DA AURENA page 41__42

770 45 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452

'''Ina matukar mika godiya gareku masoyana irin sosai dinnanfa da sosai dan gaskiya kuna birgeni kuna samun sonku yana kara sama sama a kololiyar zuciyata 🥰🥰🥰🥰🥰
Allah yabarni daku 👏🏻👏🏻👏🏻

'''


Page 41 42

Tsai tsaye mukayi cirko cirko kowa da abunda ranta yabata .

,,muje mana maryam fadan uncle kenan dake zaune cikin motar.

Hakan yasa na fahimci ita yake son ta shiga gaban motar ba niba dan haka nai bisimillah nafada gidan baya nace sis muje koh.

Tashige gidan gaba yaja mota muka bar gidan ammafa naji ba dadi a zuciyata dan niya kamata a matsayina na Budurwansa na shiga shine yaba kanwaisa wajena amma ba komi .

Sosai ya lura da sam bataji dadiba amma yazama dole yadinga yi yana sirkawa kada wata ran Angle ta kwabsa masa amma idan yana mata basaja bazata gane komiba  dan ya godema Allah da su duka basu da bin kwakwkwafin abu suna da yarda sosai kan duk maganarsa.

Satar kallon maryam yai yaga hankalinta nakan wayanta tana duba pic dinsu da sukai wani zuwa da yai .damar yai amfani ya gyara madubi saitin fuskai  Huwailat yasakar mata murmushi yakashe mata ido daya.
Cikin sa a itama idonta yana kansa .cikin salon kwarewa ya kashe mata ido daya ya dan lumshesa ya langabar da kansa alamai sorry dinnan.

Sosai taji dadi ta aminta bada wata niyya yasaka maryam gaban motar ba itama ta maida masa murmushin hankalinta ya kwanta ta gane ba da manufa yayiba.

Ajiyar zuciya ya saki . ,na kashe wannan matsalai ya furta a hankali .

,,Yayanmu amma itama yau zaka sai mata waya ko  ? Fadan maryam kenan .

Kincika rigima dole naba saini zan saimata waya duk gasu Mama nan?

Sunata labarinsu kasa kasa har muka  isa wani hadadden Shago wanda bantaba ganin kalaisaba tunda nake sai a cikin kasasuwa .

Mazewa nayi kada nabada kaina muka shige ciki sai dai banji dadin yanda Sis ta kama hannun Uncle ta rikeba suna tafiya .

Hakan yasa nikuma nabisu a baya .

Yasan halin Huwailat sosai da kawaici amma akwaita da kishin tsiya sosai da sosai amma zai kokari ya San yanda yai yasa ta rage kishin nan dan zaibasa ciwon kai anan gaba .

Nace ba ciwon zuciyaba uncle 😜

Muna shiga sis ta waigo ,,waike sis saikita abu kamar wata village girl . dariya nadanyi sis baki da damafa .

Munata zagayawa dasu sai dai hankalina sam bai jikina sis sai wani jan uncle take suna photo jinai tamkar nasa kuka . ganin zan bakaina ciwon kai a banza nace sis bara nadan dubo wasu kaya can nayi gaba abuna.

Ina cikin zagayawa nama kasa daukar komi na hango wani   agogo sak na yah Habeeb cikin sauri na karasa gun ido rufe na kaimasa cafka da niyyar daukowa .
Sai dai me hannun mutum naji na rike madadin agogon .

Cikin sauri nakai idanuwana gun hannuwan dan ganin da gaske hannun ne koko ?  , da gaske kuwa hannune na rike bansan sanda nakai idanuwana kan mamallakin hannunba .

Ya salam !

Yah Suleiman ne cikin kakinsa na soja ransa bace eyes dinsa dade da bakin gilas.

Cikin jin haushin tuna kalamansa nai fuska nai saurin sakin hannunsa sorry Sir ban ankara bane nai saurin bacewa agun na lafe wani lungu ina lekensa naga yai saurin cire gilas dinsa ya kalli wadanda ke bayansa banji miya fadaba nagadai sun Sara masa sun nufi kofar fita cikin sauri hakan yasa na kara lafewa dan ganin me zasuyi masa .

Can naga sun dawo sun kame sun fada masa wata magana sai naga yadan zabura yai saurin fita shima suka mara masa baya .

Ajiyan zuciya nasaki bazan taba barin Wanda yasan asalina ya ganeniba balle yaje gida yafa damasu yaganni nafiso sumanta dani kamar yanda zan manta dasu kwata kwata a rayuwa zan zauna anan na auri uncle nai rayuwata tare da ahalinsa shikenan .

Hawaye suka zubomin naji hannu ana sharemun na dago da sauri naga uncle ne da alamai damuwa a fuskansa . ,,kiyi hakuri mun saba hakan da itane koda yaushe nikadai gareta kamar yanda ita kadai gareni kanwata kisama zuciyarki hakuri nariga nakoya mata shakuwa danine dan inasan ta daukeni tamkar abokinta amininta yanda zan zama jigo na share mata duk wata damuwa afuwan my pretty ke kadai nake so da kauna banjin so ko kaunar wata bayanke wallahi idan naga mata mamaki nake dan ganinsu nake tamkar maza .

Maryam kuwa tunda suka gama daukar🤳🏻 ya samu ya jata gefe ,,bakisan wani abuba pretty bafa kaya taje zabowaba kuka taje tayi dan nasan ta tuna iyayenta dan yar gatace kowa naji da ita duk randa zata shopping Abbanta ke kaita da yayanta sosai take da gata nasan zata ga yau tazo babusu sannan bamai tayata zaben mun biyota mun buge da shan love ya kashe mata ido daya.

Cikin sauri maryam ta bata fuska baka kyautaba yah dasaika fadan jiya damuna chat dabazan kulaka muita love ba ai .tana magana tana tafiya Neman Huwailat .

Can ta hangota tana  hawaye tabbas gaskiya yah yafada abar tausai ce sis . ta koma ta kira shi ta gwada masa ita ,,kije kizabar mata duk abunda yakamata zanje nabata baki kinji my Angle.

Maryam ta wuce shinefa ya isketa tana kukan tuno gida datai.

Wallahi pretty bansan kalan sonda nake makiba yai mun yawaba sai naji duk sanda naganki tamkar na hadeki cikin cikina na ajeki bamai kara ganinki ki narke kibi jinin jikina .ya curo wani kyakykyawan zobe yasamata a yatsanta alkawarin aure nane wannan pretty muje sis  dinki tagama zabar maki kayan tunda kin gaza ke.




Cikin matukar bacin rai ya dubesu ,,kuka ce Baku gantaba musa ?

,,Yes sir

Aikin banza daga yau zuwa sati kutabbatar kun samo min kaf information kanta idanba hakaba zaku sani yaja karamin tsaki ya shige motarsa da mugun gudu yabar wajen

To waishin da gaske Suleiman ne kuwa 🤷🏻‍♀


Yaya Huwalat zataji  idanta gane Uncle love yake da maryam


Itakanta maryam din yazatayi ?

Kibiyoni danjin amsarku

Nagode

DA AURENAWhere stories live. Discover now