DA AURENA page 53__54

713 36 0
                                    

*♦♦DA AURE NAH♦♦*

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452

Gaskiya ina matukar godiya gareku masoyan book din *DA AURE NAH* Koda yaushe kara yawa kuke Allah yabar kauna ina sonku over over wlh



Jinjina ga group din *DA AURE NAH FAN'S* Yabonku addu'anku suna tasiri sosai kaina dan haka nake ta suburbudo maku typing ba dare ba rana ,



Page 53 54


*Gidansu Huwailat*

,_Alhaji lafiya naganka zugudim ba walwala ?

, ,Ke dai Bari Zahra,u yau ina cikin tashin hankali sosaima kuwa daga wannan bala'i sai wancan 🤷🏻‍♂

,nan nan fa agabanki yaron nan Amadu yazo yace na hada jarina nabashi zai zuba a sabon company da aka bude zamu samu riba sosai harkai Addugace ( kada) naje na tattara komi nawa hadasu cin bashi na hada kan kudaden naba yaronnan yatafi dasu shinefa yanzu yake fadamin wai anyima company fashi dan haka kudaden kowa ya salwanta,

Ya ilahi ,!

,, kai ammafa anyi azzalumai Alh. Yanzu shikenan munyi asara kenan ta dukiyarmu Alh.

,,tashin hankalina zahara'u na anshi kudin Alh Bawa dubu 90k kinsan kau baida mutunci akan kudinsa .

,,to Alh gobe kabari sai an kwana biyu da bikin Amadu kaimasa magana kaji yanda za'ai .

*Amadu*

Aranai cikin dare ya je gidan inna harta kwanta barci taji maganar Yusuf nacewa Brother lafiya kake tafe cikin dare bayan kaidin ango ne.

Cikin matsiyacin yake yace ,, akwai sauran abinci a gidannan kuwa ,?

,,Wane irin abinci kuma da tsakar dare kake nema Dannan?

Shafa keyars yai ,,duk yau dagani har ita Hafsat din bawanda yasami damar cin abincine Inna shine yanzu yunwa tasa nafito nema kuma duk sun tashi,

Kasantuwar inna mai shegen bin diddikin abu yasa tace ,,kai Yusuf bakai naga kamar ya aika kasiyo masa kaza da lemuba 🤔

Cikin sauri Amadu yace ,,ai muncinyeshi tun dazun yanzu wata yunwarce dai tamotsa.

Uncle ya tabe bakinsa yanufi dakinsa dan yana cikin chat da masoyansa Huwailat da maryam yakirasa ya bude masa gida.

Inna data saki baki 😩tace ,, anya kuwa. Dannan farawa da iyawa yarinya tafara aikenka da tsakar dare😳 tobazan lamintaba niban haifi raggon miji ba yauwa ,

Ganin zata tara masa jama' ar bikin yasa yace zan jira dakin Yusuf inna kar dare ya kara dan Allah.

Sosai taji zafin abun aranta amma xataima Hafsat kashedi karta sake tace zata wahal mata da Danda bazata lamunci wannan shegantakarba.

Ahankali ya shiga dakin Yusuf din Wanda ya bude da kamshin da dakin Huwailat kawai yasanshi yasashi lumshe ido ya fada kan katifar gefen uncle daketa chat abunshi .

Gashinsa yasa uncle canja akalai firan tasa.
,,kinsan Allah Angle Huwailat nada kokari asanina da ita kenan yanzu abun yaci uban Nada ☺

Huwailat . wace Huwailat din badai Huwailat dinaba Yusuf ina kaji labarinta ?

Cikin banzan kallonsa ya dubi Amadu ina maganane da Maryam Huwailat dakaji kuma itama yar cance yayar Maryam dince.but why kake min wannan tambayai brother koka fara Neman Huwailat dinne tun yanzu🤷🏻‍♂

,,Allah yasawake na nemi Huwailat yanzu hakama na gama tsara komi yanda zan rabu da iyayenta ta hanya mai sauki nagama tsiyatasu nasa sun wulakanta yarsu sun kori masifeffen yaron nan mustapha nasa an maida Babanta mai rariyar hannu yanzu basuda wani karfi ko mai karfi da konan gaba asirina ya tonu dazai dau masu fansa balle mataki kaina.

Ko kadan uncle baiji komiba kan makircin da Amadu xaima iyayen Huwailat dan sungama bashi haushi baitaba ganin iyayenda sukaima 'yarsu mace abunda sukaima Huwailat dinsaba dan haka yabasar da maganar .

Da kyal  inna tasamo masa kingin masa ( waina) ya koma gidan time din dare ya tsala sosai .

Yajima yana buga gidan kafintazo ta bude masa ta anshe  dan kwanon da tagani gunsa ta shige dakin bata jimaba ta fito da tabarma da filo ta watsamai wallahi bazaka kwanarmun agadoba kanata uban wariba tasama dakin sakata tai kwanciyarsa.

Sosai yaga daren tayi masa nisa fatansa gari ya waye yaje gun Abokinsa Gardi yabasa taimako kan lamarin Hafsat danta bala'in bashi ciwon kai daga zuwanta.

Itama tagama tsara komi itada kawarta Binta kan yanda zasu gano malaminsa susashi yazama su yakema aiki ba Amaduba.

Tunda Asuba Hafsat ta fito ta gama Sallah inda Allah ya taimaketa kenan taga Amadu kwance yasaki baki yanata Jan nasarin barci.

Takoma ta debo ruwanta cike da jug ta watsa masa.
,,Malam kobaka sallah ne kazama mace🤷🏻‍♀

Cikin firgita ya tashi yaganta tsaye ta rike kugu.
Duk iskancin mutum inyana sallah yasamu saukin wani abun .maza aje ai sallah Amadu ta nuna masa buta.

Shikam yabani dama Hafsat kurace da fatar akuya baisaniba😳

Shikam yagata Kansa.

Yana gamawa tabashi tsintsiya ,,maza ashare gidan uban yan dauda.
Baisan yanda akai bai iya musama yarinyaiba dole yana gama sallai yashare mata gidan da dakinta ya goge sannan ya dora ruwan tea danta fada masa itada koko sai gani daga nesa.

Amma yasan yana zuwa gun Abokinsa Gardi komi zai dai data yanzuma dan yayi wata 'yar tafiyane komi yajaguje masa.

Tofa yakenan zaman Amadu Da Hafsat🤷🏻‍♀

Miye matakin da inna zata dauka kar Danta yazama raggon miji🤷🏻‍♀

Zainab taci nasaran karya asirin Suleiman kuwa ?

Inyadawo wane mataki zai dauka kan Amadu da iyayen Huwailat🤷🏻‍♀
Shin Captain Ahmed kuwa zaisamu zuciyar Huwailat😂🤣

Yaushe mama zata cika burinta ne kan Huwailat🤷🏻‍♀

Da gaske Daddy zai iya fadamasu yanason Huwailat kuwa🤷🏻‍♀

Kudai biyoni Haupha danjin chakwakiyar🤣🤣💃🏻

DA AURENAWhere stories live. Discover now