yahanata ta bayyanasa matsayin masoyinta .

Gawata barazana dake son dawowa a rayuwaita yanda Daddy yake yawan shishshige mata komi ita butsu butsu yakirata awaya yaji tanada damuwa abunfa yafara bata tsoro.

To maji dai magani ai.🤣

Nagode masoyanah

Takunce dai Haupha

DA AURENAWhere stories live. Discover now